Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce Game da Zub da Ciki?
Amsar Littafi Mai Tsarki
Littafi Mai Tsarki bai yi amfani da furucin nan “zub da ciki” wato, an yi amfani da wani magani don dan tayi ya fita karfi da yaji ba. Amma, an fadi ra’ayin Allah game da rai, har da na jaririn da ke ciki a cikin ayoyin Littafi Mai Tsarki.
Rai kyauta ne daga Allah. (Farawa 9:6; Zabura 36:9) Dukan ran ’yan Adam yana da tamani ga Allah, har da ran jariri da ke ciki. Saboda haka, idan wani ya kashe jaririn da ke ciki da ganga, mutumin ya yi kisan kai ke nan.
A dokar da aka ba Isra’ilawa, an ce: “Idan mutum biyu suna cikin faɗa, sai suka yi wa mace mai ciki rauni, har cikinta ya fita, amma idan ba wani rauni kuma ba, wanda ya yi wa macen rauni za a ci masa tara bisa ga yadda mijinta ya yanka zai biya, in dai abin da mijinta ya yanka ya yi daidai da abin da masu yin shari’a suka tsara. Amma idan wani rauni ya bayyana nan gaba, sai a hukunta mai laifin bisa ga raunin, za a ba da rai a maimakon rai.”—Fitowa 21:22, 23. a
A wane lokaci ne dan tayi yake zama mutum?
Da zarar mace ta yi juna biyu, a gaban Allah dan tayin mutum ne. A cikin Kalmarsa, Allah ya nuna cewa jaririn da ke ciki ya zama mutum mai rai. Ga wasu misalai da suka nuna cewa a gaban Allah, jaririn da ke ciki da wanda aka haifa duk daya ne.
Sarki Dauda ya gaya wa Allah: “Idanunka sun ga gabobin jikina kafin su cika.” (Zabura 139:16) A gaban Allah, Dauda ya zama mutum sa’ad da yake ciki.
Kari ga haka, kafin a haife Irmiya, Allah ya san cewa akwai aiki na musamman da Irmiya zai yi. Allah ya gaya masa: “Kafin in siffata ka a cikin ciki, na san ka, tun kafin a haife ka, na keɓe ka. Na naɗa ka annabi ga al’ummai.”—Irmiya 1:5.
Luka marubucin Littafi Mai Tsarki da likita ne ya yi amfani da wannan kalmar Helenanci don ya kwatanta jaririn da ba a haifa da kuma wanda aka haifa.—Luka 1:41; 2:12, 16.
Allah zai gafarta ma wadda ta zub da ciki ne?
Allah zai iya gafarta ma wadanda suka zub da ciki. Idan suka amince da ra’ayin Allah game da rai, ba sa bukatar su ci gaba da bakin ciki. “Yahweh mai jinƙai ne, mai alheri kuma . . . kamar yadda gabas take nesa da yamma, haka ne ya sa zunuban gangancinmu sun yi nesa da mu.” b (Zabura 103:8-12) Jehobah zai gafarta ma dukan wadanda suka tuba daga zunuban su na dā, har da zub da ciki.—Zabura 86:5.
Zub da ciki laifi ne idan cikin zai kashe mahaifiyar ko kuma jariri?
Domin abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da ran dan tayi, mace ba ta da hujja zub da ciki don tana ganin cikin zai sa ranta ko jaririn cikin hadari.
Mene ne kuma za a ce game da yanayin da a lokacin haihuwa wani abu ya faru da zai sa a zabi ko za a ceci ran mahaifiyar ko na jaririn? A irin wannan yanayin, wadanda hakan ya shafa za su tsai da shawara wanda za su ceci.
a Wasu juyin Littafi Mai Tsarki sun nuna cewa abin da ya fi muhimmanci a dokar da aka ba Isra’ilawa shi ne abin da ya faru da mahaifiyar ba dan tayin ba. Amma, kalmar Ibrananci tana maganar tsausayi da ya shafi mahaifiyar ko kuma jaririn.
b Jehobah ne sunan Allah kamar yadda aka nuna a Littafi Mai Tsarki.—Zabura 83:18.