Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

29 ga Afrilu–5 ga Mayu

ZABURA 34-35

29 ga Afrilu–5 ga Mayu

Waƙa ta 10 da Adduꞌa | Gabatarwar Taro (minti 1)

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

1. “Zan Yabi Yahweh” a Koyaushe

(minti 10)

Dauda ya yabi Jehobah duk da cewa yana fama da matsaloli (Za 34:1; w07 3/1 24 sakin layi na 11)

Dauda ya yi alfahari da Jehobah, ba da abubuwan da ya cim ma ba (Za 34:​2-4; w07 3/1 24 sakin layi na 13)

Kalaman Dauda na yabo sun ƙarfafa abokansa (Za 34:5; w07 3/1 25 sakin layi na 15)

Bayan Dauda ya bar Abimelek, mutane 400 da ba sa jin daɗin mulkin Sarki Saul sun zo sun goyi bayan Dauda a daji. (1Sam 22:​1, 2) Wataƙila Dauda ya yi tunani game da mutanen nan ne saꞌad da ya rubuta wannan zaburar.—Za 34.

KA TAMBAYI KANKA, ‘Ta yaya zan yabi Jehobah saꞌad da nake magana da wani a taron ikilisiya da za a yi?’

2. Abubuwa Masu Daraja Daga Kalmar Allah

(minti 10)

  • Za 35:11—Mene ne ya faru a zamanin Yesu da aka annabta a wannan ayar? (w11 8/15 14 sakin layi na 9)

  • A karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon, waɗanne abubuwa masu daraja ne ka samu?

3. Karatun Littafi Mai Tsarki

(minti 4) Za 34:​1-22 (th darasi na 5)

KA YI WAꞌAZI DA ƘWAZO

4. Fara Magana da Mutane

(minti 2) SAꞌAD DA KAKE AYYUKA NA YAU DA KULLUM. Kun kammala hiranku kafin ka sami damar yi wa mutumin waꞌazi. (lmd darasi na 1 batu na 4)

5. Komawa Ziyara

(minti 4) SAꞌAD DA KAKE AYYUKA NA YAU DA KULLUM. (lmd darasi na 2 batu na 4)

6. Ka Bayyana Imaninka

(minti 5) Gwaji. lff darasi na 44 batu na 1-3—Jigo: Ta Yaya Shaidun Jehobah Suke Sanin Bukukuwan da Ba Su Dace Ba? (th darasi na 17)

RAYUWAR KIRISTA

Waƙa ta 59

7. Hanyoyi Uku Na Yabon Jehobah a Taronmu

(minti 15) Tattaunawa.

Akwai hanyoyi da dama da za mu iya yabon Jehobah a taron ikilisiya. Ga guda uku a cikinsu.

Tattaunawa: Ku riƙa tattaunawa da juna game da yadda Jehobah yake mana alheri. (Za 145:​1, 7) Kun ji ko karanta wani batun da ya amfane ku? Kuna da wasu labarai masu daɗi game da waꞌazi? Kun sami ƙarfafa daga wani ta wajen furucinsa ko kuma ayyukansa? Kun ga wani abu game da wata halitta da ya burge ku? Dukan abubuwan nan kyauta ne daga Jehobah. (Yak 1:17) Ku dinga zuwa da wuri kafin a soma taro don ku sami damar tattaunawa da mutane.

Yin kalami: Ku yi ƙoƙari ku riƙa yin kalami ko ɗaya ne a kowane taro. (Za 26:12) Za ku iya ba da amsar tambayar farko da aka yi ko kuma ku ba da ƙarin bayani daga talifin ko wata aya ko hoto ko kuma darussan da muka samu. Da yake wasu za su iya ɗaga hannu saꞌad da kai ma ka ɗaga hannu, don haka ka shirya kalamai da yawa. Mutane da yawa za su iya “miƙa hadayar yabo ga Allah” idan kalamanmu ba su wuci sakan 30 ko kasa da hakan.—Ibr 13:15.

Waƙoƙi: Ku riƙa rera waƙoƙinmu da ƙwazo. (Za 147:1) Mai yiwuwa ba a kowane taro ne za a kira ka ka yi kalami ba, musamman idan kuna da yawa a ikilisiyar, amma za ka iya rera waƙoƙinmu tare da ꞌyanꞌuwa a koyaushe. Ko da kana ganin cewa ba ka iya rera waƙa sosai ba, idan ka yi iya ƙoƙarinka ka rera, hakan zai sa Jehobah farin ciki. (2Ko 8:12) Za ku iya rera waƙoƙin a gida kafin ku zo taro.

Ku kalli BIDIYON Tarihinmu da Ci gaban da Muka Samu—Kyautar Waƙa, Kashi na 1. Sai ka tambayi masu sauraro:

A dā, ta yaya ƙungiyarmu ta nuna cewa rera waƙoƙi ga Jehobah yana da muhimmanci?

8. Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya

Kammalawa (minti 3) | Sabuwar Waƙa na Taron Yanki na 2024 da Adduꞌa