Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Mai Hikima Yana Kame Kansa

Mai Hikima Yana Kame Kansa

Toñi wadda take aikin kula da masu rashin lafiya ta kaɗa ƙararrawar ƙofa kuma wata mata ‘yar shekara hamsin ta fito. Matar ta hasala kuma ta zagi Toñi don ba ta zo aiki da wuri ba ta kula da mahaifiyar matar. Ko da yake Toñi ba ta makara ba, amma ta ba matar haƙuri.

DA Toñi ta zo aiki washegari, matar ta ƙara hasala mata kuma. Mene ne Toñi ta yi? Ta ce: “Abin ba shi da sauƙi, don bai kamata matar ta yi fushi ba.” Duk da haka, Toñi ta sake ba matar haƙuri kuma ta gaya wa matar cewa ta fahimci mawuyacin yanayi da take ciki.

Mene ne kake ganin za ka yi da a ce kai ne Toñi? Za ka yi iya ƙoƙarinka ka kame kanka ne? Shin zai yi maka wuya ka yi hakan? Hakika, ba zai kasance da sauƙi ba mutum ya natsu a irin yanayin da aka ambata ɗazu. Saboda haka idan muna cikin matsi ko kuma wani ya ɓata mana rai, zai yi wuya sosai mu kame kanmu.

Littafi Mai Tsarki ya ƙarfafa Kiristoci su riƙa kame kansu. Ban da haka, Kalmar Allah ta ce wanda yake kame kansa mai hikima ne. Yaƙub ya ce: “Wanene a cikinku mai-hikima ne, mai-fahimi? ta wurin kyakkyawan tasarrufinsa shi nuna ayyukansa cikin tawali’u [ko kamewa] na hikima.” (Yaƙ. 3:13) Ta yaya mai kame kansa yake nuna cewa shi mai hikima ne? Mene ne zai taimaka mana mu riƙa nuna wannan halin?

AMFANIN KAME KANKA

Yakan kwantar da hankalin masu fushi. “Mayar da magana da taushi yakan juyar da hasala: Amma magana mai-zafi takan ta da fushi.”​Mis. 15:1.

Mayar da magana mai zafi ga mai fushi yakan sa mutumin ya daɗa fushi. (Mis. 26:21) Amma idan muka yi magana da ladabi hakan zai sa mai fushi ya kwantar da hankalinsa. Kuma yana sa mai hasala ya canja halinsa.

Toñi ta ga cewa hakan gaskiya ne, don matar ta fashe da kuka da ta ga cewa Toñi ta kame kanta. Sai matar ta gaya wa Toñi cewa tana fuskantar matsaloli kuma iyalinta ma na fuskantar hakan. Don Toñi ta natsu kuma ta kame kanta, ta iya yi wa matar wa’azi kuma ta soma nazarin Littafi Mai Tsarki da ita.

Kasancewa da kamewa zai iya sa mu farin ciki. “Masu-albarka [farin ciki] ne masu-tawali’u: gama su za su gāji duniya.”​—⁠Mat. 5:⁠5.

Me ya sa masu kame kansu suke farin ciki? Don suna kame kansu, mutane da yawa waɗanda a dā suna faɗa sosai suna farin ciki yanzu. Rayuwarsu ta gyaru, kuma sun san cewa za su yi rayuwa mai kyau a nan gaba. (Kol. 3:12) Adolfo wani mai kula da da’ira a ƙasar Sifen ya tuna irin rayuwar da yake yi kafin ya soma bauta wa Jehobah.

Adolfo ya ce: “Rayuwata ba ta da ma’ana don sau da yawa nakan yi fushi sosai har wasu cikin abokaina suka soma jin tsoro na. Sai wata rana sa’ad da nake wani mugun faɗa, an aka soke ni da wuƙa a wurare shida kuma na kusan mutuwa.”

Amma don kalamin Adolfo da misalinsa, yanzu yana koya wa mutane su zama masu kame kansu. Mutane da yawa suna son sa don halinsa. Adolfo ya ce yana farin ciki don canjin da ya yi a rayuwarsa. Kuma yana godiya ga Jehobah don yadda ya taimaka masa ya zama mai kame kansa.

Kasancewa da kamewa yakan faranta wa Jehobah rai. “Ɗana, ka yi hikima, ka fa faranta zuciyata: domin in mayar da magana ga wanda ya zarge ni.”​Mis. 27:11.

Iblis magabcin Jehobah yana zaginsa. Kuma ya kamata wannan zagin ya sa Allah fushi, duk da haka, Littafi Mai Tsarki ya ce Jehobah “mai-jinkirin fushi” ne. (Fit. 34:6) Idan muka yi ƙoƙari mu yi koyi da yadda Allah ba ya saurin fushi kuma yana kame kansa, za mu yi abin da zai faranta wa masa rai sosai.​—⁠Afis. 5:⁠1.

Mutane suna yawan fushi a duniyar da muke ciki. Mukan haɗu da “masu-girman kai, masu-zagi, . . . masu-tsegumi, marasa-kamewa, masu-zafin hali.” (2 Tim. 3:​2, 3) Amma, hakan bai kamata ya sa Kirista ya zama mai zafin hali ba. Kalmar Allah ta ce “hikima mai-fitowa daga bisa . . . mai-salama ce, mai-sauƙin hali.” (Yaƙ. 3:17) Ta wajen zama masu salama da sanin yakamata, muna nuna cewa mu masu hikima ne. Irin wannan hikima za ta sa mu mayar da amsa yadda ta dace sa’ad da aka ɓata mana rai kuma za ta sa mu kusaci Jehobah mai hikima da babu kamarta.