Tarihi
Na Yi Kokarin Bin Misalai Masu Kyau
Na tambaye shi, “Ka san ko shekaruna nawa kuwa?” Sai ɗan’uwa Izak Marais wanda ya kira ni daga garin Patterson da ke jihar New York sa’ad da nake jihar Colorado ya ce: “Na san shekarunka.” Bari in gaya muku abin da ya sa muka yi irin wannan hirar.
AN HAIFE ni a birnin Wichita da ke jihar Kansas a Amirka a ranar 10 ga Disamba, shekara ta 1936. Ni ne ɗan fari a cikin yara huɗu. Iyayena William da Jean sun bauta wa Jehobah da ƙwazo. Mahaifina ne bawan ikilisiya, wato sunan da ake kiran wanda yake shugabanci a cikin ikilisiya ke nan a lokacin. Kakata Emma Wagner ce ta koya wa mahaifiyata gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki. Emma ta yi nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane da yawa, kuma wasu daga cikin waɗannan mutanen su ne Gertrude Steele, wadda ta yi shekaru da yawa tana hidima a ƙasar Puerto Rico. * Don haka ina da misalai da yawa masu kyau da zan yi koyi da su.
NA TUNA DA MISALAI MASU KYAU
Wata ranar Asabar da yamma sa’ad da nake ɗan shekara biyar, ni da mahaifina muna rarraba wa mutanen da suke wucewa a kan titi mujallun Hasumiyar Tsaro da kuma Consolation (yanzu Awake!) A lokacin, ƙasar tana cikin ƙasashen da suke Yaƙin Duniya na Biyu. Wani likita da ya sha giya ya bugu ya zo yana zagin Mahaifina domin ya ƙi saka hannu a yaƙi, kuma ya ce mahaifina matsoraci ne wanda yake gudun shiga aikin soja. Sai likitan ya tsaya a gaban mahaifina yana kallonsa ido da ido kuma ya ce, “Ka taɓa ni mana, kai matsoraci!” Na tsorata, amma abin da Mahaifina ya yi ya burge ni. Ya ci gaba da rarraba mujallu ga mutanen da suka taru. Da wani soja ya zo wucewa, sai likitan ya yi ihu kuma ya ce: “Zo ka kama wannan matsoracin!” Amma da sojan ya lura cewa wannan mutumin ya bugu, sai ya gaya masa, “Ka koma gidanka don ka dawo cikin hankalinka!” Bayan haka, sai sojan da mutumin suka bar wurin. Na yi farin ciki sosai da Jehobah ya sa mahaifina ya kasance da ƙarfin zuciya a wannan ranar. Mahaifina yana da shagon yin aski guda biyu a birnin Wichita, kuma wannan likitan yakan zo ya yi aski a shagon!
Sa’ad da nake ɗan shekara takwas, iyayena sun sayar da gidansu da shagunansu, kuma suka gina ƙaramin ɗaki mai taya kuma suka ƙaura zuwa jihar Colorado don su yi hidima a inda ake bukatar masu shela sosai. Mun koma da zama kusa da birnin Grand Junction. A wurin ne
iyayena suka yi hidimar majagaba kuma suka yi noma da kiwon dabbobi na ɗan lokaci. Sun yi hidimarsu da ƙwazo kuma Jehobah ya taimaka musu har suka kafa ikilisiya a wurin. A ranar 20 ga Yuni, shekara ta 1948 ne Mahaifina ya yi mini baftisma a wani rafin da ke kan tudu tare da wasu da suka soma nazarin Littafi Mai Tsarki, har da Billie Nichols da matarsa. Daga baya, Billie Nichols da matarsa sun yi hidimar mai kula da da’ira, kuma ɗansu da matarsa sun yi hakan.Mun yi tarayya na kud da kud da mutane da yawa da suka ba da kansu don yin wa’azin Mulkin Allah kuma mun tattauna abubuwa masu ban ƙarfafa da su. Mun yi hakan musamman ma da iyalin Steele, kamar Don da Earlene, Dave da Julia, da kuma Si da Martha. Dukan waɗannan mutanen sun taimaka mini sosai. Sun nuna mini cewa saka al’amura na Mulkin Allah a kan gaba ne take sa rayuwar mutum ta kasance da ma’ana da kuma sa mutum farin ciki.
NA SAKE ƘAURA
Sa’ad da nake ɗan shekara 19, wani abokinmu mai suna Bud Hasty ya ce mu je hidimar majagaba a kudancin Amirka. Mai kula da da’ira ya ce mu je birnin Ruston a jihar Louisiana inda Shaidu da yawa ba sa halartan taro da kuma fita wa’azi. An gaya mana mu riƙa gudanar da dukan taro a kowane mako ko da babu wanda ya halarci taron. Mun samu wani wurin da ya dace don yin taro kuma muka yi wasu gyare-gyare. Ƙari ga haka, muna gudanar da dukan taron, ko da yake mu biyu ne kaɗai muke halartan taron. Kowannenmu yakan ba da jawabi a taron, sai ɗayan ya amsa dukan tambayoyin. Idan za a yi gwaji a jawabin, mu biyun za mu yi hakan duk da cewa babu mutanen da suka halarci taron. Daga baya, wata ‘yar’uwa tsohuwa ta soma halartan taron. Sa’an nan wasu ɗaliban Littafi Mai Tsarki da kuma wasu da suka daɗe ba sa halartan taro sun soma zuwa. Ba da daɗewa ba aka kafa ikilisiya a wurin.
Wata rana, ni da ɗan’uwa Bud mun haɗu da wani faston Church of Christ kuma ya yi magana a kan nassosin da ban san su ba. Hakan ya ɗan firgitar da ni kuma ya sa ni tunani sosai a kan abin da na yi imani da shi. Na yi mako guda ina kunna fitila a tsakar dare don in nemo amsoshin tambayoyin da wannan faston ya yi. Hakan ya taimaka mini in kasance da tabbaci a kan abin da na yi imani da shi, kuma na yi ɗokin ƙara yin magana da wani fasto.
Ba da daɗewa ba bayan hakan, sai mai kula da da’ira ya ce mini in ƙaura zuwa birnin El Dorado da ke jihar Arkansas don in taimaka wa ikilisiyar da ke wajen. Sa’ad da nake wajen, nakan yi tafiya zuwa jihar Colorado don in je wurin da ake sa mutane su shiga
aikin soja. A wani lokacin da nake wannan tafiyar da wasu majagaba a cikin motata, mun yi hatsari a jihar Texas kuma motata ta yi kaca-kaca. Sai muka kira wani ɗan’uwa kuma ya zo ya kai mu gidansa da kuma taron ikilisiya. A taron, an yi sanarwa cewa mun yi hatsari, kuma ‘yan’uwan suka ba mu gudummawar kuɗi. Ƙari ga haka, ɗan’uwan ya sayar da motata dalla ashirin da biyar.Mun samu motar da ta kai mu birnin Wichita, inda ɗan’uwa McCartney wani abokinmu yake hidimar majagaba. Yana da tagwaye maza masu suna Frank da Francis, kuma su abokai na ne na kud da kud har yanzu. Suna da wata tsohuwar mota kuma suka sayar mini da ita dala ashirin da biyar, wato ainihin kuɗin da aka biya ni don motata da ta lalace. Wannan ne lokaci na farko da na ga yadda Jehobah ya yi mini tanadin abubuwan da nake bukata don na saka al’amura na Mulkin Allah a kan gaba a rayuwata. A wannan lokacin ne iyalin McCartney suka nuna mini wata ‘yar’uwa mai ƙwazo mai suna Bethel Crane. Mahaifiyarta mai suna Ruth Mashaidiya ce mai ƙwazo a birnin Wellington da ke jihar Kansas, kuma ta ci gaba da hidimar majagaba har lokacin da ta ba shekara 90 baya. Haɗuwarmu da Bethel bai kai shekara ɗaya ba sai muka yi aure a shekara ta 1958, kuma muka soma hidimar majagaba tare a birnin El Dorado.
GAYYATAR DA TA SA MU FARIN CIKI
Bayan mun yi tunanin a kan misalai masu kyau da ‘yan’uwa suka kafa mana sa’ad da muke girma, sai muka tsai da shawarar yin duk wata hidimar da ƙungiyar Jehobah ta ce mana mu yi. An tura mu yin hidimar majagaba ta musamman a birnin Walnut Ridge da ke jihar Arkansas. Bayan haka, a shekara ta 1962, mun yi farin ciki sosai sa’ad da aka gayyace mu mu halarci aji na 37 na makarantar Gilead. Mun kasance a aji ɗaya da ɗan’uwa Don Steele kuma hakan ya ƙara sa mu farin ciki. Bayan mun sauke karatun, sai aka tura ni da matata Bethel hidima a jihar Nairobi a ƙasar Kenya. Mun yi baƙin ciki sosai da muka bar jihar New York, amma mun yi farin ciki sa’ad da muka haɗu da ‘yan’uwanmu a tashar jirgin ƙasa da ke Nairobi!
Ba da daɗewa ba muka soma jin daɗin ƙasar Kenya da kuma hidimarmu. Kuma mutane na farko da muka yi nazarin Littafi Mai Tsarki da su da suka samu ci gaba su ne Chris da Mary Kanaiya. Har yanzu suna hidima ta cikakken lokaci a Kenya. Bayan shekara guda, an tura mu hidima a birnin Kampala a ƙasar Uganda, kuma mu ne masu wa’azi daga ƙasar waje da muka fara zuwa wannan ƙasar. Mun yi farin ciki sosai a lokacin domin mutane da yawa suna son yin nazarin Littafi Mai Tsarki, kuma daga baya sun zama Shaidun Jehobah. Bayan mun yi shekara uku da rabi a Afirka, sai muka koma Amirka don mu haifi ‘ya’ya. Mun yi baƙin ciki sosai ranar da muka bar Afirka fiye da yadda muka yi a ranar da muka bar New York, domin muna ƙaunar mutanen Afirka. Kuma muna fatan cewa za mu sake komawa wata rana.
MUN SAMU SABON AIKI
Mun koma da zama a yammacin gangaren jihar Colorado inda iyayena suke zama. Ba da daɗewa ba aka haifi ‘yarmu ta farko Kimberly, kuma bayan watanni 17 aka haifi Stephany. A matsayinmu na iyaye, mun ɗauki hakkinmu da muhimmanci sosai, kuma mun koya wa yaranmu gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki. Muna so mu kafa musu misalai masu kyau da ‘yan’uwa suka kafa mana. Ko da yake kafa wa yara misali mai kyau yakan taimaka musu, hakan ba tabbaci ba ne cewa za su bauta wa Jehobah sa’ad da suka yi girma. Abin da ya faru da ƙanena da ƙanwata ke nan. Duk da cewa an kafa musu misalai masu kyau, sun
daina bauta wa Jehobah. Ina fatan wata ran za su komo ga Jehobah.Mun ji daɗin renon yaranmu kuma mukan yi abubuwa tare a matsayinmu na iyali. Alal misali, tun da yake muna zama kusa da garin Aspen da ke jihar Colorado, sai dukanmu muka soma wasan gudu a ƙanƙara, kuma muna amfani da wannan lokacin don mu tattauna da yaranmu. Ƙari ga haka, mukan je yin zango kuma mu yi hira da su a lokacin da muke shan ɗumi. Ko da yake su ƙananan yara ne, sukan yi tambayoyi kamar, “Mene ne zan yi idan na girma?” da kuma “Wane irin mutum ne zan aura?” Mun yi iya ƙoƙarinmu don mu koya musu ƙa’idodin da ke cikin Littafi Mai Tsarki. Mun taimaka musu su kafa makasudin soma hidima ta cikakken lokaci, kuma mun koya musu amfanin auren wanda ya kafa makasudi irin na su. Ban da haka, mun koya musu cewa ba shi da kyau su yi aure sa’ad da suke ƙanana. Mukan gaya musu “Kada ku yi aure sai kun kai shekara 23.”
Kamar yadda iyayenmu suka yi, mu ma mun yi ƙoƙari wajen halartan taro da kuma fita wa’azi a kai a kai tare da yaranmu. Mukan gayyaci wasu da suke hidima ta cikakken lokaci su zauna a gidanmu. Ƙari ga haka, mukan yi hira game da lokacin da muka yi hidima a ƙasar waje. Mun gaya musu cewa wata rana wataƙila dukanmu za mu je Afirka. Kuma yaranmu sun so mu yi hakan.
Muna yin ibada ta iyali a kai a kai, kuma a lokacin mukan yi kwaikwayon abubuwan da za su iya faruwa a makaranta. Yaran ne suke ɗaukan matsayin Mashaidi da ke amsa tambayoyi. Sun ji daɗin koyon abubuwa a wannan hanyar, kuma hakan ya sa sun kasance da gaba gaɗi. Yayin da suke girma, a wasu lokuta ba sa so mu yi ibada ta iyali. Akwai wani lokacin da na yi fushi, kuma na gaya musu cewa kowannensu ta koma ɗakinta don ba za mu yi nazari ba. Sun yi mamaki sosai kuma hakan ya sa suka soma kuka cewa suna so su yi nazari. Hakan ya sa mun fahimci cewa mun koya musu su so abubuwan da suka shafi ibadarsu ga Jehobah. Saboda haka, sun yi girma suna son nazari, kuma mukan ƙyale su su faɗi ra’ayinsu. Amma, a wasu lokatai sukan yi shakkar wasu koyarwar Littafi Mai Tsarki kuma hakan yana sa mu baƙin ciki sosai. Duk da hakan, mun yi ƙoƙari don mu san abin da ke cikin zuciyarsu. Bayan mun tattauna da su, sukan gamsu da ra’ayin Jehobah a kan batun.
BI DA CANJIN YANAYI
Shekarun da muka yi renon yaranmu sun shige da sauri. Ƙungiyar Jehobah ta taimaka da kuma yi mana ja-gora wajen renonsu, kuma mun yi iya ƙoƙarinmu don mu rene su su ƙaunaci Jehobah. Da suka gama makarantar sakandare, sai suka soma hidimar majagaba kuma suka koyi aikin da zai taimaka musu su riƙa biyan bukatunsu, hakan ya sa mu farin ciki sosai. Sun koma birnin Cleveland da ke jihar Tennessee tare da wasu ‘yan’uwa mata don su yi hidima a inda ake bukatar masu shela sosai. Mun yi kewarsu sosai, amma mun yi farin ciki cewa suna yin hidima ta cikakken lokaci. Ni da matata Bethel mun koma hidimar majagaba, kuma hakan ya ba mu damar samun wasu gata. Mun yi hidimar wakilin mai kula da da’ira da kuma aiki a babban taro.
Yaranmu sun je Landan a Ingila, kuma sun ziyarci ofishinmu da ke ƙasar kafin su koma jihar Tennessee. A lokacin, shekarar Stephany 19 kuma ta haɗu da Paul Norton, wani matashi da ke hidima a Bethel. Sa’ad da suka sake wata ziyarar, Kimberly ta haɗu da wani abokin aikin Paul Norton mai suna Brian Llewellyn. Paul da Stephany sun yi aure sa’ad da take ‘yar shekara 23. Bayan shekara guda, Kimberly ta auri Brian sa’ad da take ‘yar shekara 25. Hakika, sun yi aure sa’ad da suka kai shekara 23. Mun amince da waɗanda suka aura da dukan zuciyarmu.
Yesu ya ba da umurni cewa ‘ku fara biɗan Mulkin’ Allah. Yaranmu sun gaya mana cewa misalinmu da na iyayenmu ne ya taimaka musu su yi biyayya ga wannan umurnin ko a lokacin da suke fuskantar matsalar kuɗi. (Mat. 6:33) An gayyaci Paul da Stephany su halarci aji na 105 na makarantar Gilead a watan Afrilu ta shekara ta 1998, kuma bayan haka an tura su hidima a ƙasar Malawi a Afirka. An gayyaci Brian da Kimberly su yi hidima a Bethel da ke Landan kuma daga baya aka mai da su Bethel da ke Malawi. Mun yi farin ciki matuƙa, kuma wannan ita ce rayuwa mafi inganci da matasa za su iya yi.
GAYYATA MAI BAN MAMAKI
Abin da na ambata ɗazu a farkon wannan labarin ya faru ne a watan Janairu, shekara ta 2001. Ɗan’uwa
Marais, mai kula da Sashen Taimakon Masu Fassara ya kira ni kuma ya gaya mini cewa ana shirin koya wa masu fassara a faɗin duniya Turanci kuma ana son in zama ɗaya daga cikin masu koyarwar ko da yake shekarata 64. Ni da matata Bethel mun yi addu’a a kan batun kuma mun tattauna hakan da mahaifiyata da kuma surkuwata don su ba mu shawara. Dukansu suna so mu tafi ko da yake muna taimaka musu. Sai na sake kiran ɗan’uwan kuma na ce masa za mu yi farin cikin yin wannan aikin.An gano cewa mahaifiyata tana da ciwon kansa. Sai na gaya wa matata cewa za mu tsaya don mu taimaka wa Linda wajen kula da ita. Mahaifiyata ta ce: “Kada ka yi hakan, ba zan ji daɗin ba idan ba ku je ba.” Ita ma Linda tana ganin ya fi kyau mu je. Mun yi farin ciki sosai don sadaukarwar da suka yi da kuma yadda abokanmu da ke yankin suka taimaka musu. Ranar da muka tafi Cibiyar Koyarwa ta Watchtower da ke Patterson da ke jihar New York a Amirka, Linda ta kira mu kuma ta gaya mana cewa Mahaifiyata ta rasu. Bayan haka, sai muka saka ƙwazo a sabon aikinmu kamar yadda mahaifiyata za ta so mu yi.
Mun yi farin ciki sosai sa’ad da aka tura mu hidima a ofishin da ke Malawi, inda yaranmu da mazansu suke hidima. Sake haɗuwa da su ya sa mu farin ciki sosai! Bayan haka, mun je ƙasar Zimbabwe da kuma Zambia don mu koyar da mafassaran da suke wajen. Bayan mun yi shekara uku da rabi muna koyar da Turanci, sai aka ce mu koma ƙasar Malawi don mu rubuta irin ƙalubalen da Shaidun Jehobah suka fuskanta a ƙasar don sun ƙi saka hannu a siyasa. *
A shekara ta 2005, mun yi baƙin cikin komawa gidanmu a garin Basalt da ke jihar Colorado inda ni da Bethel muka ci gaba da yin hidimar majagaba. A shekara ta 2006, Brian da Kimberly sun ƙaura zuwa gidan da ke kusa da mu don su yi renon yaransu mata guda biyu masu suna Mackenzie da Elizabeth. Har yanzu Paul da Stephany suna hidima a ƙasar Malawi inda Paul yake hidima a matsayin ɗaya daga ciki Kwamitin da ke Kula da ofishin Shaidun Jehobah. Yanzu na kusan kai shekara 80, kuma ina farin cikin ganin matasan da na yi aiki tare da su suna yin irin hidimar da na yi. Muna wannan farin cikin ne don misalai masu kyau da aka kafa mana, da kuma waɗanda muka yi ƙoƙarin kafa wa yaranmu da jikokinmu don su ma su amfana.
^ sakin layi na 5 Ka duba mujallun Hasumiyar Tsaro na 1 ga Mayu, 1956, shafuffuka na 269 zuwa 272, da kuma 15 ga Maris, 1971, shafuffuka na 186 zuwa 190 don ka sami ƙarin bayani game da yadda mambobin iyalin Steele suka yi hidima a ƙasashen waje.
^ sakin layi na 30 Alal misali, ka duba tarihin rayuwar Trophim Nsomba a Hasumiyar Tsaro na 15 ga Afrilu 2015, shafuffuka na 14-18.