BABI NA TARA
Ta Nuna Basira
1-3. (a) Mene ne ya jefa iyalin Abigail cikin matsala? (b) Mene ne za mu koya game da wannan macen da ta yi fice?
ABIGAIL ta lura cewa saurayin yana cike da tsoro. Akwai ƙwaƙƙwaran dalilin da ya sa hankalinsa ya tashi. Wani mugun abu na gab da faruwa. Mayaƙa aƙalla ɗari huɗu suna nan tafe, kuma sun ƙudurta cewa za su kashe dukan mazajen da ke gidan Nabal, mijin Abigail. Amma, ka san abin da ya sa?
2 Nabal ne ya tsokano faɗa. Ya yi wulaƙanci da rashin kunya, kamar yadda ya saba yi. Amma a wannan lokacin, ya wulaƙanta mutumin da ya fi ƙarfinsa, wato shugaban wasu ƙwararrun mayaƙa masu aminci. Sai wani matashi da ke yi wa Nabal aiki, wataƙila makiyayi ne, ya zo wajen Abigail kuma yana da tabbaci cewa za ta nemi hanyar kāre su. Amma mene ne mace guda za ta iya yi wa rundunar soja?
Mene ne mace guda za ta yi wa rundunar sojoji?
3 Yanzu, bari mu fara tattauna game da wannan macen da ta yi fice. Wace ce Abigail? Ta yaya wannan bala’in ya taso? Kuma mene ne za mu iya koya daga bangaskiyarta?
‘Mai-Fahimi da Kuma Kyakkyawa’
4. Waye ne Nabal?
4 Abigail da Nabal ba su dace da juna ba. Nabal ya yi dacen mata, amma ita ba ta yi dacen miji ba. Hakika, mutumin yana da kuɗi, shi ya sa ya ɗauki kansa da muhimmanci sosai. Amma yaya wasu suka ɗauke shi? Da wuya ka ga wani da aka kwatanta da irin waɗannan kalamai masu muni a cikin Littafi Mai Tsarki. Sunansa yana nufin “Marar hankali” ko “Wawa.” Shin iyayensa ne suka ba shi wannan sunan ko kuwa an sa masa sunan ne saboda ayyukansa? Ko ta yaya, ya ci sunansa. Nabal “mai-tankiya ne 1 Sam. 25:2, 3, 17, 21, 25.
mai-munanan ayyuka.” Mutane suna tsoronsa kuma sun ƙi jininsa don shi azzalumi ne da mashayi.—5, 6. (a) Waɗanne cikin halayen Abigail kake gani suka fi kyau? (b) Mene ne wataƙila ya sa Abigail ta auri irin wannan sakaran?
5 Abigail kuwa ta fita dabam da mijinta. Sunanta na nufin “Mahaifina Ya Faranta Zuciyarsa.” Maza da yawa suna alfahari idan ’yarsu kyakkyawa ce, amma uba mai hikima ya fi farin ciki idan ’yarsa tana da halin kirki. A yawancin lokatai, mutumin da ke da kyaun sura ba ya ganin amfanin kasancewa da halaye masu kyau kamar su basira da hikima da gaba gaɗi da kuma imani. Amma ba haka Abigail take ba. Littafi Mai Tsarki ya ce ita mace “mai-fahimi ce, kyakkyawa” kuma.—Karanta 1 Sama’ila 25:3.
6 Wasu mutane a yau za su yi mamakin abin da ya sa irin wannan kyakkyawar mace mai hankali ta auri wannan sakarai. Amma, ka tuna cewa iyaye ne suke zaɓa wa yawancin yaransu mata a zamanin dā. Ko da ba su zaɓa musu mata ba, sai sun amince da auren. Shin iyayen Abigail sun goyi bayan wannan auren, ko kuma sun shirya auren ne domin suna son wadatar Nabal? Sun yarda ya aure ta ne domin su fatararru ne? Ko yaya dai, wadatar Nabal ba ta sa shi ya zama mijin kirki ba.
7. (a) Mene ne bai kamata iyaye su yi ba idan suna son su koya wa yaransu ra’ayin da ya dace game da aure? (b) Mene ne Abigail ta ƙudura niyyar yi?
7 Iyaye masu hikima suna koya wa yaransu yadda za su daraja aure. Ba sa gaya wa yaransu su auri wani saboda wadata, ko kuwa su matsa musu su fara fita zance da wani tun ba su isa aure ba. (1 Kor. 7:36) Amma ga Abigail, bakin alƙalami ya riga ya bushe. Ta riga ta auri Nabal, kuma ta ƙudurta ta nuna hikima ko ma a yanayi mai tsanani.
“Ya Zazzage Su”
8. Wane ne Nabal ya zaga, kuma me ya sa hakan bai dace ba?
8 Nabal ya zagi Dauda kuma hakan ya daɗa tsananta yanayin Abigail. Dauda amintaccen bawan Jehobah ne wanda annabi Sama’ila ya shafe, don nuna cewa Allah ya zaɓe shi ya sauya Saul a matsayin sarki. (1 Sam. 16:1, 2, 11-13) Dauda ya gudo daga Sarki Saul mai kishi da kisa, kuma ya ɓoye a cikin jeji tare da sojojinsa masu aminci ɗari shida.
9, 10. (a) A wane irin yanayi ne Dauda da mutanensa suke fama su rayu? (b) Me ya sa ya kamata Nabal ya nuna godiya ga abin da Dauda da mutanensa suke yi? (Duba hasiyar da ke sakin layi na 10.)
9 Nabal yana da zama a garin Maon, amma yana aiki a garin * Waɗannan garurruka masu tsaunuka sun dace da kiwon tumaki domin suna da ciyayi, kuma Nabal yana da tumaki dubu uku. Kurmi ya zagaye garin. Jejin Paran yana kudancin ƙasar. Hanyar zuwa Tekun Gishiri kuma tana gabas a cikin hamada da ke cike da kwazazzabai da koguna. A waɗannan wuraren ne Dauda da mutanensa suke fama don su rayu, suna neman abin da za su ci kuma suna jimre wahaloli da yawa. Suna yawan haɗuwa da matasan da ke kiwon tumakin Nabal mai arziki.
Karmel kuma wataƙila yana da fili a wurin.10 Ta yaya sojojin nan da ke shan wahala don su rayu suka bi da waɗannan makiyayan? Suna iya satar tunkiya a kai a kai idan suka ga dama, amma ba su yi hakan ba. Akasi, sun kāre tumakin Nabal da bayinsa. (Karanta 1 Sama’ila 25:15, 16.) A lokacin, tumaki da makiyaya suna fuskantar haɗarurruka, domin akwai masu kwace da kisa da yawa. Wurin yana kusa da iyakar kudancin ƙasar Isra’ila, shi ya sa a yawancin lokatai, ɓarayi daga ƙasashen waje suna shigowa su yi sata. *
11, 12. (a) Ta yaya Dauda ya yi amfani da basira kuma ya daraja Nabal a saƙon da ya aika masa? (b) Me ya sa yadda Nabal ya amsa saƙon Dauda bai dace ba?
11 Ciyar da dukan waɗannan mutanen a cikin jeji ba ƙaramin aiki ba ne. Saboda haka, wata rana Dauda ya aiki mutane goma zuwa wurin Nabal don neman taimako. Dauda ya zaɓi lokaci mafi kyau. Lokacin biki ne na rarraba tumaki, sa’ad da ake ba da kyauta. Dauda ya yi amfani da kalamai masu kyau, kuma masu daɗin ji. Ya ma ce: “Ka ba bayinka ko mene ne da ya shiga hannunka, har kuma ga ɗanka Dauda.” Ya ce shi ɗan Nabal ne wataƙila domin Nabal dattijo ne. Amma, mene ne Nabal ya ce?—1 Sam. 25:5-8.
12 Sai ya yi fushi! “Ya kuwa yi musu furji” in ji matashin da aka ambata da farko sa’ad da yake bayyana wa Abigail abin da ya faru. Nabal marowaci ya yi gunaguni game da abincinsa da ruwa da kuma nama. Ya yi wa Dauda ba’a kuma ya mai da shi mutumin banza da kuma bawan da ya gudu daga wajen maigidansa. Wataƙila ra’ayin Nabal ya yi daidai da na Saul, wanda ya ƙi jinin Dauda. Su biyun ba su da ra’ayin Jehobah. Jehobah ya ƙaunaci 1 Sam. 25:10, 11, 14.
Dauda kuma ya ɗauke shi a matsayin mai jiran gadon sarautar Isra’ila, ba bawa mai tawaye ba.—13. (a) Mene ne Dauda ya yi bayan Nabal ya zazzage shi? (b) Ƙa’idar da ke littafin Yaƙub 1:20 ta koya mana mene ne game da yadda Dauda ya aikata?
13 Sa’ad da bayin Dauda suka gaya masa abin da ya faru, sai ya yi fushi. Ya ce wa mutanensa, “kowane mutum shi rataye takobinsa.” Riƙe da nasa makamin, Dauda ya tafi da mutanensa ɗari huɗu don su kai hari. Ya yi alkawarin kashe dukan mazajen da ke gidan Nabal. (1 Sam. 25:12, 13, 21, 22) Fushin da Dauda ya yi ba laifi ba ne, amma yadda yake son ya nuna fushinsa ne bai dace ba. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Fushin mutum ba ya aikata adalcin Allah.” (Yaƙ. 1:20) Ta yaya Abigail za ta ceci mutanen gidanta?
“Mai-Albarka Ce Hikimarki”
14. (a) Wane mataki ne Abigail ta fara ɗauka don ta magance matsalar da mijinta ya jawo? (b) Wane darasi muka koya daga yadda Nabal da Abigail suka bambanta? (Duba hasiya.)
14 Mun riga mun ga mataki na farko da Abigail ta ɗauka don ta magance abin da ya riga ya faru. Ba kamar mijinta ba, Abigail ta saurara sosai. Bawan ya ce game da Nabal: “Shi shaƙiyin mutum ne, har ba shi yiwuwa a yi magana da shi.” * (1 Sam. 25:17) Abin baƙin ciki, Nabal bai saurara ba saboda ya ɗauki kansa da muhimmanci. Irin wannan girman kan ya zama ruwan dare a yau. Amma wannan bawan ya san cewa ba haka Abigail take ba, shi ya sa ya gaya mata wannan matsalar.
Ba kamar mijinta Nabal ba, Abigail ta saurara sosa
15, 16. (a) Ta yaya Abigail ta nuna cewa tana kamar matar kirki da aka ambata a littafin Misalai? (b) Me ya sa abin da Abigail ta yi ba raini ba ne ga shugabancin mijinta?
15 Abigail ta yi tunani kuma ta ɗauki mataki nan da nan. Littafi Mai Tsarki ya ce “Abigail ta yi sauri.” An yi amfani da wannan aikatau, “sauri” sau huɗu game da wannan matar a labarin. Ta shirya kyautar da za ta ba Dauda da rundunarsa. Kyautar ta haɗa da gurasa da ruwan anab da raguna da soyayyen hatsi da wainar ’ya’yan inabi da kuma wainar ɓaure. Babu shakka, Abigail ta san abubuwan da take da shi kuma takan yi ayyukanta na gida, kamar matar kirki da aka ambata a littafin Misalai. (Mis. 31:10-31) Ta sa wasu cikin bayinta su yi gaba da tanadin, sai ta bi su a baya. Littafi Mai Tsarki ya ce “ba ta faɗa wa Nabal, mijinta ba.”—1 Sam. 25:18, 19, Littafi Mai Tsarki.
16 Shin hakan ya nuna cewa Abigail ba ta daraja matsayin mijinta ne? A’a. Nabal ya riga ya yi abin da bai da kyau ga shafaffen bawan Jehobah, kuma wannan wataƙila zai kai ga mutuwar mutanen da ba su yi laifi ba a gidan Nabal. Da a ce Abigail ba ta ɗauki mataki ba, da wataƙila hakan zai nuna cewa tana goyon bayan mijinta. Ko yaya dai, ya kamata ta yi biyayya ga Allahnta fiye da mijinta.
17, 18. Ta yaya Abigail ta tuntuɓi Dauda, mene ne ta gaya masa kuma me ya sa ya saurari abin da ta ce?
17 Ba da daɗewa ba, Abigail ta haɗu da Dauda da rundunarsa. Ta yi sauri, ta sauko daga jakinta kuma ta durƙusa a gaban Dauda. (1 Sam. 25:20, 23) Sai ta gaya wa Dauda yadda ta ji, kuma ta roƙe shi a madadin maigidanta da kuma iyalinta. Me ya sa Dauda ya saurare ta?
18 Ta ɗauki nauyin laifin da mijinta ya yi kuma ta ce wa Dauda ya yafe mata. Ta yarda cewa mijinta marar hankali ne kamar yadda sunansa yake nufi, wataƙila hakan yana nufin cewa Dauda zai ɓata lokacinsa ne kawai idan ya ce zai yi wa irin wannan mutumin horo. Ta nuna dogararta ga Dauda a matsayin wakilin Jehobah, da sanin cewa “yana yaƙin jihadin Ubangiji.” Ta kuma nuna cewa ta san alkawarin sarauta da Jehobah ya yi wa Dauda, domin ta ce ‘Ubangiji zai sanya ka sarki bisa ga Isra’ila.’ Bugu da ƙari, ta gaya masa cewa kada ya yi abin da zai sa ya ɗauki alhakin jini ko kuma zai zama “abin ladama,” wato lamirinsa ya dame shi. (Karanta 1 Sama’ila 25:24-31.) Waɗannan kalamai ne masu ban sha’awa!
19. Ta yaya Dauda ya aikata ga abin da Abigail ta faɗa, kuma me ya sa ya yabe ta?
19 Mene ne Dauda ya yi? Ya karɓi abubuwan da Abigail ta kawo kuma ya ce: “Mai-albarka ne Ubangiji Allah na Isra’ila, wanda ya aiko ki yau garin ki tarbe ni: mai-albarka ce hikimarki, mai-albarka ce ke kuma da kin hana ni yau daga alhakin jini.” Dauda ya yaba mata don ta yi hanzari ta same shi, kuma ya faɗi cewa ta hana shi ɗaukan alhakin jini. Ya ce mata: “Ki isa gidanki lafiya,” kuma ya daɗa cewa: “Ga shi, na saurari muryarki.”—1 Sam. 25:32-35.
“Ga Baiwarka”
20, 21. (a) Mene ne ya fi ba ka sha’awa ga yadda Abigail ta kasance a shirye ta koma wurin mijinta? (b) Ta yaya Abigail ta nuna gaba gaɗi da kuma basira wajen zaɓan lokacin da za ta yi wa Nabal magana?
20 Babu shakka, bayan sun rabu, Abigail ta yi tunani a kan 1 Sam. 25:36.
abin da ya faru, kuma ta ga bambancin da ke tsakanin amintaccen sarki Dauda da mijinta marar hankali. Amma, ba ta ci gaba da yin wannan tunanin ba. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Sai Abigail ta zo wurin Nabal.” Hakika, ta koma wurin mijinta, kuma ta ci gaba da yin aikace-aikacenta na gida a matsayin matarsa. Tana bukatar ta gaya masa game da kyautar da ta yi wa Dauda da mutanensa domin ya kamata ya sani. Kuma tana bukatar ta gaya masa abin da ya faru, domin kunyar za ta yi yawa idan ya ji hakan daga bakin wani. Amma, ba za ta iya gaya masa yanzu ba. Me ya sa? Domin yana biki kamar sarki kuma ya riga ya bugu sosai.—21 Domin tana da ƙarfin zuciya da kuma hankali, ta dakata har sai gari ya waye, lokacin da giyan ya riga ya sake shi. Zai kasance cikin hankalinsa sosai kuma zai fahimci abin da ta faɗa, amma hakan yana da lahani sosai saboda fushinsa. Duk da haka, ta gaya masa dukan abin da ya faru. Babu shakka, ta yi tsammanin cewa zai yi fushi sosai kuma ya hau ta da faɗa. Maimakon haka, ya zauna shiru, ya kasa yin motsi.—1 Sam. 25:37.
22. Mene ne ya sami Nabal, kuma me hakan ya koya mana game da dukan zalunci ko wulaƙanci da ke faruwa a cikin iyali?
22 Mene ne ya same shi? “Zuciyarsa kuwa ta mutu a cikinsa, ya zama kamar dutse.” Wataƙila ya kamu da cutar shanyewar jiki. Amma bayan kwana goma sai ya mutu, ba sanaddiyar cuta ba, amma domin “Ubangiji ya buga Nabal har ya mutu.” (1 Sam. 25:38) Wannan hukunci na adalci, ya sa Abigail ta huta da matsalar da take samu a aurenta. Ko da yake Jehobah ba ya yin hukunci cikin mu’ujiza a yau, amma wannan labarin ya tuna mana cewa babu zaluncin da ba ya gani. Zai yi hukunci a daidai lokaci.—Karanta Luka 8:17.
23. Wace albarka ce Abigail ta samu, kuma ta yaya ta nuna cewa sabon yanayinta bai sa ta canja ba?
23 Abigail ta samu kwanciyar rai sosai sa’ad da mijinta ya mutu, amma akwai sauran rina a kaba. Sa’ad da Dauda ya samu labari cewa Nabal ya mutu, sai ya aika da saƙo wajen Abigail cewa yana son ya aure ta. Sai ta ce: “Ga baiwarka kuyanga ce ta wanki ƙafafun bayin ubangijina.” Hakika ba ta yi fahariya ba domin Dauda zai aure ta, amma ta ce za ta zama baiwa 1 Sam. 25:39-42.
ga bayinsa! Kuma mun sake karanta cewa ta yi hanzari don ta tafi wajen Dauda.—24. Waɗanne ƙalubale ne Abigail ta fuskanta a sabon yanayinta, amma yaya mijinta da Allah suka ɗauke ta?
24 Hakan ba ya nufin cewa ta daina samun matsala, zaman Abigail tare da Dauda ba zai kasance mai sauƙi a kowane lokaci ba. Dauda ya riga ya auri Ahinoam, kuma ko da yake Allah bai hana auren mata da yawa ba a lokacin, hakan yakan jawo ƙalubale ga mata amintattu. Dauda bai zama sarki ba tukun a lokacin, kuma zai fuskanci matsaloli sosai kafin ya soma bauta wa Jehobah a wannan matsayin. Amma, yayin da Abigail ta taimaka wa Dauda a rayuwarsa, har ta haifa masa ɗa, ta ga cewa ta samu mijin da ya daraja ta kuma yana kāre ta. Akwai lokacin da ya cece ta daga hannun masu sace mutane! (1 Sam. 30:1-19) Da haka, Dauda ya yi koyi da Jehobah Allah, wanda yake ƙauna da kuma daraja irin waɗannan mata masu gaba gaɗi da aminci.
^ sakin layi na 9 Wannan ba sanannen Dutsen Karmel da ke arewancin ƙasar ba ne, inda daga baya, annabi Iliya ya yi jayayya da annabawan Baal. (Duba Babi na 10.) Wannan Karmel wani gari ne da ke gefen jejin da ke kudu.
^ sakin layi na 10 Wataƙila Dauda yana ganin cewa tsare mutanen garin tare da garkensu hidima ce ga Jehobah. A wannan zamanin, nufin Jehobah ne zuriyar Ibrahim da Ishaƙu da Yakubu su zauna a ƙasar. Saboda haka, kāre ta daga ɓarayin da suke shigowa daga ƙasashen waje, hidima ce mai tsarki.
^ sakin layi na 14 Furucin da wannan bawan ya yi amfani da shi yana nufin “ɗan belial (marar amfani).” Wasu juyin Littafi Mai Tsarki sun kwatanta Nabal da “mutumin da ba ya saurarar kowa,” kuma a ƙarshe, “yi masa magana bai da amfani.”