BABI NA GOMA SHA SHIDA
Ta Nuna Hikima da Gaba Gaɗi da Kuma Sadaukarwa
1-3. (a) Mene ne Esther take bukatar ta yi kafin ta je karagar mijinta? (b) Mene ne sarki ya yi sa’ad da ya ga Esther?
GABAN ESTHER yana faɗuwa yayin da take takawa a hankali zuwa inda karagar sarki take. Ka yi tunanin yadda ko’ina ya yi shuru kuma kowa ya yi tsit a fādar sarkin Farisa da ke Shushan. Abin da Esther za ta iya ji kawai shi ne takunta da kuma ƙarar rigarta. Yanzu ba lokacin da za ta mai da hankali ga kyau da kuma armashin fādar da aka yi da katakai masu kyau daga ƙasar Lebanon ba ne. Ta mai da hankali ga mutumin da yake zama a kan karagar. Me ya sa? Domin ranta yana hannunsa.
2 Sarkin ma ya zuba wa Esther ido yayin da take matsowa kusa, kuma ya miƙa kandirinsa. Ta wajen yin hakan, sarkin ya nuna cewa ya yafe mata, domin ta shiga fādar ba tare da ya gayyace ta ba. Sa’ad da ta iso karagar, sai ta miƙa hannunta don ta taɓa kan kandirin.—Esther 5:1, 2.
3 A bayyane yake cewa Sarki Ahasuerus yana da iko da kuma wadata. Alkyabbar da sarakunan Farisa suke yafawa a zamanin kusan dalla biliyan ce. Duk da haka, Esther ta ga cewa mijinta yana ƙaunarta. Ya ce: “Me ki ke so, ya sarauniya Esther? Mene ne kuwa roƙonki? Za a ba ki har sashin mulkin.”—Esther 5:3.
4. Wane ƙalubale ne ke gaban Esther?
4 Esther ta nuna cewa tana da bangaskiya da kuma gaba gaɗi. Ta je wurin sarki don ta kāre mutanenta daga kisan ƙare-dangi da wani ya ƙulla musu. Kamar dai ta soma yin nasara domin sarki ya amince da zuwanta, amma tsugune ba ta ƙare ba. Tana bukatar ta sa wannan sarki mai alfahari ya fahimci cewa wani mashawarcinsa da kuma amininsa mugu ne kuma ya ruɗe shi ya sa hannu don a kashe dukan mutanenta. Ta yaya za ta rinjaye shi? Kuma ta yaya za mu iya yin koyi da bangaskiyarta?
Ta Yi Magana a Lokacin da Ya Dace
5, 6. (a) Ta yaya Esther ta bi ƙa’idar da ke cikin littafin Mai-Wa’azi 3:1, 7? (b) Ta yaya Esther ta nuna hikima a yadda ta yi magana da maigidanta?
5 Shin ya kamata Esther ta faɗi matsalarta a gaban dukan fadawan ne? A’a. Yin hakan zai kunyatar da sarkin kuma zai ba Haman damar kāre kansa. Mene ne Esther ta yi? Sulemanu, Sarki mai hikima ya rubuta shekaru da yawa da suka shige cewa: “Ga kowane niyya akwai nasa kwanaki, . . . akwai lokacin shuru da lokacin magana.” (M. Wa. 3:1, 7) Za mu iya yin tunanin yadda Mordekai wanda ya raine ta yake koya mata irin waɗannan ƙa’idodin yayin da take girma. Esther ta fahimci cewa yana da muhimmanci ta yi magana a lokacin da ya dace.
6 Esther ta ce: “Idan sarki ya ga ya yi kyau, bari sarki da Haman su zo yau wurin biki da na shirya masa.” (Esther 5:4) Sarki ya yarda kuma ya sa aka kira Haman. Shin ka lura da yadda Esther ta yi magana da hikima kuwa? Ta daraja maigidanta kuma ta shirya ta gaya masa matsalarta a lokaci da kuma wurin da ya dace.—Karanta Misalai 10:19.
7, 8. Yaya liyafa ta farko da Esther ta shirya ta kasance, amma me ya sa ta yi jinkirin gaya wa sarki matsalarta?
7 Babu shakka, Esther ta shirya wannan liyafar da kyau kuma ta tabbatar cewa ta shirya dukan abubuwan da maigidanta yake so. Ta shirya ruwan inabi domin kowa ya sha ya yi farin ciki. (Zab. 104:15) Ahasuerus ya shaƙata sosai, kuma ya sake tambayar Esther ta gaya masa abin da take so. Shin yanzu ne lokacin da ya dace ta yi magana?
8 Esther ba ta ji hakan ba, amma washegari ta sake gayyatar sarki da kuma Haman zuwa wata liyafa. (Esther 5:7, 8) Me ya sa? Ka tuna cewa Haman ya riga ya karɓi izini daga sarki don a halaka dukan Yahudawa. Saboda haka, wajibi ne Esther ta zaɓi lokacin da ya fi dacewa. Shi ya sa ta yi haƙuri kuma ta jira har sai ta sami damar nuna wa maigidanta daraja da kuma girma.
9. Me ya sa haƙuri hali ne mai kyau, kuma ta yaya za mu iya yin koyi da Esther?
Misalai 25:15 ya ce: “Da tsawon jimrewa a kan rinjayi mahukunci, harshe mai-taushi kuma ya kan karye kashi.” Idan muka yi haƙuri don mu yi magana a lokacin da ya dace kuma ba a garaje ba, za mu iya rinjayar wanda ba ya son ya saurare mu. Shin Jehobah, Allahn Esther ya albarkace ta don ta yi haƙuri kuma ta kasance da hikima kuwa?
9 Haƙuri hali ne mai kyau sosai, amma mutane ƙalilan ne suke da shi. Ko da yake matsalar tana ci mata tuwo a ƙwarya, Esther ta jira har sai ta sami lokacin da ya fi dacewa ta yi magana. Za mu iya yin koyi da ita. Me ya sa? Domin a wasu lokatai, za mu iya ganin wani abin da bai dace ba yana faruwa. Idan muna so mu tuntuɓi wanda zai iya daidaita yanayin, ya kamata mu yi haƙuri kamar Esther. LittafinSakamakon Haƙuri
10, 11. Me ya sa Haman ya yi fushi bayan ya gama liyafa ta farkon, kuma mene ne matarsa da kuma abokansa suka ce ya yi?
10 Abubuwa da yawa sun faru domin Esther ta yi haƙuri. Haman ya gama liyafa ta farko “da farinciki da murna,” domin yana ganin cewa ya fi sauran hakiman tagomashi a gaban sarki da kuma sarauniyarsa. Amma sa’ad da ya isa ƙofar birnin, wani abu ya ɓata masa rai. Ya hangi Mordekai, Bayahuden nan da ya ƙi ya rusuna masa. Kamar yadda muka koya a babin da ya gabata, ba domin Mordekai ba ya daraja Haman ba ne ya sa ya ƙi rusuna masa ba, amma domin ba ya son ya ɓata dangantakarsa da Jehobah da kuma lamirinsa. Hakan ya sa Haman “ya cika da fushi.”—Esther 5:9.
11 Sa’ad da Haman ya gaya wa matarsa da kuma abokansa abin da Mordekai ya yi, sai suka ce ya shirya babban gungume mai tsawon kafa fiye da 72 kuma ya nemi izinin sarki don a rataye Mordekai a kai. Haman ya amince da wannan shawarar kuma ya umurci wani ya soma kafa gungumen.—Esther 5:12-14.
12. Me ya sa sarki ya sa aka karanta masa littafin tarihin sarakuna, kuma mene ne ya gano?
12 Sarki Ahasuerus kuma bai ji daɗin barcinsa ba. Littafi Mai Tsarki ya ce “sarki ya kāsa barci,” sai ya sa aka karanta masa littafin da aka rubuta tarihin sarakuna. Tarihin ya ƙunshi labarin wata maƙarƙashiya da aka ƙulla don a kashe Ahasuerus. Sai ya tuna cewa an kama waɗanda suka yi ƙullin kuma an kashe su. Amma mutumin da ya fallasa su kuma fa? Sai farat ɗaya, sarki ya yi tambaya ko an saka wa mutumin nan, wato Mordekai. Amsar ita ce, ba a saka masa ba.—Karanta Esther 6:1-3.
13, 14. (a) Ta yaya yanayin Haman ya soma muni? (b) Mene ne matar Haman da kuma abokansa suka gaya masa?
13 Cike da alhini, sarkin ya sa a kira hakimansa don a gyara wannan kuskuren. Haman ne aka samu a fādar. Wataƙila ya yi sammako ya zo neman izinin sarki don a rataye Mordekai. Amma kafin Haman ya yi roƙonsa, sarki ya nemi ra’ayinsa a kan yadda ya kamata a saka wa mutumin da ya sami tagomashin sarki. Haman ya ɗauka cewa shi ne mutumin da sarki yake magana a kai. Sai Haman ya ƙaga wata hanya mai kyau da ya kamata a daraja mutumin. Ya ce a yafa wa mutumin alkyabba mai kyau, kuma a sa babban hakimi ya zagaya da shi a kan dokin sarki yana kirari da sunansa. Ka yi tunanin yadda Esther 6:4-10.
Haman ya ɓata rai sa’ad da ya ji cewa Mordekai ne mutumin! Shin wane ne zai zagaya Mordekai kuma ya yi kirari da sunansa? Haman ne!—14 Haman ya yi hakan da fushi da kuma ƙyama sosai kuma bayan haka, ya koma gida nan da nan. Matarsa da kuma abokansa sun gaya masa cewa abin da ya faru alama ce cewa reshe ya kusan juye da mujiya.—Esther 6:12, 13.
15. (a) Mene ne sakamakon haƙurin da Esther ta yi? (b) Me ya sa ya dace mu riƙa yin haƙuri?
15 Esther ta sami sakamako mai kyau don haƙurin da ta yi na kwana ɗaya kafin ta gaya wa sarki matsalarta. Hakan ya ba Haman zarafin tona kabarinsa. Wataƙila Jehobah ne ya sa sarkin ya kasa barci. (Mis. 21:1) Shi ya sa Kalmar Allah ta ƙarfafa mu mu riƙa yin haƙuri! (Karanta Mikah 7:7.) Idan muka dogara ga Allah kuma muka kasance da haƙuri, zai magance matsalolinmu a hanyar da ta fi dacewa.
Ta Yi Magana da Gaba Gaɗi
16, 17. (a) A wane lokaci ne Esther ta sami zarafin yin magana? (b) Yaya Esther ta yi dabam da Vashti?
16 A yanzu, Esther ba ta bukatar ta yi wani jinkiri kuma. Wajibi ne ta gaya wa sarki matsalarta a liyafa ta biyu. Amma, za ta sami zarafin yin hakan a wannan liyafar kuwa? Hakika, sarkin ya ba ta zarafi ta faɗi matsalarta. (Esther 7:2) Yanzu ne lokacin da ya dace ta yi magana.
17 Muna iya tunanin yadda Esther ta yi addu’a a zuciyarta kafin ta ce wa sarki: “Idan na sami tagomashi a gabanka, ya Esther 7:3) Ka lura cewa ta tabbatar wa sarki cewa ta daraja ra’ayinsa. Esther ta yi dabam da Vashti, matar da sarki ya yi wa saki don ta yi masa rashin kunya. (Esther 1:10-12) Esther ba ta yi wa sarki sūka don ya yi wauta wajen amince da Haman ba. Maimakon haka, ta roƙi sarki ya kāre ta.
sarki, idan kuma ya gami sarki, a ba ni raina bisa ga roƙona, al’ummata kuma bisa ga biɗata.” (18. Ta yaya Esther ta gaya wa sarki matsalar da take ciki?
18 Babu shakka, wannan roƙon ya sa sarki mamaki kuma ya ratsa zuciyarsa. Wa ya isa ya yi wa sarauniyarsa barazana? Esther ta ci gaba da cewa: “An sayar da mu, ni da al’ummata, an sayar da mu domin a hallaka mu, a karkashe mu, mu lalace. Amma da a ce an sayar da mu domin mu zama bayi maza da mata, da na yi shuru, gama ƙuncinmu ba ya tsananta har da za a gwada shi da hasarar sarki ba.” (Esther 7:4) Esther ta ambata matsalar da suke ciki kuma ta ce da a ce an yi barazanar kai su bauta ne, da ta yi shuru. Amma ko sarki ma ba zai ji daɗi ba idan bai samu labarin wannan maƙarƙashiyar ba.
19. Mene ne za mu koya daga Esther game da yin magana da rinjaya?
19 Esther ta kafa mana misali mai kyau na yin magana da rinjaya. Sa’ad da kake so ka gaya wa wani ko kuma hukuma game da wata babbar matsala, kana bukatar ka yi haƙuri, ka nuna daraja kuma ka faɗi gaskiya.—Mis. 16:21, 23.
20, 21. (a) Ta yaya Esther ta fallasa Haman, kuma mene ne sarki ya yi? (b) Mene ne Haman ya yi sa’ad da aka fallasa shi?
20 Sai Ahasuerus ya yi tambaya: “Wane ne shi, ina shi ke Esther 7:5-7.
kuma, wanda ya yi ƙarfin hali a cikin zuciyarsa shi yi wannan?” Ka kwatanta a zuci yadda Esther ta nuna mutumin da yatsa kuma ta ce: “Magabci ne da abokin gāba, shi wannan mugun Haman.” Sai Haman ya cika da tsoro. Ka yi tunanin yadda idanun sarkin suka yi ja wur sa’ad da ya gano cewa amininsa ya yaudare shi kuma ya hatimce kisan matarsa ƙaunatacciya. Sai sarkin ya fusata kuma ya je ya zauna a lambun da ke fādar don ya ɗan huce.—21 Sa’ad da Haman ya ga cewa an fallasa shi, sai ya durƙusa a gaban sarauniyar. Sarki ya dawo kuma ya tarar da Haman kusa da kujerar Esther sa’ad da yake neman ahuwa, sai ya yi masa zargin son yi wa matarsa fyaɗe a cikin gidansa. Wannan zargin hukuncin kisa ne. Yayin da aka rufe fuskarsa kuma ake fitar da shi, sai wani hakimi ya sanar da sarki cewa Haman ya sa an kafa wani gungume don a rataye Mordekai a kai. Nan da nan Ahasuerus ya umurta a rataye Haman a kan gungumen.—Esther 7:8-10.
22. Ta yaya misalin Esther zai taimaka mana mu kawar da shakka da kuma rashin bangaskiya?
22 A wannan duniyar da rashin adalci ya zama ruwan dare, za mu iya ji cewa ba zai yiwu a yi adalci ba. Shin ka taɓa jin haka kuwa? Esther ba ta yi shakka ko fid da rai ko kuma rashin bangaskiya ba. Ta yi magana da gaba gaɗi a lokacin da ya dace kuma ta kasance da tabbaci cewa Jehobah zai yi abin da ya dace. Ya kamata mu yi koyi da ita. Jehobah bai canja ba. Har ila, zai iya sa miyagu su faɗa cikin ramin mugunta da suka tona kamar yadda ya yi da Haman.—Karanta Zabura 7:11-16.
Ta Yi Sadaukarwa don Allah da Bayinsa
23. (a) Ta yaya sarki ya saka wa Mordekai da Esther? (b) Ta yaya annabcin da Yakubu ya yi sa’ad da ya kusan mutuwa game da Banyamin ya cika? (Ka duba akwatin nan “Annabcin da Ya Cika.”)
23 A ƙarshe, sarki ya fahimci cewa Mordekai ne ya kāre shi daga ƙullin kisa da aka yi masa kuma shi ne ya raini Esther. Ahasuerus ya ba Mordekai matsayin Haman a dā, wato firayim Esther 8:1, 2.
minista. Ya kuma ba Esther gidan Haman da dukan dukiyarsa. Esther kuma ta bar su a hannun Mordekai.—24, 25. (a) Mene ne Esther ta yi bayan ta fallasa maƙarƙashiyar Haman? (b) Ta yaya Esther ta sake sa ranta cikin haɗari?
24 Shin Esther za ta huta ne da yake ta ceci kanta da kuma Mordekai? A’a. Esther ba ta nuna son kai ba. A wannan lokacin, an kusan idar da saƙon hukunci da Haman ya zartar a kan Yahudawa a daular baki ɗaya. Haman ya jefa ƙuri’a ko kuma wani irin sihiri da ake kira Pur don ya san lokacin da ya fi dacewa ya aiwatar da maƙarƙashiyarsa. (Esther 9:24-26) Da sauran watanni kafin ranar ta kai, amma hannun agogo yana tafiya. Za a iya kawar da wannan masifar kuwa?
25 Esther ta sake sa ranta cikin haɗari ta wajen zuwa wurin sarki ba tare da gayyata ba. A wannan karon ta roƙi mijinta har da kuka don ya janye wannan mugun hukuncin. Amma, ba zai yiwu a janye doka da aka kafa da sunan sarkin Farisa ba. (Dan. 6:12, 15) Saboda haka, sarkin ya ba Esther da Mordekai izinin kafa wata doka. Dokar ta ba Yahudawa ikon kāre kansu kuma mahaya suka hanzarta wajen yin shelar wannan albishirin ga Yahudawa a kowane gefen ƙasar. Yahudawa sun sake kasancewa da bege. (Esther 8:3-16) Za mu iya yin tunanin yadda Yahuduwa da ke Farisa suke shirin yaƙi. Amma, hakan ya yiwu ne domin sabuwar doka da aka kafa. Shin Jehobah “mai-runduna” zai taimaka wa mutanensa a yaƙin kuwa?—1 Sam. 17:45.
26, 27. (a) Shin Jehobah ya sa bayinsa su yi nasara kuwa? Ka bayyana. (b) Wane annabci ne ya cika sa’ad da aka halaka ’ya’yan Haman?
26 A ƙarshe, ranar ta kai kuma bayin Allah suna a shirye. Hakiman Farisa da yawa sun kāre bayin Allah domin sun sami labari cewa Mordekai ne sabon firayim minista kuma shi Bayahude ne. Jehobah ya sa mutanensa sun yi nasara sosai a kan magabtansu domin kada su sake yi musu lahani. *—Esther 9:1-6.
27 Ƙari ga haka, an halaka ’ya’yan Haman guda goma domin gidansa ya zama na Mordekai. (Esther 9:7-10) Hakan ya sa annabcin da Allah ya yi cewa za a halaka Amalakawa da suka zama miyagun magabtan mutanensa ya cika. (K. Sha 25:17-19) Wataƙila, ’ya’yan Haman ne mutane na ƙarshe a wannan al’ummar da aka la’anta.
28, 29. (a) Me ya sa Jehobah ya sa Esther da mutanenta su yi yaƙi? (b) Ta yaya Esther ta kafa mana misali mai kyau?
28 Esther ta ɗauki nawaya sosai, duk da cewa ita mace ce. Yin hakan bai da sauƙi, amma ba ta yi jinkiri ba domin ta san cewa nufin Jehobah ne a kāre mutanensa. Me ya sa? Domin daga wannan al’ummar ne za a sami Almasihu, wanda zai ceci ’yan Adam. (Far. 22:18) Bayin Allah a yau suna farin cikin sanin cewa sa’ad da Yesu ya zo duniya, ya hana mabiyansa yin yaƙi.—Mat. 26:52.
29 Amma, akwai wani irin yaƙi da Kiristoci suke yi domin Shaiɗan ya duƙufa ya sa su daina kasancewa da bangaskiya ga Jehobah. (Karanta 2 Korintiyawa 10:3, 4.) Hakika, Esther ta kafa mana misali mai kyau! Bari mu yi koyi da bangaskiyarta ta wajen yin haƙuri da hikima sa’ad da muke son mu rinjayi mutum. Bari mu kuma nuna gaba gaɗi da sadaukarwa ta wajen kāre bayin Allah.
^ sakin layi na 26 Sarkin ya daɗa wa Yahudawa rana ɗaya don su gamar da magabtansu. (Esther 9:12-14) Har yau, Yahudawa sukan yi biki a kowane watan Adar da ya yi daidai da ƙarshen watan Fabrairu zuwa farkon watan Maris, don su tuna da nasarar da suka yi. Ana kiran bikin Purim wato jam’in Pur da ke nufin ƙuri’ar da Haman ya jefa don ya halaka Isra’ilawa.