Tsoron Mutuwa, Ta Yaya Zan Shawo Kansa?
Amsar Littafi Mai Tsarki
Ba laifi ba ne mu ji tsoron mutuwa kuma muna iyakacin kokarinmu a tsare kanmu daga haka. (1 Korintiyawa 15:26) Amma irin banzan tsoro na razana da ake yi domin karya ko kuma camfi yana jefa mutane cikin “bauta muddar ransu.” (Ibraniyawa 2:15) Sanin gaskiya zai ’yantar da kai daga banzan tsoron mutuwa, irin tsoron da ke hana mutum sukuni a rayuwa.—Yohanna 8:32.
Gaskiya game da mutuwa
Matattu ba su san kome ba. (Zabura 146:4) Kada ka yi tunani azaba ko ciwo bayan ka mutu, domin Littafi Mai Tsarki ya kwatanta mutuwa da barci.—Zabura 13:3; Yohanna 11:11-14.
Matattu ba za su iya mana wani barna ba. Ko magabta a dā ma sun “mutu.” (Misalai 21:16) Littafi Mai Tsarki ya ce “kiyayyarsu, da kishinsu, yanzu sun kare.”—Mai-Wa’azi 9:6.
Mutuwa ba ita ce karshen rayuwarmu ba sam sam. Allah za ya dawo da mutane da suka mutu ta wurin ta da su zuwa rai.—Yohanna 5:28, 29; Ayyukan Manzanni 24:15.
Allah ya yi alkawarin lokacin da “mutuwa kuwa ba za ta kara kasancewa ba.” (Ru’ya ta Yohanna 21:4) Game da ranar nan, Littafi Mai Tsarki ya ce: “Masu-adalci za su gāji kasan, su zauna a cikinta har abada,” ba za a kara jin tsoron mutuwa kuma ba.—Zabura 37:29.