Koma ka ga abin da ke ciki

Ba na Jin Dadin Rayuwata ko Kadan​—Addini ko Allah ko kuma Littafi Mai Tsarki Za Su Iya Taimakawa Kuwa?

Ba na Jin Dadin Rayuwata ko Kadan​—Addini ko Allah ko kuma Littafi Mai Tsarki Za Su Iya Taimakawa Kuwa?

Amsar Littafi Mai Tsarki

 E. Tsohon littafin nan da ke cike da hikima, wato Littafi Mai Tsarki zai ba mu amsar tambayoyi masu muhimmanci a rayuwa, kari ga haka, zai taimaka mana mu ji dadin rayuwa. Ka bincika wasu tambayoyin da littafin nan ya ba da amsoshinsu.

  1.   Akwai Mahalicci kuwa? Littafi Mai Tsarki ya ce Allah ne ya “halicci dukan abu.” (Ru’ya ta Yohanna 4:11) Da yake shi ne mahaliccinmu, ya san abin da muke bukata don mu yi rayuwa mai ma’ana kuma mu ji dadi.

  2.   Allah yana kula da ni kuwa? Littafi Mai Tsarki bai ce Allah yana gudun mutane ba, amma, ya ce: “Ba shi da nisa da kowane dayanmu.” (Ayyukan Manzanni 17:27) Ya damu da abin da kake fuskanta a rayuwa kuma yana so ya taimake ka ka yi nasara.—Ishaya 48:17, 18; 1 Bitrus 5:7.

  3.   Ta yaya sanin Allah zai taimaka mini in ji dadin rayuwa? Allah ya halicce mu don mu kasance “masu-ladabi,” wato, mu rika marmarin koya game da ma’anar rayuwa kuma mu fahimci dalilin da ya sa aka halicce mu. (Matta 5:3) Kasancewa da bukata ta ibada ta kunshi son sanin Mahaliccinmu da kuma kasancewa da dangantaka mai kyau da shi. Allah zai amince da kokarin da kake yi don ka san shi. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ku kusato ga Allah, shi kuwa za ya kusato gare ku.”—Yakub 4:8.

 Miliyoyin mutane sun fahimci cewa kasancewa da dangantaka mai kyau da Allah ya sa sun kyautata rayuwarsu kuma hakan ya sa suna jin dadin rayuwa. Da yake sanin Allah ba zai sa ka daina fuskantar matsaloli a rayuwa ba, hikimarsa da ka samu a Littafi Mai Tsarki zai taimaka maka

 Addinai da yawa da suke karanta Littafi Mai Tsarki ba sa bin abin da aka rubuta a ciki. Amma wadanda suke bin abin da Littafi Mai Tsarki ya fada za su taimaka maka ka san Allah sosai.