Allah Yana Amincewa da Dukan Addinai Ne?
Amsar Littafi Mai Tsarki
A’a, ba dukan addinai ne Allah yake amincewa da su ba. Littafi Mai Tsarki ya ba mu misalan addinai da dama da ba sa faranta wa Allah rai. Sun kasu gida biyu.
Kashi na 1: Bauta wa allolin karya
Littafi Mai Tsarki ya ce bauta wa allolin karya, daya ne da aikin “banza” da kuma aiki ‘marar amfani.’ (Irmiya 10:3-5; 16:19, 20) Jehobah a ya umurci al’ummar Isra’ila ta dā cewa: ‘Ba za ku yi sujada ga wadansu alloli ba sai ni kadai.’ (Fitowa 20:3, 23; 23:24) Daga baya, da Isra’ilawan suka soma bauta wa wasu alloli, “sai fushin Yahweh ya kunna,” wato ya yi fushi sosai.—Littafin Kidaya 25:3; Littafin Firistoci 20:2; Alkalai 2:13, 14.
Har wa yau, Allah ya tsani masu bauta wa “wadanda ake ce da su alloli.” (1 Korintiyawa 8:5, 6; Galatiyawa 4:8) Ya umurci wadanda suke so su bauta masa cewa su fita sha’anin masu bautar karya, ya kuma ce: “Ku fito daga cikin marasa bi, ku wāre kanku.” (2 Korintiyawa 6:14-17) Da a ce Allah ya amince da kowane irin addini, da zai ba da irin umurnin nan?
Kashi na 2: Bauta wa Allah ba a hanyar da ta dace ba
A wasu lokuta, Isra’ilawa sun hada bautar Allah da wasu al’adun bautar allolin karya, amma Jehobah ya tsani irin wannan hadin. (Fitowa 32:8; Maimaitawar Shari’a 12:2-4) Sa’ad da yake duniya, Yesu ya yi tir da yadda malaman addinai suke bauta wa Allah. Suna nuna wa mutane a fili cewa su masu ibada ne, amma su munafukai ne kuma sun “kyale abubuwan da suka fi muhimmanci a cikin dokoki, wato gaskiya, da jin kai, da aminci.”—Matiyu 23:23.
Haka ma a yau, addinin da aka kafa a kan gaskiya ne kadai ke faranta ran Allah. Gaskiyar tana cikin Littafi Mai Tsarki. (Yohanna 4:24; 17:17; 2 Timoti 3:16, 17) Duk addinin da ke koyar da abin da ya saba wa koyar Littafi Mai Tsarki zai sa mutane su kauce daga hanyar gaskiya. Akwai abubuwa da dama da ake koyarwa a yau da mutane sun dauka yana cikin Littafi Mai Tsarki. Wadannan koyarwar sun hada da, koyarwar Allah-uku-cikin-daya, da koyarwar da ake ce idan mutum ya mutu, bai mutu kwata-kwata ba, da koyarwar nan cewa za a kona mutane a cikin wutar jahannama. Irin wadannan koyarwar sun samo asali ne daga bautar allolin karya. Duk wadanda suke koya wa mutane abubuwan nan, “a banza” suke yi, domin suna bin al’adun mutane maimakon ka’idodin Allah.—Markus 7:7, 8.
Allah ya tsane addinai da suke munafunci. (Titus 1:16) Kafin addini ya taimaka wa mutum ya zama aminin Allah, wajibi ne ya koya wa mutumin yadda zai yi rayuwa mai kyau a gaban Allah, ba wai ya bi wasu al’adu ba. Alal misali, Littafi Mai Tsarki ya ce: “Idan wani yana tsammani shi mai addini ne sosai, amma ba ya kame bakinsa, to, yana rudin kansa ne, addininsa kuma banza ne. Addinin da Allah Uba ya tabbatar mai tsarki kuma mai gaskiya, shi ne, a kula da matan da mazansu suka mutu, da kuma marayu cikin shan wuyarsu, a kuma kebe kai daga muguwar rayuwa ta duniya.”—Yakub 1:26, 27.
a Jehobah ko kuma Yahweh, shi ne sunan Allah na gaskiya bisa ga Littafi Mai Tsarki.