Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA HUƊU

Duk ‘Inda Za Ki Tafi, Nan Za Ni’

Duk ‘Inda Za Ki Tafi, Nan Za Ni’

1, 2. (a) Ka kwatanta tafiya da kuma baƙin cikin da Ruth da Naomi suke yi. (b) Wane bambanci ne ke tsakanin tafiyar da Ruth take yi da kuma ta Naomi?

NAOMI tana kan hanya za ta bar ƙasar Mowab, kuma Ruth tana bin ta sawu da kafa. Su biyu ne kaɗai a wannan babban filin. Ka ɗan yi tunanin yadda Ruth ta ji sa’ad da ta lura cewa dare ya fara yi, sai ta kalli surukarta tana mamaki ko lokaci ya yi da za su nemi masauki. Tana ƙaunar Naomi sosai, kuma za ta yi iya ƙoƙarinta don ta kula da ita.

2 Kowacce cikinsu tana baƙin ciki sosai. Me ya sa? Ko da yake Naomi gwauruwa ce, amma ta fi baƙin ciki yanzu da ’ya’yanta Chilion da Mahlon suka rasu. Ruth kuma tana baƙin ciki domin Mahlon da ya rasu mijinta ne. Ruth da Naomi za su garin Bai’talami da ke ƙasar Isra’ila. Amma, da akwai ɗan bambanci tsakaninsu. Naomi za ta koma ƙasar da aka haife ta. Ruth kuma ta baro danginta da ƙasarta da al’adunta da allolinta, kuma za ta ƙasar da ba ta taɓa sani ba.—Karanta Ruth 1:3-6.

3. Amsoshin waɗanne tambayoyi ne za su taimaka mana mu yi koyi da bangaskiyar Ruth?

3 Mene ne zai sa Ruth ta tsai da irin wannan shawarar farat ɗaya? Mene ne zai taimaka mata ta soma wani salon rayuwa a wata ƙasa, kuma ta kula da Naomi? Amsoshin waɗannan tambayoyin za su taimaka mana mu yi koyi da bangaskiyar Ruth. (Ka kuma duba akwatin nan  “Ƙarami, Amma Yana Ɗauke da Darussa.”) Bari mu soma tattauna abin da ya sa waɗannan mata biyu suka soma tafiya zuwa garin Bai’talami.

An Yi Musu Rasuwa

4, 5. (a) Me ya sa iyalin Naomi suka ƙaura zuwa ƙasar Mowab? (b) Wane ƙalubale ne Naomi ta fuskanta a ƙasar Mowab?

4 Ruth ta yi girma a ƙasar Mowab da ke gabashin Tekun Gishiri. Akwai itatuwa a ƙasar amma suna a ware, kuma akwai kwari masu zurfi. Ana yalwar abinci a “ƙasar Mowab,” har ma sa’ad da ake fari a ƙasar Isra’ila. Fari ne ya sa Ruth ta haɗu da Mahlon da danginsa.—Ruth 1:1.

5 Farin da ake yi a ƙasar Isra’ila ya sa mijin Naomi, Elimelech ya ƙaura da matarsa da ’ya’yansa biyu zuwa ƙasar Mowab. Babu shakka, ƙaurar da suka yi ta shafi imanin kowannensu. Me ya sa? Domin Isra’ilawa suna bukatar su bauta wa Jehobah a kai a kai a wuri mai tsarki da ya keɓe. (K. Sha 16:16, 17) Naomi ta ƙoƙarta don ta ci gaba da bauta wa Jehobah. Duk da haka, ta yi baƙin ciki sa’ad da mai gidanta ya rasu.—Ruth 1:2, 3.

6, 7. (a) Mene ne wataƙila ya sa Naomi baƙin ciki sa’ad da ’ya’yanta suka auri Mowabawa? (b) Me ya sa yadda Naomi ta bi da surukanta abin yabawa ne?

6 Wataƙila Naomi ta sake yin baƙin ciki sa’ad da ’ya’yanta biyu suka auri Mowabawa. (Ruth 1:4) Ta san cewa kakan-kakanninta Ibrahim ya ƙoƙarta sosai don ya samo wa ɗansa Ishaƙu mata daga danginsa masu bauta wa Jehobah. (Far. 24:3, 4) Daga baya, Dokar da Jehobah ya ba Isra’ilawa ta hannun Musa, ta yi musu kashedi cewa kada su ƙyale ’ya’yansu maza ko mata su yi aure daga wata ƙasa, domin hakan zai iya sa su soma bauta wa gumaka.—K. Sha 7:3, 4.

7 Akasin haka, Mahlon da Chilion sun auri Mowabawa. Ba mu san ko hakan ya sa Naomi baƙin ciki ba. Amma ba ta ƙyale hakan ya shafi dangantakarta da Ruth da kuma Orpah ba. Wataƙila, ta sa rai cewa wata rana, su ma za su soma bauta wa Jehobah. Ruth da Orpah suna ƙaunar Naomi sosai. Yadda suka ƙaunaci juna ya taimaka musu sa’ad da bala’i ya auko musu. Mahlon mijin Ruth da Chilion mijin Orpah sun rasu ba su samu ’ya’ya ba.—Ruth 1:5.

8. Mene ne wataƙila ya sa Ruth ta kusaci Jehobah?

8 Shin addinin Ruth ya koya mata abin da za ta yi sa’ad da mijinta ya rasu? Da ƙyar. Me ya sa? Mowabawa suna bauta wa alloli kalla-kalla, kuma Chemosh ne ya fi dukansu girma. (Lit. Lis. 21:29) A zamanin dā, addinai sun halalta cin zalin mutane da kuma ƙona yara. Wataƙila, Mowabawa ma suna yin hakan. Babu shakka, abin da Ruth ta koya daga Mahlon ko Naomi game da Jehobah Allah na Isra’ila mai ƙauna da kuma jin ƙai ne ya shafe ta sosai. Jehobah Allah ne mai ƙauna, ba mai cin zali ba. (Karanta Kubawar Shari’a 6:5.) Wataƙila, bala’in da ya faɗa wa Ruth ya daɗa sa ta kusaci Naomi kuma ta saurare ta yayin da take magana game da Jehobah, Allah maɗaukaki, da ayyukansa masu ban al’ajabi da kuma yadda yake bi da bayinsa cikin ƙauna da jin ƙai.

Ruth ta kusaci Naomi a lokacin baƙin ciki da kuma rashi

9-11. (a) Wace shawara ce Naomi da Ruth da Orpah suka yanke? (b) Waɗanne darussa ne za mu iya koya daga bala’in da ya faɗa musu?

9 Naomi ta ƙosa ta san abin da ke faruwa a ƙasarsu. Wata rana sai ta samu labari, wataƙila daga wani attajiri cewa an daina fari a ƙasar Isra’ila. Jehobah ya sake tunawa da bayinsa. Garin Bai’talami ya sake cika sunansa, wato “Gidan Abinci.” Sai Naomi ta tsai da shawara ta koma gida.—Ruth 1:6.

10 Mene ne Ruth da Orpah za su yi? (Ruth 1:7) Bala’in da ya auko musu ya sa dangantakarsu da Naomi ta yi danƙo sosai. Wataƙila kirkin Naomi da bangaskiyarta ga Jehobah ne suka fi burge Ruth. Su uku sun kama hanya tare, za su ƙasar Yahuda.

11 Labarin Ruth ya koya mana cewa bala’i da rashi suna faɗa wa masu adalci da marasa adalci. (M. Wa. 9:2, 11) Ya kuma koya mana cewa sa’ad da aka yi mana rasuwa, ya kamata mu nemi ta’aziya daga mutane, musamman waɗanda suke dogara ga Jehobah, Allahn Naomi.—Mis. 17:17.

Ruth ta Nuna Ƙauna da Aminci

12, 13. Me ya sa Naomi take son Ruth da Orpah su koma ƙasarsu, kuma mene ne waɗannan matan suka ce?

12 Yayin da suka yi tafiya mai nisa sosai, wani abu ya soma damun Naomi. Ta yi tunanin ’yan mata biyu da ke tare da ita da kuma yadda suka ƙaunace ta da ’ya’yanta. Ba ta son ta daɗa musu wani nauyi kuma. Me za ta yi musu idan sun bi ta zuwa Bai’talami?

13 Daga baya, sai Naomi ta yi magana, ta ce: “Ku tafi, kowace ɗayanku ta koma gidan uwarta: Ubangiji shi nuna muku aikin alheri, kamar yadda kuka nuna wa matattun, da ni kuma.” Ta kuma yi musu fata cewa Jehobah zai sa su sake yin aure. “Sa’an nan ta yi musu sumba: amma suka ta da muryarsu da ƙarfi, suka yi kuka.” Ba abin mamaki ba ne cewa Ruth da Orpah suna ƙaunar wannan mata mai kirki. Sai su biyu suka nace, suka ce: “A’a, mu dai za mu koma tare da ke zuwa wurin mutanenki.”—Ruth 1:8-10.

14, 15. (a) Ga mene ne Orpah ta koma? (b) Mene ne Naomi ta yi don Ruth ta koma gida?

14 Naomi ba ta yarda ba. Ta ce ba abin da za ta iya yi musu a ƙasar Isra’ila. Ba ta da miji da zai tanadar da bukatunsu, ko kuma ’ya’ya da za su aure su. Ta ce hakan yana bala’in ci mata rai sosai. Orpah ta fahimci abin da Naomi take nufi. Danginta suna ƙasar Mowab da mahaifiyarta da kuma gidansu. Ta fahimci cewa ya fi kyau ta kasance a ƙasar Mowab. Cike da baƙin ciki, sai ta yi wa Naomi sumba da ban-kwana kuma ta koma gida.—Ruth 1:11-14.

15 Ruth kuma fa? Abin da Naomi ta faɗa ya shafe ta ma. Amma, Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ruth ta manne mata.” Wataƙila Naomi ta sake soma tafiya, kafin ta lura cewa Ruth ta ƙi komawa gida. Sai ta ce mata: “Duba! surukuwarki ta koma wurin danginta, da kuma allahnta: sai ki koma ki bi surukuwarki.” (Ruth 1:15) Mene ne kalaman Naomi suke nufi? Orpah ba ta koma ga danginta kaɗai ba, amma ga “allahnta.” Ta fi son ta ci gaba da bauta wa Chemosh da kuma wasu alloli. Amma Ruth kuma fa?

16-18. (a) Ta yaya Ruth ta nuna ƙauna da kuma aminci? (b) Wane darasi ne za mu iya koya daga Ruth game da ƙauna da aminci? (Ka kuma duba hotunan matan.)

16 Yayin da Ruth take bin Naomi sawu da kafa, ta san cewa ta yanke shawara mafi kyau. Tana ƙaunar Naomi da kuma Allahnta. Sai Ruth ta ce: “Kada ki roƙe ni in rabu da ke, in kuma bar binki: gama inda za ki tafi duka, nan za ni; inda za ki sauka, nan zan sauka: danginki za su zama dangina, Allahnki kuma Allahna: wurin da kika mutu, nan kuma in mutu, a kuma bizne ni: [Jehobah] ya yi mani hukunci mai zafi, idan ba mutuwa kaɗai ta raba ni da ke.”—Ruth 1:16, 17.

“Danginki za su zama dangina, Allahnki kuma Allahna”

17 Ruth ta furta kalamai masu ban mamaki sosai, waɗanda har bayan shekaru 3,000 da ta rasu, an ci gaba da ambata su. Waɗannan kalamai sun nuna cewa tana da halaye masu kyau, wato aminci da ƙauna. Ruth tana da aminci ga Naomi sosai, kuma tana ƙaunarta da har ta yarda ta je duk inda za ta. Mutuwa ce kaɗai za ta iya raba su. Ta yaya mutanen Naomi za su zama nata? Domin Ruth ta yarda ta yi wa dukan abubuwan da take da su a ƙasar Mowab baya, har da allolinta. Ruth ba ta kamar Orpah. Ta faɗa da dukan zuciyarta cewa tana son ta bauta wa Jehobah, Allahn Naomi. *

18 Sai su biyu kaɗai suka ci gaba da tafiya zuwa Bai’talami. Wani bincike da aka yi ya nuna cewa wataƙila tafiyar ta kai mako ɗaya. Babu shakka, sun ƙarfafa juna duk da yake suna makoki.

19. Ta yaya za mu iya yin koyi da ƙauna da amincin Ruth (a) a cikin iyali (b) ikilisiya, (c) ga abokanmu?

19 Mutane da yawa suna baƙin ciki a yau. A wannan ‘miyagun zamanun’ da muke ciki, muna fuskantar rashi da makoki iri-iri. (2 Tim. 3:1) Saboda haka, halin Ruth ya fi muhimmanci yanzu. Idan mutum yana da ƙauna da kuma aminci, zai manne wa wani sawu da kafa. Kuma wannan hali ne mai kyau a wannan muguwar duniya. Muna bukatar wannan halin a aure da kuma cikin iyali. Muna kuma bukatar mu nuna wannan halin ga abokanmu da kuma a cikin ikilisiyar Kirista. (Karanta 1 Yohanna 4:7, 8, 20.) Idan muka kasance da wannan halin, hakan zai nuna cewa muna yin koyi da misalin Ruth.

Ruth da Naomi a Bai’talami

20-22. (a) Ta yaya zaman da Naomi ta yi a ƙasar Mowab ya shafe ta? (b) Wane ra’ayi da bai dace ba ne Naomi take da shi game da wahalar da take sha? (Ka kuma duba Yaƙub 1:13.)

20 Mutum zai iya ciccika baki cewa yana da ƙauna da kuma aminci, amma gani ya kori ji. Ruth tana da zarafin nuna cewa tana da aminci da kuma ƙauna ga Naomi da kuma Jehobah, Allahn da take son ta bauta wa.

21 Bayan tafiya mai nisa, sai suka isa Bai’talami, wani gari da ke kusan mil shida daga kudancin Urushalima. Wataƙila a dā, Naomi da danginta sanannu ne sosai a garin. Me ya sa muka kammala hakan? Domin labari ya bazu ko’ina cewa ta dawo. Matan ƙauyen suna cewa, “Wannan Naomi ce?” Babu shakka, zama a ƙasar Mowab ya shafi surarta sosai. Yanayin jikinta ya nuna cewa ta sha wahala sosai, kuma ta yi makoki.—Ruth 1:19.

22 Naomi ta bayyana wa danginta da maƙwabtanta abin da ya sa take baƙin ciki. Ta ma ce a bar kiranta Naomi, wato “Abin Sha’awa.” Amma, a riƙa kiranta Mara, wato “Ɗaci.” Abin tausayi! Naomi tana da irin ra’ayin Ayuba, domin tana ganin cewa Jehobah ne ya haddasa mata wahala.—Ruth 1:20, 21; Ayu. 2:10; 13:24-26.

23. Mene ne Ruth ta soma tunani a kai, kuma wace Doka ce Allah ya ba da game da talakawa? (Ka kuma duba hasiya.)

23 Bayan sun sauka a Bai’talami, sai Ruth ta soma tunanin yadda za ta kula da kanta da kuma Naomi. Ta samu labari cewa Jehobah ya ba Isra’ilawa, wata Doka mai kyau da ta shafi talakawa. Dokar ta ba talakawa izinin yin kala a lokacin girbi. *Lev. 19:9, 10; K. Sha 24:19-21.

24, 25. Mene ne Ruth ta yi sa’ad da ta samu zarafin yin kala a gonar Boaz, kuma yaya ake yin kala a lokacin?

24 A lokacin da ake girbin sha’ir, ƙila a watan Afrilu, Ruth ta bi gona-gona don ta nemi inda za ta yi kala. Sai ta samu zarafin yin kala a gonar wani mutum mai suna Boaz. Shi mawadaci ne, yana da filaye kuma dangin mijin Naomi ne da ya rasu. Ko da yake Dokar ta ba ta izinin yin kala, amma ta daraja Dokar. Ta nemi izinin yin kala daga shugaban ’yan ƙodagon. Sai ya yarda, kuma ta soma aiki ba tare da ɓata lokaci ba.—Ruth 1:22–2:3, 7.

25 Ka yi tunanin yadda Ruth take bin masu girbin a baya. Yayin da suke yanka sha’ir da lauje, sai ta ɗurkusa ta tsinci wanda ya faɗa a ƙasa ko wanda ba su yanka ba. Bayan haka, sai ta tattara su ta kai inda za ta buga su kuma ta cire hatsin. Aiki ne mai wuya, kuma yana daɗa wuya sa’ad da rana ta fito. Duk da haka, Ruth ta ci gaba da yin aikin. Tana dakatawa kawai don ta share zufa daga fuskarta, kuma ta ɗan ci abinci a cikin “gida.” Wataƙila, rumfa ce da aka gina don ’yan ƙodago su riƙa zama.

Ruth ta yi aiki tuƙuru don ta kula da kanta da kuma Naomi

26, 27. Wane irin mutum ne Boaz, kuma yaya ya bi da Ruth?

26 Wataƙila, Ruth ba ta sa rai cewa kowa zai lura da ita ba. Amma, akwai wani da ya lura da ita. Ka san ko wane ne? Boaz ne, kuma ya tambayi shugaban ’yan ƙodagonsa ko wace ce ita. Boaz mutum ne mai imani sosai. Sai ya gai da ’yan ƙodagon, wasu suna aikin yini ne, wasu kuma baƙi ne. Ya ce musu: “Ubangiji shi zauna tare da ku.” Sai su ma suka ce masa, “Ubangiji shi albarkace ka.” Wannan dattijon da ke tsoron Allah ya kula da Ruth kamar uba.—Ruth 2:4-7.

27 Boaz ya kira ta “ɗiyata,” ya ce ta riƙa zuwa gonarsa kala, kuma ta riƙa bin ’yan matan da suke masa aiki don kada wani ya wulaƙanta ta. Ya ce a riƙa ba ta abincin rana. (Karanta Ruth 2:8, 9, 14.) Bugu da ƙari, ya yaba mata kuma ya ƙarfafa ta. Ta yaya ya yi hakan?

28, 29. (a) Wane irin suna ne Ruth ta yi? (b) Ta yaya za ka sa Jehobah ya zama mafakarka kamar Ruth?

28 Sa’ad da Ruth ta tambayi Boaz abin da ta yi da ya sa yake nuna mata tagomashi duk da yake ita baƙuwa ce, sai ya ce ya ji dukan alherin da ta yi wa surukarta, Naomi. Wataƙila, Naomi ta yaba mata a gaba matan Bai’talami, kuma Boaz ma ya samu labari. Ya kuma san cewa ta soma bauta wa Jehobah, gama ya ce: “[Jehobah] ya sāka miki aikinki, ki karɓi cikakkiyar lada daga wurin [Jehobah], Allah na Isra’ila, wanda kika zo neman mafaka ƙarƙashin fukafukansa.”—Ruth 2:12.

29 Babu shakka, waɗannan kalmomin sun ƙarfafa Ruth! Ta yanke shawara ta nemi mafaka ƙarƙashin fukafukan Jehobah, kamar yadda ’yar tsako take fakewa a ƙarƙashin fukafukan mamarta. Ta yi wa Boaz godiya don yadda ya ƙarfafa ta. Sai ta ci gaba da yin aiki har yamma.—Ruth 2:13, 17.

30, 31. Mene ne za mu iya koya daga Ruth game da aiki da hamdala da aminci da kuma ƙauna?

30 Misalin Ruth darasi ne sosai ga dukan mu a yau, yayin da muke gwagwarmaya da gurgujewar tattalin arziki. Ruth ba ta yi zaman kashe wando ba, tana sa rai cewa wani zai kula da ita domin ita gwauruwa ce. Ta daraja dukan abin da aka ba ta. Ba ta ji kunyar yin aiki tuƙuru don ta kula da Naomi ba, ko da yake ba irin aikin da kowa yake sha’awar yi ba ne. Ta koya yadda ake aiki ba tare da kasada ba. Mafi muhimmanci, ba ta manta da ainihin mafakarta ba, wato Jehobah.

31 Ya kamata mu kasance da aminci da ƙauna da tawali’u, kuma mu riƙa aiki tuƙuru kamar Ruth. Kuma zai dace mu yi hamdala don Jehobah ya sa mun san shi. Idan muka yi haka, bangaskiyarmu za ta zama abin koyi ga wasu. Amma, yaya Jehobah ya tanadar wa Ruth da Naomi bukatunsu? Za mu tattauna wannan tambayar a babi na gaba.

^ sakin layi na 17 Ruth ba ta yi amfani da laƙabin nan “Allah” yadda baƙi da yawa suke yi ba. Ta yi amfani da ainihin sunan Allah, wato Jehobah. Wani juyin Littafi Mai Tsarki ya ce: “Marubucin ya nuna cewa wannan baƙuwar baiwar Allah na gaskiya ce.”

^ sakin layi na 23 Wannan doka ce mai kyau sosai, kuma wataƙila babu irin ta a ƙasar Mowab. Ba a kula da gwauraye sosai a Gabas ta Tsakiya a zamanin dā. Wani littafi ya ce: “Bayan mace ta rasa mijinta, ’ya’yanta ne suke kula da ita. Amma idan ba ta da ’ya’ya, za ta iya zama baiwa ko ta yi karuwanci ko kuma ta mutu.”