Yadda Za Ka Amfana Daga Taimakon Allah
Allah ya halicce jikinmu a hanyar da zai iya warkewa da kansa. Idan mun ji rauni, “nan da nan jikinmu yakan yi wani abu mai ban mamaki don ya warkar da ciwon ko da ciwon babba ne ko kuma ƙarami.” (Bisa ga Johns Hopkins Medicine) Da farko, yakan yi wani abu don kada jini ya riƙa zuba. Bayan haka, sai ya gyara ciwon kuma ya ƙarfafa jijiyoyinmu.
KA YI LA’AKARI DA WANNAN: Da yake Mahaliccinmu ya yi jikinmu a hanyar zai riƙa warkar da raunuka, shin hakan bai ba mu tabbaci cewa zai taimaka mana a lokacin da muke baƙin ciki ba? Wani marubucin zabura ya ce: “Yakan warkar da masu fid da zuciya, yakan ɗaure raunukansu.” (Zabura 147:3) Amma idan kana baƙin ciki, ta yaya za ka tabbata cewa Jehobah zai ɗaure maka raunukanka a yanzu da kuma a nan gaba?
ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE GAME DA YADDA ALLAH YAKE KAUNAR MU
Allah ya yi alkawari cewa: “Kada fa ka ji tsoro, gama ina tare da kai, kada ka damu, gama ni ne Allahnka; Zan sa ka yi ƙarfi, in kuma taimake ka.” (Ishaya 41:10) Duk mutumin da ya san cewa Jehobah ya damu da shi zai yi farin ciki kuma zai sami ƙarfin zuciya don ya jimre matsaloli. Manzo Bulus ya kira hakan ‘salama ta Allah irin wadda ta wuce dukan ganewar ɗan Adam.’ Ya kuma ƙara da cewa: “Zan iya yin kome ta wurin Almasihu wanda yake ƙarfafa ni.”—Filibiyawa 4:4-7, 9, 13.
Nassosi sun taimaka mana mu kasance da tabbaci cewa alkawuran da Jehobah ya yi mana za su cika. Alal misali, littafin Ru’uyar da aka yi wa Yohanna 21:4, 5 (yana shafi na gaba) ya gaya mana abin da Jehobah zai yi da kuma dalilin da ya sa za mu tabbata cewa zai yi hakan:
-
‘Zai share dukan hawaye’ daga idanun mutane. Jehobah zai kawo ƙarshen dukan wahala da matsalolin da muke fama da su har da wasu bukatun da wasu suke ganin ba su da muhimmanci sosai.
-
Wanda “yake zama a kujerar mulkin” sama, wato Allah Maɗaukakin Sarki da ya halicci dukan abubuwa, zai yi amfani da ikonsa domin ya kawo ƙarshen wahala kuma ya taimaka mana.
-
Jehobah ya nuna cewa alkawuransa “masu-aminci ne masu-gaskiya” kuma. Hakan yana nufin cewa Jehobah ya yi amfani da sunansa don ya tabbatar mana cewa zai cika alkawuran da ya yi.
Sararin sama da kuma Littafi Mai Tsarki suna nuna mana halayen Jehobah. Halittu suna taimaka mana mu san shi sosai don mu zama aminansa. Littafi Mai Tsarki kuma ya nuna dalla-dalla cewa: Idan muka “yi kusa da Allah, shi kuwa zai yi kusa da” mu. (Yaƙub 4:8) Littafin Ayyukan Manzanni 17:27 ya ce: “Bai yi nesa da kowannenmu ba.”
Idan ka nemi lokaci don ka san Allah sosai, za ka ga cewa yana “lura” da kai. (1 Bitrus 5:7) Ta yaya za mu amfana idan mun san cewa Jehobah yana kula da mu?
Ka yi la’akari da labarin wani mutum mai suna Toru, daga ƙasar Jafan. Mahaifiyarsa Mashaidiyar Jehobah ce, duk da haka, ya haɗa kai da wata ƙungiyar ’yan iska a Jafan da ake kira da suna yakuza. Ya ce, “Na yi imani a lokacin cewa Allah ya tsane ni kuma na ɗauka cewa rasuwar mutanen da nake ƙauna horo ne daga Allah.” Toru ya ce irin mutanen da yake tarayya da su da kuma ra’ayinsa ya sa ya zama “mugu marar tausayi.” Ya yi magana game da burinsa ya ce, “Na so in kashe wani da ya fi ni shahara kuma in mutu tun ina matashi domin in yi suna.”
Amma sa’ad da Toru da matarsa, Hannah suka yi nazarin Littafi Mai Tsarki, ya canja halinsa da ra’ayinsa gabaki ɗaya. Matarsa Hannah ta ce: “Na lura da yadda mijina ya canja rayuwarsa.” Yanzu, Toru ya ce: “Akwai Allah wanda yake kula da kowannenmu. Ba ya son kowa ya mutu kuma yana gafarta wa mutane idan sun tuba da gaske. Yana sauraron abubuwan da ba za mu iya gaya ma wasu ba kuma yana fahimtar mu fiye da kowa. Jehobah ya kusan kawo ƙarshen dukan wahala da baƙin ciki. Ko a yanzu ma yana taimaka mana a hanyoyin da ba mu taɓa tsammani ba. Yana kula da mu kuma yana ƙarfafa mu a lokacin da muke sanyin gwiwa.”—Zabura 136:23.
Labarin Toru ya nuna cewa za mu kasance da bege kuma mu yi rayuwa mai ma’ana yanzu idan muka san cewa Allah yana marmarin kawo ƙarshen dukan wahala. Babu shakka, ko a wannan duniyar da muke fama da matsaloli ma, za mu iya amfana daga yadda Allah yake kula da mu.
“Zai share musu dukan hawaye daga idanunsu. Babu sauran mutuwa, ko baƙin ciki, ko kuka, ko azaba. Gama abubuwan dā sun ɓace. Sai wannan da yake zama a kujerar mulkin ya ce, ‘Ga shi, yanzu zan yi dukan kome sabo!’ Ya kuma ce mini, ‘Rubuta wannan, gama wannan maganar gaskiya ce, kuma tabbatacciya ce.’”—Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 21:4, 5.