Littafi Mai Tsarki Yana Ɗauke da Labarin Rayuwan Yesu Daidai Yadda Ya Ke Kuwa?
Amsar Littafi Mai Tsarki
Marubucin Littafi Mai Tsarki Luka ya ce game da labarin rayuwar Yesu: “Tun da fari na biddigin abubuwa duka daidai.”—Luka 1:3.
Wasu sun ce labarin rayuwar Yesu da aka rubuta cikin Lingila—rubutun da tsaransa suka yi, su Matta, Markus, Luka, da Yohanna—cewa an canja su a ƙarni na huɗu.
Amma, an sami wani gutsurin Lingilar Yohanna a farkon ƙarni na 20 a Masar. Yanzu ana kiransa Papyrus Rylands 457 (P52) kuma an adana shi a Laburare na John Rylands, Manchester, Ingila. Yana ɗauke da abin da ke a Yohanna 18:31-33, 37, 38 a cikin Littafi Mai Tsarki na zamani.
Wannan shi ne gutsurin tsohon rubutu na dā na Nassosin Helenanci na Kirista. Ɗalibai da yawa sun gaskata cewa an rubuta shi a misalin shekara ta 125 a Zamaninmu, kusan shekara 25 bayan da aka yi rubutu na asali. Abin da ke cikin gutsurin rubutun ya yi daidai da wanda ke cikin rubutun littattafan.