Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce Game da Tashin Matattu?
Amsar Littafi Mai Tsarki
A Littafi Mai Tsarki, Kalmar da aka fassara zuwa “tashin matattu” an samo ta ne daga kalmar Helenanci da ake kira a·naʹsta·sis, kuma tana nufin mutum ya “tashi” ko ya “sake tashi tsaye.” Idan aka ta da mutum daga mutuwa, mutumin zai sake rayuwa kamar yadda yake yi a dā.—1 Korintiyawa 15:12, 13.
Ko da yake ba a ambata furucin nan “tashin matattu” a Nassosin Ibrananci da ake kira Tsohon Alkawari ba, akwai koyarwar a ciki. Alal misali, ta wurin annabi Ishaya, Allah ya yi alkawari cewa: “Mutanenku da suka mutu za su rayu, gawawwakinsu za su tashi!”—Ayuba 14:13-15; Ishaya 26:19; Daniyel 12:2, 13.
A ina wadanda aka ta da za su zauna? Wasu za a ta da su zuwa sama don su yi sarauta tare da Kristi. (2 Korintiyawa 5:1; Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 5:9, 10) Littafi Mai Tsarki ya kira hakan “farkon tashin matattu,” kuma wannan ya nuna cewa akwai wani tashin matattu da za a yi bayan hakan. (Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 20:6) Tashin matattu na biyu shi ne wanda zai amfani yawancin mutanen da suka mutu. Za a ta da su su ji dadin rayuwa a duniya.—Zabura 37:29.
Ta yaya za a ta da mutane? Allah ya ba wa Yesu ikon ta da matattu. (Yohanna 11:25) Yesu zai ta da “duk wadanda suke cikin kaburbura,” kuma kowannensu zai dawo da asalin kamaninsa da halinsa da kuma tunaninsa. (Yohanna 5:28, 29) Wadanda za a ta da su zuwa sama za su kasance da jiki na ruhu, wadanda za a ta da su a nan duniya kuma, za su kasance da koshin lafiya, jikinsu garau.—Ishaya 33:24; 35:5, 6; 1 Korintiyawa 15:42-44, 50.
Su waye za a ta da? Littafi Mai Tsarki ya ce “za a tā da matattu, masu adalci da marasa adalci duka.” (Ayyukan Manzanni 24:15) Masu adalcin sun kunshi mutane kamar su Nuhu da Saratu da kuma Ibrahim. (Farawa 6:9; Ibraniyawa 11:11; Yakub 2:21) Marasa adalcin kuma sun kunshi wadanda ba su bi dokokin Allah ba domin ba su sami damar koyansu ba.
Amma ba za a ta da mugayen mutane da suka ki tuba ba. Idan suka mutu, sun hallaka ke nan har abada.—Matiyu 23:33; Ibraniyawa 10:26, 27.
Yaushe ne za a ta da matattu? Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa a lokacin bayyanuwar Yesu Kristi ne za a ta da wadanda za su yi rayuwa a sama kuma lokacin ya soma ne a shekara ta 1914. (1 Korintiyawa 15:21-23, New World Translation) A lokacin Sarautar Yesu Kristi na Shekara Dubu ne za a ta da mutanen da za su yi rayuwa a duniya, bayan an mai da ita aljanna.—Luka 23:43; Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 20:6, 12, 13.
Me ya sa ya kamata mu gaskata da tashin matattu? Littafi Mai Tsarki ya ba da labarin mutane tara da aka ta da su daga mutuwa a idanun jama’a. (1 Sarakuna 17:17-24, NW; 2 Sarakuna 4:32-37; 13:20, 21; Luka 7:11-17; 8:40-56; Yohanna 11:38-44; Ayyukan Manzanni 9:36-42; 20:7-12; 1 Korintiyawa 15:3-6) Wani labarin tashin matattu da ya yi fice shi ne na Li’azaru, domin ya yi kwana hudu da mutuwa kafin Yesu ya ta da shi a idanun jama’a. (Yohanna 11:39, 42) Ko magabtan Yesu ma ba su yi musūn cewa ya yi hakan ba, a maimako sai suka kulla cewa za su kashe Yesu da Li’azaru.—Yohanna 11:47, 53; 12:9-11.
Littafi Mai Tsarki ya nuna mana cewa Allah yana da iko kuma yana so ya ta da wadanda suka mutu. Yana sane da duk bayani game da mutumin da yake so ya yi amfani da ikonsa ya ta da. (Ayuba 37:23; Matiyu 10:30; Luka 20:37, 38) Allah yana da ikon ta da matattu kuma yana marmarin yin hakan! Sa’ad da Littafi Mai Tsarki yake kwatanta yadda Allah yake so ya ta da matattu, ya ce: “Za ka yi marmarina, ni aikin hannuwanka.”—Ayuba 14:15.
Wasu karyace-karyace game da tashin matattu
Kage: Tashin matattu yana nufin a dawo da kurwa cikin gangan jiki.
Gaskiya: Littafi Mai Tsarki ya ce kurwa ita ce mutum gabaki daya, ba wani abu da ke fita daga jikin mutum bayan ya mutu ba. (Farawa 2:7; Ezekiyel 18:4) Idan aka ta da mutum, ba dawo da kurwarsa aka yi ba, amma an sake halittar sa ne.
Kage: Za a ta da wasu mutane kuma a hallaka su nan da nan.
Gaskiya: Littafi Mai Tsarki ya ce “wadanda suka yi rashin gaskiya, za su tashi a kuwa yi musu hukunci.” (Yohanna 5:29) Wannan hukuncin, za a yi musu ne bisa ga abin da suka yi bayan an ta da su, ba bisa abin da suka yi kafin a ta da su ba. Yesu ya ce: “Hakika, ina gaya muku, lokaci yana zuwa, ya riga ya zo ma, da matattu za su ji muryar Dan Allah, wadanda suka ji kuwa za su rayu.” (Yohanna 5:25) Wadanda suka “ji” ko kuma suka yi biyayya ga abubuwan da suka koya bayan an ta da su, za a rubuta sunayensu a cikin ‘littafin rai.’—Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 20:12, 13.
Kage: Idan aka ta da mutum, za a ta da shi da ainihin jikin da aka san da shi kafin ya mutu.
Gaskiya: Bayan mutum ya mutu, jikinsa yakan rube kuma ya lalace.—Mai-Wa’azi 3:19, 20.