Shin Wahala Horo Ne Daga Allah?
LUZIA TANA ƊINGISHI IDAN TANA TAFIYA. Ta kamu da cutar polio a lokacin da take ƙarama, kuma cutar takan iya kama wasu. Ban da haka ma, cutar takan yi wa jijiyoyin jikin mutum illa. A lokacin da Luzia take shekara 16, matar da take mata aiki ta gaya mata cewa, “Wannan cutar horo ne daga Allah domin a lokacin da kike ƙarama ba ki yi wa mahaifiyarki biyayya ba.” Shekaru da yawa sun wuce bayan an yi mata maganar nan, amma har ila tana tuna irin baƙin cikin da ta yi a lokacin.
A LOKACIN DA DAMARIS TA KAMU DA CUTAR KANSA TA ƘWAƘWALWA, mahaifinta ya tambaye ta: “Me kika yi da wannan cutar ta kama ki? Babu shakka, kin yi wani abu mai muni shi ya sa Allah yake miki horo.” Furucin da mahaifinta ya yi ya sa Damaris baƙin ciki sosai.
Mutane sun yi shekaru da yawa suna gaskata cewa ciwo horo ne daga Allah. Littafin nan Manners and Customs of Bible Lands ya ce mutane da yawa a zamanin Yesu sun gaskata cewa “zunubin mutum ko na danginsa ne yake sa shi yin ciwo kuma hakan horo ne don zunubin.” Bayan zamanin manzanni, littafin nan Medieval Medicine and the Plague ya ce, “wasu sun gaskata cewa Allah yana amfani da annoba don ya azabtar da mutanen da suka yi zunubi.” A lokacin da miliyoyin mutane suka mutu don wata annoba a Turai a ƙarni na 14, shin Allah ne yake hukunta mugayen mutane? Ko kuma wasu ƙwayoyin cuta ne suka jawo hakan kamar yadda masana a fannin kiwon lafiya suka gano? Wasu za su yi tunani, shin Allah yana amfani da cuta don ya azabtar da mutane domin zunubin da suka yi? a
KA YI LA’AKARI DA WANNAN: Idan cuta da wahala horo ne daga Allah, to me ya sa Ɗansa Yesu ya warkar da marasa lafiya? Shin hakan ba zai nuna cewa yana rena hukuncin Allah da adalcinsa ba? (Matiyu 4:23, 24) Yesu ba zai taɓa yin wani abin da zai saɓa nufin Allah ba. Yesu ya ce: “Kullum ina yin abin da yake so.” Kuma ya ƙara da cewa, “Ina yin daidai abin da Uba ya faɗa mini in yi.”—Yohanna 8:29; 14:31.
Littafi Mai Tsarki ya faɗi dalla-dalla cewa: Jehobah Allah “ba ya ruɗu.” (Maimaitawar Shari’a 32:4) Alal misali, Allah ba zai taɓa sa jirgin sama ya faɗo kuma ya halaka mutane da yawa da ba su san hawa ko sauka ba don yana son ya hukunta wani a cikin jirgin! Ibrahim bawan Allah mai aminci ya san cewa Allah mai adalci ne shi ya sa ya ce Allah ba zai taɓa “kashe mai adalci tare da mai mugunta” ba. Ya ce hakan ba zai taɓa ‘yiwuwa’ ba. (Farawa 18:23, 25) Littafi Mai Tsarki ya ƙara da cewa, “Allah ba zai taɓa aikata mugunta ba” kuma ba ya yin “kuskure.”—Ayuba 34:10-12.
ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE GAME DA WAHALA
Wahalar da muke sha ba horo daga Allah don zunubin da muka aikata ba ne. Yesu da kansa ya bayyana batun nan dalla-dalla a lokacin da shi da almajiransa suka ga wani mutum da aka haife shi makaho. “Almajiransa suka tambaye shi suka ce, ‘Malam, zunubin wane ne ya sa an haifi wannan mutum makaho? Zunubinsa ne, ko zunubin iyayensa?’ Yesu ya amsa ya ce, ‘Ba wai saboda mutumin nan ko iyayensa sun yi zunubi ba ne, amma an haife shi makaho ne domin a nuna ikon Allah a kansa.’”—Yohanna 9:1-3.
Mutane a zamanin Yesu sun yi imani cewa ciwo horo ne daga Allah, shi ya sa almajiran Yesu suka yi Yohanna 9:6, 7) Don haka, waɗanda suke fama da rashin lafiya a yau za su sami ƙarfafa wajen sanin cewa ba Allah ba ne ya sa su ciwon.
mamaki sa’ad da ya gaya musu cewa cutar mutumin ba sanadiyyar zunubinsa ko na iyayensa ba ne. Warkar da makahon da Yesu ya yi ya tabbatar wa mutane cewa wahala ba daga Allah ba ne. (Nassosi sun tabbatar mana cewa
-
“Allah ba ya jarrabtar kowa da mugunta, kuma ba ya yiwuwa a jarrabce shi.” (YAKUB 1:13) Babu shakka, za a kawo ƙarshen “mugunta” da cututtuka da baƙin ciki da mutuwa da suke damun mutane shekaru aru-aru nan ba da daɗewa ba.
-
Yesu Kristi zai “warkar da duk marasa lafiya.” (MATIYU 8:16) Warkar da mutanen da Yesu ya yi ya nuna abin da zai yi wa mutanen duniya gabaki ɗaya a Mulkin Allah.
-
“[Allah] zai share musu dukan hawaye daga idanunsu. Babu sauran mutuwa, ko baƙin ciki, ko kuka, ko azaba. Gama abubuwan dā sun ɓace.”—RU’UYAR DA AKA YI WA YOHANNA 21:3-5.
TO WA KE SA MU WAHALA?
Me ya sa ’yan Adam suke baƙin ciki da shan wahala haka? Mutane sun daɗe suna yin wannan tambayar. Idan ba Allah ba ne yake sa muke shan wahala, to waye ne? Za a amsa waɗannan tambayoyin a talifi na gaba.
a Akwai wasu lokuta a dā da Allah ya hukunta mutane don wasu zunubai da suka yi. Amma Littafi Mai Tsarki bai nuna cewa Jehobah yana amfani da ciwo ko wani irin bala’i a zamaninmu don ya yi wa mutanensa horo domin zunubin da suka yi ba.
Idan ciwo horo ne daga Allah, to me ya sa Yesu ya warkar da marasa lafiya?