KA YI KOYI DA BANGASKIYARSU | AYUBA
“Ba Zan Daina Tsare Mutuncina Ba!”
Yana zaune a kasa, ga marurai sun cika jikinsa daga kai zuwa kafa. Ka yi tunanin yadda ya sunkuyar da kai, kafadarsa a yankwane, yana zaune shi kadai, ba shi da ma karfin da zai kori kudajen da ke binsa. Ban da haka, ya zauna cikin toka don ya nuna yana makoki, kuma ya dauki kaskon tukunyar lakar da ta fashe yana sosa jikinsa da shi. A dā, mutane suna daraja shi sosai amma yanzu suna kyamarsa! Abokansa da makwabtansa da danginsa sun yi watsi da shi. Mutane har ma da yara suna yi masa ba’a. Kari ga haka, yana tunanin cewa Allahnsa Jehobah ya juya masa baya, amma hakan ba gaskiya ba ne.—Ayuba 2:8; 19:18, 22.
Ayuba ne mutumin. Allah ya ce: “Babu wani mai kama da shi a duniya.” (Ayuba 1:8) Darurruwan shekaru bayan haka, Jehobah ya ce Ayuba yana cikin mutane masu adalci sosai da suka taba rayuwa.—Ezekiyel 14:14, 20.
Shin kana fuskantar matsaloli sosai a yau? Labarin Ayuba zai karfafa ka. Zai kuma taimaka maka ka fahimci wani halin da ya kamata kowane bawan Allah ya kasance da shi. Wannan halin shi ne aminci. ’Yan Adam za su nuna cewa suna da aminci idan suka dogara ga Allah kuma suka ci gaba da yin nufinsa ko a lokacin da suke fuskantar matsaloli. Bari mu kara koyan darasi daga Ayuba.
Abin da Ayuba Bai Sani Ba
Kamar dai bayan mutuwar Ayuba ne Musa ya rubuta labarin Ayuba. Allah ya sa Musa ya rubuta abubuwan da suka faru a duniya da suka shafi Ayuba da kuma wasu abubuwan da suka faru a sama.
Da aka soma labarin, an gaya mana cewa Ayuba yana jin dadin rayuwarsa. Shi mai arziki ne kuma sanannen mutum ne da ake darajawa a kasar Uz, da watakila take arewacin kasar Larabawa. Shi mai karimci ne sosai da ke taimaka wa talakawa da kuma kāre wadanda ba su da mai taimako. Ayuba da matarsa suna da yara goma. Abin da ya fi muhimmanci shi ne, Ayuba ba ya wasa da dangantakarsa da Jehobah. Ya yi kokari ya faranta ran Jehobah yadda danginsa Ibrahim da Ishaku da Yakubu da Yusufu suka yi. Ayuba ya bi sawun wadannan mutanen, ya yi hidimar firist a madadin iyalinsa ta wajen mika hadayu a kai a kai a madadin yaransa.—Ayuba 1:1-5; 31:16-22.
Sai mai ba da labarin ya canja daga labarin Ayuba zuwa abin da ya faru a sama. Ya ambata abin da ya faru a sama, kuma ya fadi abubuwan da Ayuba bai sani ba. Mala’iku masu aminci sun taru a gaban Allah, kuma Shaidan wanda dan tawaye ne, ya bi su. Jehobah ya san cewa Shaidan ya tsani Ayuba don amincinsa, kuma ya yi magana da Shaidan game da amincin Ayuba. Sai Shaidan ya amsa ya ce: “A’i, ba a banza ne Ayuba yake jin tsoron Allah ba! A’i, yana jin tsoronka gama kai ka kewaye shi da katanga, da shi, da gidansa, da dukan abin da yake da shi a kowane gefe.” Shaidan ya ki jinin mutane masu aminci. Domin suna nuna wa kowa cewa shi maci amana ne kuma ba ya kaunar kowa. Saboda haka, Shaidan ya ce Ayuba yana bauta wa Allah ne domin abubuwan da Allah yake ba shi. Ya ce idan Ayuba ya rasa kome, zai zagi Allah!—Ayuba 1:6-11.
Ko da yake Ayuba bai sani ba, Jehobah ya ba shi dama ta musamman na nuna cewa Shaidan makaryaci ne. Jehobah ya bar Shaidan ya sa Ayuba ya rasa abubuwan da ya mallaka. Amma bai bar shi ya ji wa Ayuba rauni ba. Nan da nan sai Shaidan ya soma muguntarsa. A rana guda, bala’o’i masu tsanani sun fado wa Ayuba. Da farko, an gaya wa Ayuba cewa shanayensa da jakunansa sun mutu. Bayan haka, ya ji cewa tumakinsa, sa’an nan rakumansa duk sun halaka. Abin takaici ma, an kashe bayin da ke kula da dabbobin. Kari ga haka, wani bawansa ya zo ya gaya masa cewa “wutar Allah” ta halaka tumakinsa da bayinsa. Watakila walkiya ce daga sama. Kafin Ayuba ya fahimci me ke faruwa, abin da ya fi wadannan hasarar muni ya faru. Yaransa goma sun taru a gidan babban yayansu, sai guguwa ta rusa gidan kuma ta halaka su gaba daya!—Ayuba 1:12-19.
Zai yi wuya mu fahimci ainihin yadda Ayuba ya ji a lokacin. Ya yayyage rigarsa, ya aske kansa kuma ya fadi a kasa. Sai Ayuba ya ce Allah ne ya ba shi kome kuma Allah ne ya kwace. Shaidan ya shirya bala’o’in nan yadda Ayuba zai dauka cewa Allah ne ya jawo su. Duk da haka, Ayuba bai zagi Allah ba, akasin abin da Shaidan ya fada. A maimakon hakan, Ayuba ya ce: “Yabo ya tabbata ga sunan Yahweh!”—Ayuba 1:20-22.
“Lallai Zai Fito a Fili Ya Yi Maka Sabo”
Shaidan ya yi fushi sosai kuma ya ki ya sare. A lokacin da mala’iku suka sake taruwa a gaban Allah, Shaidan ya bi su. Sai Jehobah ya sake yaba wa Ayuba don amincinsa duk da bala’o’in da Shaidan ya jawo masa. Amma Shaidan ya ce: “Mutum zai ... ba da dukan abin da yake da shi domin ya ceci ransa. ... Yanzu sai ka mika hannunka ka raba shi da lafiyar jikinsa, za ka gani lallai zai fito a fili ya yi maka sabo.” Shaidan yana ganin idan Ayuba ya yi rashin lafiya mai tsanani, zai yi wa Allah sabo. Jehobah ya tabbata cewa Ayuba zai rike amincinsa, don haka ya kyale Shaidan ya sa shi rashin lafiya muddin ba zai kashe shi ba.—Ayuba 2:1-6.
Ba da dadewa ba, Ayuba ya soma rashin lafiya kamar yadda aka kwatanta a farkon talifin nan. Matarsa ta zama abin tausayi. Ka yi tunanin irin bakin cikin da ta shiga saboda mutuwar yaranta goma, da kuma irin mummunar ciwon da maigidanta yake fama da shi. Ba abin da za ta iya yi don ta taimaka masa. Bakin ciki ya sa ta gaya wa Ayuba cewa: “Har yanzu kana naciya a cikin mutuncin nan naka? Yi wa Allah sabo ka mutu!” Wannan ba irin furucin da ta saba yi ba ne. Ayuba ya gane cewa ta rikice ne, shi ya sa ta fadi hakan. Duk da haka, ya ki ya zagi Allah kuma bai yi sabo ba.—Ayuba 2:7-10.
Ka san cewa abin da ya faru da Ayuba ya shafe ka? Domin maganar da Shaidan ya yi ba Ayuba ne kadai ta shafa ba, amma ta shafi dukan ’yan Adam. Ya ce: “Mutum zai ... ba da dukan abin da yake da shi domin ya ceci ransa.” Shaidan yana nufin cewa ba zai yiwu mu bauta wa Jehobah da zuciya daya ba. Wato yana cewa ba ka kaunar Allah da gaske, kuma idan ka shiga matsala sosai, za ka yi watsi da Allah don ka ceci ranka. Kamar dai Shaidan yana cewa, mu masu sonkai ne kamar shi! Za ka so ka nuna cewa shi makaryaci ne? Kowannenmu yana da damar yin hakan. (Karin Magana 27:11) Bari mu ga abin da ya faru da Ayuba bayan haka.
Mutanen da Ba Su Iya Ta’aziyya Ba
Akwai wasu mutane uku da suka ji abin da ya faru da Ayuba kuma suka kawo masa ziyara don su ta’azantar da shi. Littafi Mai Tsarki ya kira su abokansa, kuma sunayensu su ne, Elifaz da Bildad da Zofar. Da suka hange shi daga nesa, ba su gane shi ba. Sun same shi yana fama da ciwo mai zafi da ya sa fatarsa ta yi baki, don haka, kamanninsa ma ta canja gaba daya. Da suka ga hakan, sai suka yi kamar wahalar da Ayuba yake ciki ya dame su sosai, suka ta da muryoyinsu suna kuka, suna zuba kura a kawunansu. Bayan haka, sai suka zauna kusa da Ayuba suka yi tsit. Sun yi mako daya suna zaune a wurin amma ba su ce masa kome ba. Shirun da suka yi ba da nufin taimaka wa Ayuba ba ne. Mun san hakan domin ba su tambaye shi yadda yake ji ba. Sun dai ga cewa Ayuba yana fama da zafin ciwo.—Ayuba 2:11-13; 30:30.
A karshe, Ayuba da kansa ne ya soma magana. Ayuba ya la’anci ranar da aka haife shi don ya nuna irin zafin da yake fama da shi. Ayuba ya dauka cewa Allah ne ya jawo masa bala’o’in nan, abin da yake dada sa shi bakin ciki ke nan. (Ayuba 3:1, 2, 23) Duk da cewa Ayuba mutum mai bangaskiya ne, yana bukatar ta’aziyya. Amma da abokan nan nasa suka soma magana, Ayuba ya gwammace da sun ci gaba da yin shiru.—Ayuba 13:5.
Elifaz ne ya soma magana. Mai yiwuwa ya girme Ayuba sosai kuma shi ne babba cikin maza ukun. Daga baya biyun ma sun yi magana. Da alama sun bi sawun Elifaz ba tare da yin tunani ba. Za mu iya dauka cewa abin da mutanen nan suka fada ba laifi, don abubuwan da mutane da yawa suke fadi game da Allah ne suka maimaita. Kuma in ka ji, za ka dauka gaskiya ne. Alal misali, sun ce Allah mai girma ne sosai, yana hukunta mugaye kuma yana saka wa mutanen kirki da alheri. Amma maganganunsu tun farko sun nuna cewa ba abin alheri suke so su gaya wa Ayuba ba. Elifaz ya yi da’awar cewa tun da Allah mai alheri ne kuma yana hukunta mugaye, ba shakka, yana hukunta Ayuba ne don ya yi abin da bai dace ba.—Ayuba 4:1, 7, 8; 5:3-6.
Ayuba bai yarda da abin da Elifaz ya fada ba sam. (Ayuba 6:25) Amma mutane ukun su ma sun nace cewa ba shakka akwai zunubin da Ayuba ya yi da yake boyewa, shi ya sa abubuwan nan suke faruwa da shi. Elifaz ya ce Ayuba mai karambani ne, kuma shi mugu ne da ba ya tsoron Allah. (Ayuba 15:4, 7-9, 20-24; 22:6-11) Zofar ya gaya wa Ayuba cewa ya daina yin mugunta da kuma zunubin ganganci. (Ayuba 11:2, 3, 14; 20:5, 12, 13) Abin da Bildad ya fada ne ya fi muni. Ya ce da alama ’ya’yan Ayuba sun yi zunubi, don haka, ya dace da suka mutu.—Ayuba 8:4, 13.
Sun Ce Rike Aminci Bai da Amfani!
Bayan mutanen nan sun ce Ayuba bai da aminci da gaske, sun yi da’awar cewa kasancewa da aminci a gaban Allah bai da amfani. Da Elifaz ya fara maganarsa, ya ce ya gamu da wani ruhu. Wannan aljanin ya sa Elifaz ya kasance da ra’ayin nan cewa Allah ‘bai amince da bayinsa ba, yana kuma samun mala’ikunsa da laifi.’ Idan hakan gaskiya ne, ’yan Adam ba za su taba iya faranta wa Allah rai ba. Wannan ra’ayin yana da illa sosai domin zai iya sa mutum ya daina kasancewa da bangaskiya. Daga baya, Bildad ya ce Allah bai damu da amincin Ayuba ba, kamar yadda ba zai kula da amincin tsutsa ba.—Ayuba 4:12-18; 15:15; 22:2, 3; 25:4-6.
Ka taba kokarin karfafa wani da yake cikin mawuyacin hali? Babu shakka hakan bai da sauki. Amma abubuwan da abokan Ayuba suka fada su ne abubuwan da bai kamata mu fada ba idan muna kokarin ba mutane karfin gwiwa. Mutane ukun sun yi maganganu da dama da suka nuna kamar su masu hikima ne, amma ba su tausaya wa Ayuba ba kuma ba su ma kira shi da sunansa ba. Ba su damu da bakin cikin da Ayuba yake ciki ba balle su fadi abin da zai kwantar masa da hankali. * Saboda haka, idan wani da ka sani yana cikin damuwa, ka nuna masa kauna da kuma alheri. Ka taimaka masa ya dada dogara ga Allah kuma ya kasance da karfin zuciya. Kuma ka tuna masa cewa Allah mai alheri ne da jin kai da kuma adalci. Da a ce abokan Ayuba ne suke cikin halin da yake ciki, da abin da zai yi musu ke nan. (Ayuba 16:4, 5) Shin, me Ayuba ya yi da suka nace cewa shi marar aminci ne?
Ayuba Ya Rike Amincinsa
Ayuba yana fama da bakin ciki sosai sa’ad da abokansa suka fara maganganun nan. Tun farko, Ayuba ya yarda cewa a wasu lokuta ya yi “saurin magana,” wato ya yi magana ba tare da yin tunani ba. Kuma ya yi magana kamar wanda ya “fid da zuciya,” ko ya rasa na yi. (Ayuba 6:3, 26) Hakika irin wahalar da yake ciki ne ya sa ya yi magana haka. Kari ga haka, maganganunsa sun nuna cewa bai gane abin da ke faruwa da shi ba. Yadda masifun nan suka fado masa da iyalinsa ne ya sa Ayuba ya dauka cewa daga wurin Jehobah suka fito. Akwai abubuwan da ke faruwa da Ayuba bai sani ba, don haka abin da yake tunani ba daidai ba ne.
Duk da haka, Ayuba mutum mai imani ne sosai. Maganganunsa sun nuna cewa yana da imani don abubuwan da ya fada gaskiya ne kuma za su iya ba mu karfin gwiwa. Da yake magana game da halittun Allah, ya kwatanta abubuwan da dan Adam ba zai iya sani ba a lokacin sai da taimakon Allah. Alal misali, ya ce Jehobah ya “rataya duniya babu kome a ƙarƙashinta.” Sai bayan darurruwan shekaru ne ’yan kimiyya suka gano hakan. * (Ayuba 26:7) Ayuba ya kuma yi magana a kan abin da shi da mutane masu aminci da suka rayu kafin shi suke sa ran morewa a gaba. Ayuba ya yi imani cewa idan ya mutu, Allah ba zai manta da shi ba, zai yi marmarin ta da shi daga mutuwa, kuma zai yi hakan a nan gaba.—Ayuba 14:13-15; Ibraniyawa 11:17-19, 35.
Amma batun aminci kuma fa? Elifaz da abokansa biyu sun nace cewa ba amfani mutum ya rike aminci ga Allah. Shin, Ayuba ya amince da wannan mummunar ra’ayin? Ko kadan! Ayuba ya ce Allah yana murna idan dan Adam ya rike amincinsa. Da yake magana game da Jehobah Ayuba ya ce, Allah zai ga cewa shi mai ‘mutunci’ ne. (Ayuba 31:6) Kari ga haka, Ayuba ya gano cewa abokan nan nasa suna karyar ne, don kawai su nuna cewa bai da aminci. Hakan ya sa Ayuba ya yi wani dogon jawabi wanda ya sa abokan nan nasa sun yi gum da bakinsu.
Ayuba ya san cewa rike aminci ya shafi dukan abubuwan da yake yi, yau da kullum. Don haka, ya bayyana musu yadda ya rike amincinsa a duk rayuwarsa. Alal misali, ya ki ya bauta wa gumaka; ya yi wa mutane alheri kuma ya mutunta su; shi ba mai lalata ba ne kuma ya daraja aurensa; ya kuma bauta wa Allah na gaskiya, wato Jehobah, da dukan zuciyarsa. Don haka Ayuba ya sami bakin gaya musu cewa: “Har in mutu, ba zan daina tsare mutuncina ba.”—Ayuba 27:5; 31:1, 2, 9-11, 16-18, 26-28.
Ka Yi Koyi da Bangaskiyar Ayuba
Kai ma kana daukan aminci da muhimmanci kamar Ayuba? Ayuba ya san cewa ba da baki ake rike aminci ba, ana bukatar a nuna hakan ta ayyuka. Za mu nuna cewa muna bauta wa Jehobah da dukan zuciyarmu idan muna yi masa biyayya kuma muna yin abin da ya dace, ko da muna fuskantar matsaloli. Yin hakan zai sa mu faranta wa Jehobah rai sosai kamar yadda Ayuba ya yi, kuma Shaidan ba zai ji dadi ba sam. Hanya mafi kyau da za mu bi sawun Ayuba ke nan!
Ba karshen labarin Ayuba ba ke nan. Ayuba ya yi ta kokarin nuna cewa shi mai adalci ne, har ya manta ya daukaka Allah, kuma abin da ya fi muhimmanci ke nan. Yana bukatar gyara don ya daidaita tunaninsa. Amma har ila Ayuba yana fama da zafin ciwo da bakin ciki, kuma yana bukatar a kwantar masa da hankali. Mene ne Jehobah ya yi wa mutumin nan mai aminci? Za ka sami amsar a talifi na gaba a jerin talifofin nan.
^ sakin layi na 17 Abin mamaki shi ne, Elifaz ya dauka cewa da yake shi da abokansa ba su ta da murya sa’ad da suke wa Ayuba magana ba, suna ta’azantar da shi ke nan. (Ayuba 15:11) Amma za a iya fadin abin da zai cutar da mutum ba tare da an daga murya ba.
^ sakin layi na 19 Sai bayan wajen shekaru 3,000 ne ’yan kimiyya suka fara gano cewa ba a bukatar wani abu ya rike duniya. Hotunan duniya da aka dauka daga sararin sama ne suka tabbatar wa mutane cewa abin da Ayuba ya fada gaskiya ne.