Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

RATAYE

Menene Sheol da kuma Hades?

Menene Sheol da kuma Hades?

A HARSUNANSA na asali, Littafi Mai Tsarki ya yi amfani da kalmar Ibrananci sheʼohlʹ da kuma ta Helenanci haiʹdes fiye da sau 70. Dukansu suna da alaƙa da mutuwa. Wasu masu fassara sun fassara su “kabari,” “jahannama,” ko kuma “rami.” Amma, a yawancin harsuna babu kalmomi da suka yi daidai da waɗannan kalmomin Ibrananci da Helenanci. Saboda haka, Litafi Mai-Tsarki ya yi amfani da kalmar nan “Hades.” Menene waɗannan kalmomi ainihi suke nufi? Bari mu lura da yadda aka yi amfani da su a wurare dabam dabam a cikin Littafi Mai Tsarki.

Mai-Wa’azi 9:19 ta ce: “Babu wani aiki, ko dabara, ko ilimi, ko hikima, cikin kabari inda za ka.” Wannan yana nufi ne cewa Sheol yana nufin kabari takamaimai na wani mamaci, ko kuma makabarta da muka binne wani da muke ƙauna? A’a. Sa’ad da Littafi Mai Tsarki yake magana game da wurin da aka binne mutum, ko kuma kabarin mutum, yana amfani da wasu kalmomi na Ibrananci ko Helenanci, ba sheʼohlʹ and haiʹdes ba. (Farawa 23:7-9; Matta 28:1) Kuma Littafi Mai Tsarki bai yi amfani da “Sheol” ga kabari da aka binne mutane da yawa ba, irin su kabarin iyali ko kuma kabari ɗaya da aka binne mutane da yawa a ciki.—Farawa 49:30, 31.

Wane irin wuri ne “Sheol” yake nufi? Kalmar Allah ta nuna cewa “Sheol,” ko “Hades,” yana nufin abu ne da ya fi babban kabari girma. Alal misali, Ishaya 5:14 ta ce Sheol ya ‘faɗaɗa gurinsa, ya wāge bakinsa gaba da misali.’ Ko da yake Sheol ya riga ya haɗiye matattun mutane marasa iyaka, kamar dai a kullum yana bukatar ƙari. (Misalai 30:15, 16) Ba kamar wuri na zahiri da ake binne mutane ba, da zai iya ɗaukan iyakar adadinsa, “[Sheol] da hallaka ba su ƙoshi ba daɗai.” (Misalai 27:20) Sheol ba ya cika. Ba shi da iyaka. Saboda haka, Sheol, ko Hades ba wuri ba ne na zahiri. Maimakon haka, kabari ne na dukan ’yan adam, wuri na alama da yawancin ’yan adam suke barci cikin mutuwa.

Koyarwar Littafi Mai Tsarki ta tashin matattu ta taimaka mana mu sami ƙarin haske game da ma’anar “Sheol” da “Hades.” Kalmar Allah ta nuna nasaba da ke tsakanin Sheol da Hades da kuma irin mutuwar da za a sami tashin matattu. * (Ayuba 14:13; Ayukan Manzanni 2:31; Ru’ya ta Yohanna 20:13) Kalmar Allah ta nuna cewa waɗanda suke Sheol, ko Hades, sun haɗa da waɗanda suka bauta wa Jehobah da kuma waɗanda ba su bauta masa ba. (Farawa 37:35; Zabura 55:15) Saboda haka, Littafi Mai Tsarki ya koyar da cewa za a “yi tashin matattu, masu-adalci da na marasa-adalci.”—Ayukan Manzanni 24:15.

^ sakin layi na 1 Akasarin haka, matattu da ba za a tashe su ba an kwatanta cewa suna cikin “Jahannama” ba cikin Sheol, ko kuma Hades ba. (Matta 5:30; 10:28; 23:33) Kamar Sheol da Hades, Jahannama ba wuri ba ne na zahiri.