Yadda Za Ka More Rayuwa a Nan Gaba
ME KAKE GANI ZAI SA MUTUM YA MORE RAYUWA A NAN GABA? KANA GANIN:
Zuwa jami’a ne?
Kuɗi ne?
Zama mutumin kirki ne?
Ko wani abu dabam?
Nassosi Masu Tsarki sun ce:
“Idan ka sami hikima, akwai sa rai [bege] nan gaba.”—KARIN MAGANA 24:14.
Idan ka bincika Nassosi Masu Tsarki, za ka sami shawarwari masu kyau da za su sa ka more rayuwa a nan gaba.