Koma ka ga abin da ke ciki

TAMBAYOYIN MATASA

Yin Luwadi Zunubi Ne?

Yin Luwadi Zunubi Ne?

 David wani dan shekara 23 ya ce: “Wata matsalar da na yi fama da ita sa’ad da nake girma ita ce yin sha’awar maza. A dā, na dauka cewa zan daina jin wannan sha’awar bayan na yi girma, amma har yanzu, ina fama da ita.”

 David Kirista ne da yake so ya yi nufin Allah. Shin, zai iya yin hakan idan yana sha’awar maza? Mene ne ra’ayin Allah game da yin luwadi?

 Mene ne Littafi Mai Tsarki ya koyar game da hakan?

 Ra’ayin mutane game da luwadi ya bambanta bisa ga al’ada ko kuma zamani. Amma ba ra’ayin jama’a ne Kiristoci suke bi ba kuma ba sa barin kowace irin ‘koyarwa ta dauki hankalinsu.’ (Afisawa 4:14, Littafi Mai Tsarki) Maimakon bin ka’idodin ’yan Adam, Kiristoci suna bin abin da Littafi Mai Tsarki ya fada idan ya zo ga batun yin luwadi da ma wasu ɗabi’un.

 Abin da Littafi Mai Tsarki ya fada game da luwadi a bayyane yake. Kalmar Allah ta ce:

  •  ‘Kada ka kwana da maza kamar yadda ake yi da mata.’—Levitikus 18:22.

  •  “Allah ya bashe su ga aikata mugayen sha’awace-sha’awacen zukatansu, ... ya bashe su ga sha’awace-sha’awace masu ban kunya. Matansu kuwa suka canja daga haɗuwar mace da miji wadda ita ce daidai bisa ga halitta zuwa irin haɗuwar da ba daidai ba.”—Romawa 1:24, 26, Littafi Mai Tsarki Juyi Mai Fitar da Ma’ana.

  •  “Kada ku yaudaru; da masu fasikanci, da masu bautan gumaka, da mazinata, da baran mata, da [maza] masu kwana da maza, da barayi, da masu kyashi, da masu maye, da masu alfasha, da masu ƙwace, ba za su gāji mulkin Allah ba.”—1 Korintiyawa 6:9, 10.

 Ka’idodin da Allah ya kafa domin kowane irin mutum ne, ko da mutum mai sha’awar kwana da wanda jinsinsu daya ko a’a. Hakika, ya kamata kowa ya san yadda zai kame kansa don ya guji yin abubuwan da ba su jitu da nufin Allah ba.​—Kolosiyawa 3:5.

 Hakan yana nufin cewa . . . ?

 Hakan yana nufin cewa Littafi Mai Tsarki yana so mu tsane ’yan luwadi ne?

 A’a. Littafi Mai Tsarki bai ce a tsani kowa ba, ko da mutumin yana sha’awar kwana da wanda jinsinsu daya ne ko a’a. A maimakon haka, ya ce mu yi zaman “salama da dukan mutane” ko da wane irin dabi’a ne suke da ita. (Ibraniyawa 12:14) Saboda haka, laifi ne a ci zalin ’yan luwadi ko a ki su ko kuma a wulakanta su.

 Shin ya kamata Kiristoci su yi adawa da dokokin da suka amince da auren jinsi daya?

 Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa abin da Allah ya tsara shi ne, aure ya kasance tsakanin mata daya da miji daya. (Matta 19:​4-6) Siyasa ne yake sa ’yan Adam su kafa dokoki game da auren jinsi daya, ba wai suna bin ka’idodin da suka dace ko wadanda ba su dace ba. Littafi Mai Tsarki ya ce kada Kiristoci su sa hannu a siyasa. (Yohanna 18:36) Saboda haka, ba sa saka baki a batun da ya shafi dokokin da gwamnati ta kafa a kan auren jinsi daya ko kuma yin luwadi.

 Amma idan . . . ?

 Amma idan mutum dan luwadi ne, zai iya canja halinsa kuwa?

 E. Hakika wasu a karni na farko sun yi hakan! Bayan da Littafi Mai Tsarki ya ce maza masu kwana da maza ba za su shiga Mulkin Allah ba, sai ya ci gaba da cewa: “Wadansu ma a cikinku haka kuke.”—1 Korintiyawa 6:11.

 Shin, wadanda suka canja halinsu a lokacin ba su sake jin sha’awar yin jima’i da jinsi daya ba? A’a. Domin Littafi Mai Tsarki ya ce: ‘Ku dau sabon halin nan da ake sabuntawa ga sani bisa ga kamannin Mahaliccinsa.’ (Kolosiyawa 3:10, Littafi Mai Tsarki) Canji abu ne da ya kamata mutum ya rika yi a kowane lokaci.

 Amma idan mutumin da yake so ya bi ka’idodin Allah ya ci gaba da jin sha’awar yin jima’i da jinsi daya fa?

 Mutum yana iya zaban ya yi abin da yake sha’awarsa ko ya ki yin hakan, ko da sha’awar kwana da jinsi daya ne ko kuma na yin wani abu dabam. Ta yaya hakan zai yiwu? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ku yi tafiya bisa ga ruhu, ba kuwa za ku [aikata] sha’awar jiki ba.”—Galatiyawa 5:16.

 Ka tuna cewa ayar ba ta ce mutumin ba zai sake yin sha’awar banza ba. Amma, ta wurin karanta Littafi Mai Tsarki da kuma yin addu’a sosai mutumin zai iya hana sha’awoyin su sha kansa.

 Karatun Littafi Mai Tsarki da kuma yin addu’a ya taimaka wa David, wanda aka ambata dazu, musamman ma bayan ya gaya wa iyayensa abin da ke damunsa. Ya ce: “Na ji kamar an sauke wani kaya mai nauyi daga kafadata, kuma na san cewa da a ce na gaya wa iyayena tun da wuri, da na more kuruciyata sosai.”

 A gaskiya, idan muka bi ka’idodin Jehobah, za mu ji dadin rayuwa. Wadanda suke bin ka’idodin sun tabbata cewa ka’idodin Jehobah “daidai suke, suna farantar da zuciya” kuma idan muka “kiyaye su” za mu sami lada mai yawa.—Zabura 19:8, 11, Juyi Mai Fitar da Ma’ana.