Koma ka ga abin da ke ciki

Littafi Mai Tsarki Yana Gyara Rayuwar Mutane

Littafi Mai Tsarki Yana Gyara Rayuwar Mutane

Littafi Mai Tsarki Yana Gyara Rayuwar Mutane

AKWAI wani babban dan kasuwa daga kasar Scotland da ya sami wani abu, ya ce wannan abin ya fi kasuwancin da yake yi muhimmanci. Me ke nan? Me ya taimaka ma wani mutumin Brazil ya daina halin lalata kuma ya bar shan hodar Ibilis? Yaya aka yi wani mutumin Slovenia ya daina shan giya da yawa? Bari mu ji daga bakinsu.

“Ba abin da na rasa.”​—JOHN RICKETTS

SHEKARAR HAIHUWA: 1958

KASAR HAIHUWA: SCOTLAND

TARIHI: BABBAN DAN KASUWA

RAYUWATA A DĀ: Na taso ne a iyalin masu kudi. Da yake babana babban hafsa ne a cikin sojojin Birtaniya, mun yi zama a wurare da yawa. Ban da Scotland, mun yi zama a Ingila da Jamus da Kenya da Malaysia da Ireland da kuma Cyprus. Ina dan shekara 8 na soma zuwa makarantun kwana a kasar Scotland. Bayan haka, na kammala karatuna a Jami’ar Cambridge da ke Ingila.

Ina dan shekara 20 na soma aiki da ya shafi harkar man fetur. Na soma wannan aikin ne a Amirka ta Kudu, daga baya na je Afirka da kuma Yammacin Ostireliya. Da na je Ostireliya na soma nawa kasuwancin. Amma daga baya na sayar da shi.

Na ga cewa kudin da na samu zai ishe ni, don haka na yi ritaya ina da shekara 40. Da yake ina da lokaci, sai na shiga yin tafiye-tafiye. Cikin yawon da na yi, na zagaya Ostireliya sau biyu da babur. Kuma na zagaya duniya gabaki daya. Ba abin da na rasa.

YADDA LITTAFI MAI TSARKI YA CANJA RAYUWATA: Tun kafin in yi ritaya na soma tunanin yadda zan gode wa Allah don irin gatan da na samu a rayuwa. Don haka, sai na koma zuwa cocin Angilika, don dā cocinmu ke nan. Amma na ga cewa yawancin abubuwan da suke fada ba daga Littafi Mai Tsarki ba ne. Bayan haka, sai na soma bin mutanen wani coci da ake kira Mormons muna binciken abin da ya shafi addini. Amma na ga cewa su ma ba su dogara da Littafi Mai Tsarki ba, sai na soma shakkar su.

Ana nan sai wata rana Shaidun Jehobah suka zo gidana. Suna gama magana, na ga cewa duk koyarwarsu daga Littafi Mai Tsarki ne. Akwai wata aya da suka karanta min, wato 1 Timoti 2:​3, 4. Wurin ya nuna cewa Allah yana “so dukan mutane su sami ceto, su kuma kai ga sanin gaskiya.” Sun ce ya kamata Kirista ya bincika ainihi abin Littafi Mai Tsarki yake koyarwa. Da na ji hakan, abin ya burge ni sosai.

Binciken Littafi Mai Tsarki da na yi da Shaidun Jehobah ya sa na gano ainihin abin da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa. Alal misali, na koyi cewa Yesu ba shi ne Allah ba, shi dabam yake da Allah Madaukaki. (Yohanna 14:28; 1 Korintiyawa 11:3) Wannan abin da na koya, ya faranta min rai sosai. Amma da na tuna irin fama da na yi ina kokarin fahimtar yadda za a ce akwai Allah uku cikin daya, sai na ji raina ya bi ya bace. Don koyarwar karya ce da ba a iya fahimtar ta.

Ba da jimawa ba, sai na soma zuwa taron Shaidun Jehobah. Na ga cewa suna da fara’a kuma suna da kirki. Irin kaunar da suke nuna wa juna ya tabbatar min cewa suna bin addinin gaskiya.​—Yohanna 13:35.

YADDA NA AMFANA: Da na yi baftisma, sai na sami wata macen kirki mai suna Diane. Iyayenta Shaidun Jehobah ne kuma tana da hali mai kyau. A kwana a tashi sai muka yi aure. A kullum ina gode wa Jehobah da ya ba ni mace irinta da take kaunata kuma tana taimaka min.

Ni da matata mun so mu je wa’azi a inda mutane da yawa suke so su ji maganar Allah. Don haka, a 2010 sai muka koma birnin Belize, da ke Amirka ta Tsakiya. A wurin, muna samun mutane da yawa da suke kaunar Allah. Muna musu wa’azi don suna so su san Allah sosai.

Yanzu da na san gaskiya game da Allah da ainihin abin da Kalmarsa Littafi Mai Tsarki take koyarwa, hankalina ya kwanta. Yanzu ni mai wa’azi na cikakken lokaci ne. Kuma na sami damar koya wa mutane da yawa Littafi Mai Tsarki. Idan na ga mutane suna gyara rayuwarsu don abin da suka koya daga Littafi Mai Tsarki, kamar yadda ni ma na yi, nakan ji dadi ba kadan ba. Ba abin da ya fi hakan. Dā ina neman hanyar da zan gode wa Allah don irin gatan da na samu a rayuwa, yanzu na samu.

“Sun nuna suna kaunata sosai.”​—MAURÍCIO ARAÚJO

SHEKARAR HAIHUWA: 1967

KASAR HAIHUWA: BRAZIL

TARIHI: YAYI RAYUWAR LALATA

RAYUWATA A DĀ: A wani gari da ake kira Avaré ne na taso. Avaré wani karamin gari ne a jihar São Paulo. Kuma yawancin mutanen da ke zama a wurin talakawa ne.

Mahaifina ya rasu a lokacin da mamata take dauke da cikina. Da nake karami, nakan sace kayan mamata in saka. Na soma yin abubuwa kamar tamace har mutane sun ce na zama dan Daudu. A kwana a tashi, na soma yin lalata da maza, manya da kanana.

Kafin in kai shekara 20, na soma neman maza da mata don in kwana da su. Ina zuwa duk inda zan same su. Ina zuwa inda ake sayar da giya da wurin fati har ma da coci ina nemansu. Idan ana manyan bukukuwan gargajiya, nakan sa kayan mata kuma in yi ta rawa. A lokacin kowa ya san da ni.

Abokaina ’yan daudu ne da karuwai da masu shan kwaya. Wasunsu sun rinjaye ni har na soma shan hodar Ibilis (crack cocaine). Kafin in hankara, shan hodar Ibilis ya zama min jiki. A wani lokaci mukan kwana muna sha. Wani lokacin kuma nakan je inda babu kowa in wuni ina sha. Na rame sosai, har mutane sun ce na kamu da ciwon sida.

YADDA LITTAFI MAI TSARKI YA CANJA RAYUWATA: A wannan lokacin ne na hadu da Shaidun Jehobah. Sun nuna cewa suna kaunata sosai. Wata aya da suka karanta min ita ce Romawa 10:​13. Ayar ta ce: “Duk wanda ya kira ga sunan Ubangiji zai sami ceto.” Abin da ayar nan ta ce ya sa na ga muhimmancin yin amfani da sunan Allah, wato Jehobah. Akwai lokuta da dama bayan na kwana ina shan hodar Ibilis, sai in bude wundo, in daga ido sama ina kuka ina rokon Allah ya taimake ni in fita daga wannan jarabar.

Da na ga yadda mahaifiyata take shan wahala sosai don shaye-shayen da nake yi, sai na tsai da shawara cewa zan daina. Bayan haka, sai na ce Shaidun Jehobah su soma nazarin Littafi Mai Tsarki da ni. Sun ba ni tabbacin cewa nazarin nan zai ba ni kwarin gwiwa in daina shan kwaya. Kuma abin da ya faru ke nan.

Binciken da nake yi a Littafi Mai Tsarki ya sa na ga cewa zai dace in canja irin rayuwar da nake yi. Bai min sauki in daina halin dan daudu ba, don tun ina karami na soma wannan halin. Wani abin da ya taimaka min in bar wannan halin shi ne, na daina bin abokaina na dā, kuma na daina zuwa wuraren fati da wuraren shan giya.

Canja halina bai min sauki ba kam, amma na ji dadi da na koya cewa Jehobah ya damu da ni kuma ya san irin famar da nake yi. (1 Yohanna 3:​19, 20) A shekara ta 2002, na daina halin dan daudu kwata-kwata kuma na yi baftisma, na zama Mashaidin Jehobah.

YADDA NA AMFANA: Mamata ta ji dadi sosai da ta ga yadda na canja halina. Har ita ma ta soma nazarin Littafi Mai Tsarki. Sai dai kafin wannan lokacin, ta riga ta kamu da cutar shanyewar jiki. Duk da rashin lafiyarta, mamata tana kaunar Jehobah da koyarwar Littafi Mai Tsarki.

Yanzu na yi shekaru takwas ina wa’azi sosai, ina koya wa mutane abin da ke Littafi Mai Tsarki. A wasu lokuta nakan ji sha’awar yin abin da bai dace ba, amma da yake ba na biye ma sha’awoyin nan, na san cewa Jehobah yana farin ciki. Abin da yake karfafa ni ke nan.

Yanzu ina da mutunci kuma ina jin dadi don na kusaci Allah kuma ina yin abin da yake so a rayuwata.

“Dā ni tulu ne da ba a ganin kasarsa.”​—LUKA ŠUC

SHEKARAR HAIHUWA: 1975

KASAR HAIHUWA: SLOVENIA

TARIHI: BABBAN MASHAYI

RAYUWATA A DĀ: An haife ni a birnin Ljubljana, wanda shi ne babban birnin Slovenia. Iyayena sun raine ni da kyau, amma da na kai shekara hudu sai mahaifina ya kashe kansa. Daga wannan lokacin, mamata ce ta shiga yin buge-buge don ta samu kudin da za ta kula da ni da yayana.

Da na kai shekara 15, sai na koma zama da kakata. Na ji dadin zama da ita domin dā ina da abokai da yawa a unguwarsu. Kuma tana bari na in yi duk abin da na ga dama. Ba na samun takura kamar a gidanmu. Da na kai shekara 16, sai na soma bin wadanda suke zuwa shan giya a ranar Asabar da Lahadi. Na bar suman kaina ya yi tsayi sosai. Na soma sa kaya na ’yan iska, kuma a kwana a tashi na soma shan taba.

Na sha kwayoyi iri-iri, amma abin da na fi so a lokacin shi ne shan giya. Da na fara shan giya, kadan-kadan nake sha, amma ba da jimawa ba sai na fara sha fiye da kwalba daya. Da haka na shiga shan giya da yawa, kuma ba a ganin alamar buguwa a jikina. A yawancin lokaci, warin giyar ne yake sa mutane su san cewa na sha. Duk da haka, ba sa sanin cewa giyar da na sha ya kai lita da yawa. Ban da haka ma, nakan hada shi da wani irin abin sa jiri mai karfi da ake kira vodka.

Mukan je wurin fati da abokaina mu kwana muna shan giya. Ko da yake nakan sha giya da ta dara nasu, a yawancin lokaci ni nake taimaka musu su san hanyar gida. Ana nan sai wata rana na ji wani abokina yana cewa ni tulu ne da ba a ganin kasarsa. A yarenmu, idan aka gaya wa mutum haka zagi ne, kuma yana nufin mutumin da ya fi kowa shan giya. Abin da ya fada ya yi min zafi sosai.

Don haka, sai na soma tunani a kan irin rayuwar nan da nake yi. Wannan halin ya mai da ni mutumin banza. Na bi na ji kamar ba na yin wani abin kirki a rayuwata.

YADDA LITTAFI MAI TSARKI YA CANJA RAYUWATA: A wannan lokacin, akwai wani dan ajinmu da na ga cewa halinsa ya canja. Ya zama mutumin kirki. Na so in san ya aka yi ya canja haka. Don haka, sai na ce masa mu je mu yi hira a wani wurin shan shayi. Da muka hadu a wurin shayin muna hira, sai ya gaya min cewa ya soma binciken Littafi Mai Tsarki da Shaidun Jehobah. Ya gaya min wasu abubuwa da ya koya. Abubuwan da ya gaya min, ban taba jinsu ba, don ban taba zuwa coci ba balle in karanta Littafi Mai Tsarki. Ni ma sai na soma zuwa taron Shaidun Jehobah kuma na ce su soma nazari da ni.

Da muka shiga nazarin, na koyi abubuwa da yawa a Littafi Mai Tsarki da suka sa ni na ce zan daina irin rayuwar da nake yi. Alal misali, na koyi cewa muna rayuwa ne a kwanakin karshe. (2 Timoti 3:​1-5) Na kuma koyi cewa nan ba da dadewa ba, Allah zai hallaka dukan mugayen mutane, kuma zai sa mutanen kirki su yi rayuwa har abada a cikin aljanna. (Zabura 37:29) Don haka, na ce ko ta yaya zan canja halina don ni ma in samu in shiga aljannar.

Daga nan sai na soma ba abokaina labarin abubuwan da na koya a Littafi Mai Tsarki. Yawancinsu sun shiga yi min dariya. Amma wannan dariya da suka yi min ya taimaka mini sosai, don ya sa na ga cewa ashe tun dā su ba abokan kirki ba ne. Na gane cewa wadannan abokan ne suka kara sa ni na shiga wannan halin shaye-shaye. A koyaushe, alla-alla suke yi a zo karshen mako don su samu su sha su bugu.

Na daina bin wadannan abokan kuma na soma bin abokan da su ma Shaidun Jehobah ne. Idan ina tare da Shaidun Jehobah, ina samun kwarin gwiwar yin abin da ya dace. Domin su ma suna kaunar Allah kuma suna son yin abin da ya ce. A hankali a hankali, na daina shan giya da yawa.

YADDA NA AMFANA: Ina godiya sosai ga Jehobah domin yanzu ba sai na sha giya kafin in ji hankalina ya kwanta ba. Da ban daina wannan halin ba, da Allah ne kadai ya san yadda rayuwata za ta zama. Ga shi yanzu ina yin rayuwa mai kyau.

Yanzu na yi shekaru bakwai ina hidima a ofishin Shaidun Jehobah da ke Slovenia. Yanzu rayuwata tana da kan gado, domin na san Jehobah kuma ina bauta masa.