Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

RATAYE

A Watan Disamba ne Aka Haifi Yesu?

A Watan Disamba ne Aka Haifi Yesu?

LITTAFI MAI TSARKI bai gaya mana watan da aka haifi Yesu ba. Amma ya ba mu kyawawan dalilai da za su sa mu tabbata cewa ba a haife shi a watan Disamba ba.

Ka lura da yanayi a Bai’talahmi a lokacin da aka haifi Yesu. Watan Chislev na Yahudawa (ya yi daidai da watannin Nuwamba/Disamba) wata ne da ake yin sanyi da ruwan sama. Watan da yake bin bayan wannan shi ne watan Tebeth (Disamba/Janairu). Wannan ne lokaci mafi sanyi a shekara, lokaci ne na dusar ƙanƙara a kan duwatsu. Bari mu bincika abin da Littafi Mai Tsarki ya gaya mana game da yanayi a lokacin.

Marubucin Littafi Mai Tsarki Ezra ya nuna cewa wannan watan Chislev wata ne na sanyi da ruwan sama. Bayan ya ce jama’a ta taru a Urushalima “wata [Chislev] na tara ke nan, kan rana ta ashirin ga wata,” Ezra ya faɗi cewa mutane suna “rawan jiki. . .saboda ruwan sama mai-yawa.” Game da yanayi a wannan lokaci na shekara, mutane da suka taru da kansu suka ce: “Lokacin ruwa mai-yawa ne kuwa, ba mu iya tsaya a waje.” (Ezra 10:9, 13; Irmiya 36:22) Babu mamaki da makiyaya na wannan ɓangaren duniya suke rufe garkensu cikin ɗaki a watan Disamba!

Amma, Littafi Mai Tsarki ya ce, makiyaya suna waje suna kula da dabbobinsu a daren da aka haifi Yesu. Hakika, kamar yadda marubucin Littafi Mai Tsarki Luka ya nuna, “makiyaya . . . suna kwana a fili kuwa, suna tsaron garkensu da dare” a kusa da Bai’talahmi. (Luka 2:8-12) Ka lura cewa makiyaya suna kwana a fili, ba kawai suna fita yawo ba da rana. Suna tare da dabbobinsu a fili cikin dare. Shin kwatancin kwana a waje ya yi daidai da yanayi na sanyi da ruwa na Bai’talahmi a watan Disamba? Ko kaɗan. Saboda haka, yanayi a lokacin haihuwar Yesu ya nuna cewa ba a haife shi a watan Disamba ba. *

Kalmar Allah ta gaya mana daidai lokacin da Yesu ya mutu, amma bai ba da cikakken bayani ba game da lokacin da aka haife shi. Wannan ya tuna mana kalmomin Sarki Sulemanu: “Nagarin suna ya fi mai mai-tamani; kuma ranar mutuwa ta fi ranar haifuwa.” (Mai-Wa’azi 7:1) Saboda haka, ba abin mamaki ba ne da Littafi Mai Tsarki ya ba da cikakken bayani game da hidima da kuma mutuwar Yesu amma ya ba da ɗan bayani kawai game da lokacin haihuwarsa.

Sa’ad da aka haifi Yesu, makiyaya da kuma dabbobinsu suna fili cikin dare.

^ sakin layi na 1 Domin ƙarin bayani, ka dubi shafuffuka na 176-179 na littafin nan Reasoning From the Scriptures, Shaidun Jehobah ne suka wallafa.