Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Sa’ad da Aka Mana Rasuwa

Sa’ad da Aka Mana Rasuwa

Wata mai suna Vanessa da ke Ostareliya ta ce: “Na yi baƙin ciki sosai da yayana ya rasu ba zato ba tsammani. Bayan ’yan watanni idan na tuna da shi, nakan yi baƙin ciki sosai har na ji kamar ana soka mini wuƙa. A wasu lokuta kuma, nakan yi fushi domin a gani na bai kamata ya mutu haka kawai ba. Har ma nakan yi fushi da kaina domin ban kasance tare da shi sosai kafin ya mutu ba.”

IDAN ka taɓa rasa wani da kake ƙauna a mutuwa, babu shakka ka yi baƙin ciki sosai kuma ka kaɗaita. Wataƙila hakan ya sa ka fushi ko tsoro ko kuma lamirinka ya dame ka. Mai yiwuwa ma ka ji kamar gwamma ka mutu da ka rayu.

Amma ba laifi ba ne ka yi baƙin ciki sa’ad da aka yi maka rasuwa. Domin baƙin cikin yana nuna yadda kake ƙaunar mamacin. Amma me zai taimaka maka ka daina baƙin ciki?

ABUBUWAN DA SUKA TAIMAKA MA WASU

Ko da yake ba za ka daina yin baƙin ciki gabaki ɗaya ba, waɗannan shawarwarin za su iya taimaka maka:

BA LAIFI BA NE KA YI KUKA

Yadda mutane suke baƙin ciki sa’ad da wani nasu ya rasu ya bambanta sosai. Amma yin kuka zai taimaka maka ka rage baƙin cikin da kake yi. Vanessa, wadda muka ambata ɗazu ta ce: “Nakan yi kuka don na rage baƙin cikina.” Sofía, wadda ’yar’uwarta ta rasu ba zato ba tsammani ta ce: “Ina kuka sosai idan na tuna da abin da ya faru, kamar ina goge ciwo ne. Kukan da nake yi yana taimaka mini na sami sauƙi.”

KA GAYA WA MUTANE YADDA KAKE JI

A wasu lokuta, za ka bukaci a bar ka kai kaɗai kuma hakan ba laifi ba ne. Amma sa’ad da aka maka rasuwa, baƙin cikin zai kasance kamar kaya mai nauyi da ba za ka iya ɗaukawa kai kaɗai ba. Wani ɗan shekara goma sha bakwai mai suna Jared da mahaifinsa ya rasu ya ce: “Nakan gaya wa wasu yadda nake ji. Ban san ko sun fahimci abin da nake cewa ba amma na yi farin cikin gaya musu damuwata.” Janice, wadda muka ambata a talifi na farko ta ce: “Gaya wa mutane yadda nake ji ya ta’azantar da ni sosai. Na ji kamar sun fahimci yanayina kuma ba ni kaɗai ba ce nake fama da wannan baƙin cikin.”

KA BAR WASU SU TAIMAKA MAKA

Wata likita ta ce: “Idan wanda aka masa rasuwa ya ƙyale ’yan’uwa da abokai su taimaka masa a lokacin rasuwar, hakan zai taimaka masa ya iya jimre baƙin cikin da yake fama da shi.” Wataƙila abokanka suna so su taimaka maka amma ba su san yadda za su yi hakan ba. Don haka, ka gaya musu abin da kake so su yi maka.​—Karin Magana 17:17.

KA KUSACI ALLAH

Wata mai suna Tina ta ce: “Da mijina ya rasu sanaddiyar cutar kansa, na rasa wanda zan riƙa gaya wa damuwata, sai na gaya wa Allah kome da kome! Kowace rana ina roƙon sa ya taimaka mini in jimre. Allah ya taimaka mini a hanyoyin da ban taɓa tsammanin su ba.” Wata ’yar shekara 22 mai suna Tarsha da mahaifiyarta ta rasu, ta ce: “Karanta Littafi Mai Tsarki a kowace rana yana ta’azantar da ni sosai. Yana sa in yi tunani a kan abubuwa masu ban ƙarfafa.”

KA YI TUNANI A KAN LOKACIN TASHIN MATATTU

Tina ta ƙara da cewa: “Da farko, begen tashin matattu bai ta’azantar da ni ba domin ina ƙaunar mijina sosai kuma yaranmu suna son mahaifinsu ya kasance tare da su. Amma yanzu bayan shekara huɗu, wannan begen yana ƙarfafa ni in ci gaba da jimrewa. Nakan yi tunanin lokacin da zan sake ganin sa kuma hakan na sa ni farin ciki da kuma kwanciyar hankali!”

Ko da yake ba za ka daina baƙin ciki nan da nan ba. Amma abin da Vanessa ta faɗa zai iya ta’azantar da kai. Ta ce: “Za ka ji kamar ba za ka iya jimrewa ba amma da sannu a hankali, za ka yi nasara.”

Ka tuna, ba za ka daina kewar wanda ya rasu ba, duk da haka za ka iya yin rayuwa mai ma’ana. Da taimakon Allah, za ka iya jin daɗin tarayya da abokai kuma ka yi rayuwa mai inganci. Nan ba da daɗewa ba, Allah zai ta da waɗanda suka mutu. Yana so ka sake ganin ’yan’uwanka da suka mutu. A lokacin, za a cire baƙin ciki da kake yi gabaki ɗaya!