KA YI KOYI DA BANGASKIYARSU | JONATHAN
Jonathan—“Babu Abin da Zai Iya Hana” Jehobah
Ka dauka cewa kana ganin wasu sojoji suna tsaye a kan tudu mai tsayi. Sojojin Filistiyawa da aka tura yin tsaro a wurin sun hango wani abin ban sha’awa. Sun ga mazan Isra’ilawa biyu suna tsaye a wani kwari. Sojojin sun yi dariya don suna ganin mazan ba za su iya kawo musu hari ba. Filistiyawa sun dade suna cin zalin Isra’ilawa, kuma mutanen Isra’ila ba za su iya watsa bakin abubuwan da suke noma da su ba, sai sun kai wajen Filistiyawan su yi musu. Hakan ya nuna cewa sojojin Isra’ila ba su da makaman yaki sosai. Kari ga haka, maza biyu ne kawai suka gani! Ba za su iya yaki da Filistiyawa ba ko da suna da makamai. Sai sojojin Filistiyawa suka ce musu: “Ku haura zuwa wajenmu, za mu koya muku hankali!”—1 Sama’ila 13:19-23; 14:11, 12.
Hakika, za a koya wa wasu hankali amma Isra’ilawan ne za su koya wa Filistiyawa hankali. Sai Isra’ilawan guda biyu suka fito daga cikin kwarin, kuma suka soma hawa zuwa tudun. Don tudun yana da santsi sosai, sai da suka yi rarrafe da hannayensu da kafafunsu don su haura da sauri zuwa inda Filistiyawan suke! (1 Sama’ila 14:13) Sai Filistiyawan suka ga cewa mutumin da yake gaba yana da makami kuma mai rike masa kayan yaki yana bin shi. Amma shin mutane biyun nan ne kawai za su je su yaki sojoji masu yawa? Mutumin yana da hankali kuwa?
Yana da hankali, shi mutum ne mai bangaskiya sosai. Sunansa Jonathan, kuma Kiristoci a yau za su koyi darussa sosai daga labarinsa. Ko da yake ba ma yaki da mutane, za mu koyi abubuwa da yawa daga yadda Jonathan ya kasance da karfin hali da aminci da kuma rashin son kai. Muna bukatar wadannan halayen idan muna so mu zama masu bangaskiya sosai.—Ishaya 2:4; Matiyu 26:51, 52.
Shi Jarumi Ne da kuma Mutum Mai Aminci ga Babansa
Ya kamata mu san tarihin Jonathan don mu fahimci dalilin da ya sa ya yi karfin zuciya ya je ya sami sojojin Filistiyawa. Jonathan ne dan farin Shawulu, sarki na farko a Isra’ila. Watakila Jonathan ya kai shekara 20 ko fiye da hakan a lokacin da aka nada Shawulu sarki. Kamar dai Jonathan na da dangantaka ta kud da kud da mahaifinsa. Sau da yawa Shawulu yakan gaya wa dansa abin da yake damunsa. A lokacin, Jonathan ya san cewa mahaifinsa mutum ne mai tsayi, mai kyaun siffa, kuma jarumi ne. Amma halayen mahaifinsa da ya fi burge shi su ne saukin kai da kuma bangaskiyarsa. Jonathan ya san cewa wadannan halayen ne suka sa Jehobah ya zabi Shawulu ya zama sarki. Annabi Sama’ila ma ya ce babu wani a cikin kasar kamar Shawulu!—1 Sama’ila 9:1, 2, 21; 10:20-24; 20:2.
Babu shakka, Jonathan ya ji dadin gatan da aka ba shi na fita yaki tare da sojojin mahaifinsa don su yaki abokan gābansu. Wadannan yake-yaken ba irin wadanda ake yi a yau ba ne. A lokacin, Jehobah ya zabi Isra’ilawa su zama mutanensa, kuma mutanen da ba sa bauta wa Allah suna yawan kawo musu hari. Filistiyawa da suke bauta ma allolin karya kamar Dagon suna yawan zaluntar mutanen Jehobah ko kuma sun yi ta kokari su halaka su gaba daya.
Saboda haka, a wurin bayin Allah masu aminci kamar Jonathan, yin yaki hidima ce ga Jehobah. Kuma Jehobah ya taimaka wa Jonathan ya yi nasara sosai. Ba da dadewa ba bayan Shawulu ya zama sarki, sai ya nada dansa Jonathan shugaban sojoji guda 1,000. Jonathan ya ja-gorance su wajen yin yaki da sojojin Filistiyawa a Geba. Ko da yake sojojin Jonathan ba su da makamai sosai, Jehobah ya taimaka masa ya ci yakin. Hakan ya sa Filistiyawa suka karo makamai da sojoji da yawa don su yaki Isra’ilawa. Sojojin Shawulu da yawa sun tsorata kuma wasu suka gudu suka boye, wasu kuma suka goyi bayan Filistiyawa! Amma Jonathan ya ci gaba da kasancewa da karfin zuciya.—1 Sama’ila 13:2-7; 14:21.
A ranar da muka ambata dazu, Jonathan ya fita da mai rike masa kayan yaki ba tare da sanin kowa ba. Yayin da suka yi kusa da sansanin Filistiyawa da ke Mikmash, Jonathan ya gaya wa mai rike masa kayan yaki abin da yake so ya yi. Za su fito fili don sojojin Filistiyawa su gan su. Idan Filistiyawa suka ce musu su zo su yi fada, hakan zai nuna cewa Jehobah zai taimaka wa bayinsa. Sai mai rike masa kayan yaki ya amince watakila don abin da Jonathan ya gaya masa cewa: “Babu abin da zai iya hana Yahweh kawo nasara, ko ta wurin mutane masu yawa, ko ta wurin mutane kadan.” (1 Samuel 14:6-10) Mene ne yake nufi?
Hakika, Jonathan ya san abin da Allahnsa zai iya yi. Ya san cewa a dā, Jehobah ya taimaka wa mutanensa su yi nasara a kan abokan gābansu da suka fi su yawa sosai. Akwai lokutan da Jehobah ya yi amfani da mutum daya tak don ya sa mutanensa su yi nasara. (Alkalai 3:31; 4:1-23; 16:23-30) Saboda haka, Jonathan ya san cewa ba yawan sojoji ko makamai ko kuma karfin bayin Allah ne yake sa su yi nasara ba, amma bangaskiyarsu ce. Jonathan mai bangaskiya ne sosai, shi ya sa ya roki Jehobah ya nuna masa ko shi da mai rike masa kayan yaki su je su tinkari Filistiyawan. Ya yi hakan ta wajen zaban alamar da za ta nuna cewa Jehobah yana goyon bayansu. Jonathan ya kai wa sojojin Filistiyawa hari da karfin hali sa’ad da ya sami amincewar Jehobah.
Abubuwa biyu ne suka sa Jonathan ya kasance da bangaskiya. Na farko, yana daraja Jehobah sosai don abubuwan ban al’ajabi da yake yi. Ya san cewa Allah Madaukaki ba ya bukatar taimakon mutane domin ya cim ma nufinsa. Kuma Jehobah yana taimakon mutanen da suke bauta masa. (2 Tarihi 16:9) Na biyu, Jonathan ya so ya tabbata cewa Jehobah goyon bayansu kafin ya dauki mataki. A yau ba ma neman alamu daga wurin Allah domin mu san ko zai amince da abin da muke so mu yi. Amma, muna da Kalmar Allah wadda take dauke da dukan abubuwan da muke bukata domin mu san nufin Allah. (2 Timoti 3:16, 17) Ya kamata mu rika karanta Littafi Mai Tsarki sosai kafin mu tsai da shawarwari masu muhimmanci. Idan muka yi haka, kamar Jonathan, muna nuna cewa mun fi damuwa da nufin Allah ba namu ba.
Sai maza biyun suka soma haura tudun da sauri zuwa wurin sojojin Filistiyawa. Da Filistiyawan suka ga cewa ana son a kawo musu hari, sai suka tura sojoji don su yaki Jonathan da mai rike masa kayan yaki. Da yake Filistiyawan suna da sojoji da yawa kuma suna saman tudu, zai yi musu sauki sosai su kashe wadanda suke so su kawo musu hari. Amma Jonathan ya dinga sarin sojojin daya bayan daya, suna fadiwa a kasa, mai rike masa kayan yaki kuma yana bin bayansa yana kashe su. Ba da dadewa ba, maza biyun suka kashe sojojin abokan gābansu guda 20! Ban da haka, akwai abin da Jehobah ya kara yin. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Sai tsoro ya kama dukan sojojin Filistiyawa, da wadanda suke a cikin sansanin yaki, da wadanda suke waje, har ma da wadanda suke a fili, da kuma wadanda suke kai hari. Dukansu suka ji tsoro sosai har suka rikice. Aka yi rawar kasa. Allah ne kuwa ya kawo wannan rikicewar.”—1 Sama’ila 14:15.
Tun daga nesa, Shawulu da sojojinsa suka hango yadda Filistiyawa suka rikice suna gudu ta ko’ina, kuma suna ta saran juna da takuba! (1 Sama’ila 14:16, 20) Sai Isra’ilawa suka yi karfin zuciya suka soma kai wa Filistiyawa hari, watakila sun yi amfani da makaman Filistiyawan da suka mutu ne. Jehobah ya sa mutanensa suka yi nasara a wannan ranar. Kuma har yanzu Jehobah bai canja ba. Idan muka ba da gaskiya gare shi yadda Jonathan da mai rike masa kayan yaki suka yi, ba za mu yi da-na-sani don zabin da muka yi ba.—Malakai 3:6; Romawa 10:11.
“Da Taimakon Allah Ne Ya Yi Shi”
A wurin Jonathan, Jehobah ne ya sa suka yi nasara, amma a wurin Shawulu ba haka yake ba. Shawulu ya riga ya yi kurakurai sosai. Ya yi wa annabi Sama’ila da Jehobah ya nada rashin biyayya sa’ad da ya mika hadayar da Lawiyawa ne kadai ya kamata su mika. Sa’ad da Sama’ila ya isa wurin, ya gaya wa Shawulu cewa sarautarsa ba za ta dawwama ba domin rashin biyayyarsa. Ban da haka, sa’ad da Shawulu ya tura sojojinsa yin yaki, sai ya yi rantsuwar da ba a umurce shi ba cewa: “La’ananne ne mutumin da ya ci abinci kafin faduwar rana, tun ban yi ramuwa a kan abokan gābana ba.”—1 Sama’ila 13:10-14; 14:24.
Kalaman Shawulu sun nuna cewa halinsa ya soma canjawa. Mutumin da a dā mai saukin kai ne da mai son ibada ya soma zama mai girman kai. Ballantana ma, Jehobah bai umurce shi ya saka ma wadannan sojojin irin wannan takunkumin ba. Kari ga haka, furucin nan da Shawulu ya yi cewa ‘tun ban yi ramuwa a kan abokan gābana ba’ ya nuna cewa Shawulu yana ganin yakin nasa ne. Kamar dai ya manta cewa abin da ya fi muhimmanci shi ne yadda za a daukaka Jehobah, ba yadda zai yi nasara kuma a girmama shi ba.
Jonathan bai san cewa mahaifinsa ya yi rantsuwa ba. Da ya dawo daga yaki a gajiye, sai ya sa sandan da ke hannunsa ya taba zuma ya sa a bakinsa kuma nan da nan ya ji ya farfado. Sai wani cikin sojojinsa suka gaya masa cewa mahaifinsa ya hana cin abinci. Jonathan ya ce: “Babana ya kawo damuwa a kasar. Ai, kai ma ka ga yadda dan zuman da na taba ya sa na sami karfi. Da yaya zai kasance ke nan da a ce an bar sojojin suka ci abincin da suka kwace daga abokan gābansu? Ai, da gawawwakin Filistiyawan da aka kashe sun fi haka!” (1 Sama’ila 14:25-30) Jonathan ya fadi gaskiya, ko da yake yana daraja mahaifinsa, ba duk abin da ya fada ba ne yake amincewa da shi ba. Hakan ya sa mutane sun daraja shi sosai.
Har ila, Shawulu bai fahimci cewa umurninsa bai dace ba sa’ad da ya ji cewa Jonathan ya karya dokarsa. Maimakon haka, yana ganin ya kamata a kashe dansa! Jonathan bai yi mūsu ko ya roka a ji tausayinsa ba. Ya ce: “Ga ni, a shirye nake in mutu.” Amma, Isra’ilawan suka ce: ‘Don me Jonathan zai mutu bayan da ta dalilinsa ne muka ci nasara? Ko kadan ba zai yiwu ba! Mun rantse da Sunan Yahweh mai rai, ba wanda zai taba gashin kansa guda. Gama abin da ya yi yau, da taimakon Allah ne ya yi shi.’ Mene ne sakamakon? Shawulu ya saurari abin da suka ce. Littafi Mai Tsarki ya ce: ‘Domin haka sojojin suka fanshi Jonathan daga mutuwa.’—1 Sama’ila 14:43-45.
Jonathan ya yi suna mai kyau don karfin halinsa da kwazonsa da kuma halinsa na sadaukarwa. Shi ya sa mutane suka taimaka masa sa’ad da ya shiga cikin matsala. Ya kamata mu yi tunanin irin sunan da muke yi a kowace rana. Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa suna mai kyau yana da daraja sosai. (Mai-Wa’azi 7:1) Kamar Jonathan, idan muka yi suna mai kyau a gaban Jehobah, sunanmu zai zama kamar dukiya mai daraja sosai.
Munanan Halaye Sun Dada Bayyana
Duk da kurakuran da Shawulu ya yi, Jonathan ya ci gaba da goyon bayansa. Ya yi bakin ciki sosai sa’ad da ya ga cewa mahaifinsa ya ci gaba da rashin biyayya da girman kai. Halin mahaifinsa ya canja sosai, kuma ba abin da Jonathan zai iya yi game da hakan.
Shawulu ya nuna girman kansa a lokacin da Jehobah ya gaya masa ya je ya yaki Amalekawa don mutanen mugaye ne sosai. Tun zamanin Musa, Jehobah ya annabta cewa zai halaka dukan al’ummar. (Fitowa 17:14) An gaya wa Shawulu ya halaka dukan dabbobin Amalekawa kuma ya kashe sarkinsu, Agag. Shawulu ya ci yakin da taimakon dansa Jonathan, wanda ya saba goyon bayan mahaifinsa a yaki. Amma da gangan Shawulu ya yi wa Jehobah rashin biyayya, ya ki kashe Agag kuma bai halaka dukiyoyi da dabbobin da suka kwaso ba. Annabi Sama’ila ya sanar wa Shawulu hukuncin Jehobah cewa: “Saboda ka ki jin maganar Yahweh shi ma ya ki ka da zaman sarki.”—1 Sama’ila 15:2, 3, 9, 10, 23.
Ba da dadewa ba, ruhun Jehobah ya bar Shawulu. Da yake Jehobah ya daina taimaka wa Shawulu, Shawulu ya canja gabaki daya, yakan yi fushi sosai a wasu lokuta, wani lokaci kuma yakan firgita sosai. Kamar dai mugun ruhu daga Allah ya shiga jikin Shawulu. (1 Sama’ila 16:14; 18:10-12) Hakika, wadannan abubuwan sun sa Jonathan bakin ciki sosai don mahaifinsa mai halin kirki, ya canja gabaki daya! Duk da haka, Jonathan ya ci gaba da kasancewa da aminci ga Jehobah. Ya yi iya kokarinsa don ya taimaka wa mahaifinsa, kuma yakan gaya masa gaskiya a wasu lokuta. Amma Jonathan ya ci gaba da tsoron Allahnsa da kuma Ubansa wanda ba ya canjawa, wato Jehobah.—1 Sama’ila 19:4, 5.
Shin ka taba ganin yadda wani da kake kauna ya canja daga mutumin kirki zuwa mugu? Watakila wani danginka ne. Hakan zai iya sa ka bakin ciki sosai. Misalin Jonathan ya tuna mana abin da wani marubucin Zabura ya rubuta cewa: “Ko da babana da mamata sun yashe ni, Yahweh zai lura da ni.” (Zabura 27:10) Jehobah ba ya barin mutanensa. Zai kula da kai sosai kuma ya zama Uban da babu kamarsa, ko da ’yan Adam ajizai sun yi watsi da kai.
Jonathan ya san cewa Jehobah yana so ya dauke sarauta daga Shawulu. Mene ne Jonathan ya yi? Shin ya soma tunanin irin sarki da zai zama ne? Ya sa rai cewa zai daidaita wasu abubuwan da mahaifinsa ya yi da ba su dace ba? Yana ganin zai kafa misali mai kyau a matsayin sarki mai aminci da biyayya? Ba mu san abin da yake zuciyarsa ba, amma mun san cewa bai zama sarki ba. Hakan yana nufin cewa Jehobah ya watsi da mutumin nan mai aminci ne? A’a, a maimakon haka, Jehobah ya ci gaba da amfani da Jonathan. Ya sa an rubuta labarinsa a matsayin daya daga cikin wadanda suka kulla abota mafi kyau a Littafi Mai Tsarki! Talifi na gaba game da Jonathan zai yi bayani a kan wannan abokantakar.