Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 2

Wane Ne Allah na Gaskiya?

Wane Ne Allah na Gaskiya?

1. Me ya sa ya kamata mu bauta wa Allah?

Allah na gaskiya shi ne Mahaliccin dukan abubuwa. Ba shi da mafari kuma ba zai taɓa samun ƙarshe ba. (Zabura 90:2) Shi ne Tushen albishirin da ke cikin Littafi Mai Tsarki. (1 Timotawus 1:11) Ya kamata mu bauta wa Allah kaɗai tun da shi ne ya ba mu rai.​—Karanta Ru’ya ta Yohanna 4:11.

2. Yaya kamannin Allah yake kuma wane irin Allah ne shi?

Babu wanda ya taɓa ganin Allah domin shi Ruhu ne. Ruhu wani irin jiki ne da ya fi na ’yan Adam. (Yohanna 1:18; 4:24) Idan muka lura da abubuwan da Allah ya halitta za mu san ra’ayinsa. Alal misali, ’ya’yan itatuwa da furanni dabam-dabam da muke gani, suna bayyana ƙaunar Allah da kuma hikimarsa. Girman sararin samaniya yana nuna mana cewa Allah yana da iko sosai.​—Karanta Romawa 1:20.

Za mu iya ƙara koyon halayen Allah ta wurin karanta Littafi Mai Tsarki. Alal misali, Littafi Mai Tsarki ya gaya mana abin da Allah yake so da abin da ba ya so, yadda yake bi da mutane da kuma yadda yake bi da abubuwa a yanayi dabam-dabam.​—Karanta Zabura 103:7-10.

3. Allah yana da suna ne?

Yesu ya ce: ‘Ubanmu wanda ke cikin sama, a tsarkake sunanka.’ (Matta 6:9) Ko da yake Allah yana da laƙabi da yawa, amma yana da suna ɗaya tak. Kowane yare suna da yadda suke kiransa. A Hausa muna kiransa “Jehobah” ko kuma “Yahweh.”​—Karanta Zabura 83:18.

An cire sunan Allah daga fassarori da dama na Littafi Mai Tsarki kuma an sauya sunan da laƙabin nan Ubangiji ko Allah. Amma sa’ad da aka rubuta Littafi Mai Tsarki, sunan Allah ya bayyana wajen sau 7,000. Yesu ya bayyana sunan sa’ad da yake koya wa mutane game da Allah.​—Karanta Yohanna 17:26.

Ka kalli bidiyon nan Allah Yana da Suna Ne?

4. Jehobah ya damu da mu kuwa?

Kamar wannan mahaifi mai ƙauna, Allah yana yin abubuwan da za su sa mu yi farin ciki a nan gaba

Wahalar da mutane da yawa suke sha yana nufin cewa Allah bai damu da mu ba ne? Waɗansu mutane suna da’awar cewa Allah yana ƙyale mu mu sha wahala ne don ya jarabce mu, amma hakan ba gaskiya ba ce.​—Karanta Yaƙub 1:13.

Allah ya ba mutane ’yancin yin zaɓi. Muna godiya sosai domin ’yancin da muke da shi na bauta wa Allah, ko ba haka ba? (Joshua 24:15) Ana shan wahala sosai domin mutane da yawa sun zaɓi su yi wa wasu mugunta. Jehobah yana baƙin ciki sosai yayin da yake ganin irin wannan rashin adalcin.​—Karanta Farawa 6:5, 6.

Jehobah Allah ne da yake damuwa da mu. Yana son mu ji daɗin rayuwa. Zai kawar da dukan wahala da kuma waɗanda suke haddasa ta nan ba da daɗewa ba. Amma a yanzu, yana da dalili mai kyau na ƙyale wahala na ɗan lokaci. A Darasi na 8, za mu san wannan dalilin.​—Karanta 2 Bitrus 2:9; 3:7, 13.

5. Ta yaya za mu iya kusantar Allah sosai?

Jehobah ya gayyace mu mu kusace shi ta wajen yin addu’a. Yana ƙaunar kowannenmu. (Zabura 65:2; 145:18) Yana a shirye ya gafarta kurakuranmu. Ko da yake muna kuskure a wasu lokatai, amma ya san ƙoƙarin da muke yi don mu bauta masa. Saboda haka, za mu iya ƙulla dangantaka na kud da kud da shi duk da yake mu ajizai ne.​—Karanta Zabura 103:12-14; Yaƙub 4:8.

Tun da yake Jehobah ne ya ba mu rai, ya kamata mu ƙaunace shi fiye da kowane mutum. (Markus 12:30) Yayin da kake nuna cewa kana ƙaunar Allah ta wajen koyon abubuwa da yawa game da shi da kuma yin abubuwa da yake bukata a gare ka, za ka kusace shi sosai.​—Karanta 1 Timotawus 2:4; 1 Yohanna 5:3.