Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 50

WAƘA TA 135 Jehobah Ya Ce: “Ɗana Ka Yi Hikima”

Iyaye, Ku Taimaki Yaranku Su Kara Ba da Gaskiya

Iyaye, Ku Taimaki Yaranku Su Kara Ba da Gaskiya

“Ku . . . tabbatar da abin da yake nufin Allah, wato abin da yake mai kyau, abin karɓa ga Allah, da kuma abin da yake cikakke.”ROM. 12:2.

ABIN DA ZA MU KOYA

A talifin nan, za mu ga yadda iyaye za su tattauna da yaransu don su taimaka musu su ƙara gaskata da Allah da kuma Littafi Mai Tsarki.

1-2. Idan yaro ya yi wa iyayensa tambaya game da imaninmu, yaya ya kamata su ɗauki tambayar?

 A GASKIYA yin renon yara ba ƙaramin aiki ba ne. Idan kuna da yara, muna yaba muku da ƙoƙarin da kuke yi don ku taimaka musu su zama masu bangaskiya. (M. Sha. 6:6, 7) Mai yiwuwa yayin da yaranku suke girma, za su soma yin wasu tambayoyi. Alal misali, ƙila su ce me ya sa Jehobah ya hana mu yin wasu abubuwa?

2 Idan kun ji ɗanku ko ꞌyarku tana irin tambayar nan, ƙila ku damu kuma ku ga kamar yaron bai gaskata da Allah ko Littafi Mai Tsarki ba. Amma a gaskiya idan yaro yana yin irin tambayoyin nan, abu mai kyau ne. Hakan zai taimaka masa ya tabbatar da abin da ya yi imani da shi. (1 Kor. 13:11) Don haka kar ku ji tsoro. Idan yaranku suka yi irin tambayoyin nan, ku yi amfani da damar ku taimaka musu su yi tunani mai zurfi a kan batun don su ƙara gaskata da Allah da kuma Littafi Mai Tsarki.

3. Me za mu tattauna a talifin nan?

3 A talifin nan, za mu tattauna yadda iyaye za su taimaka wa yaransu su tabbatar da abin da suka yi imani da shi, su ga amfanin bin ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki, da kuma yadda za su bayyana wa mutane abin da suka yi imani da shi. Za mu kuma tattauna abin da ya sa ya dace yara su dinga yin tambayoyi, kuma za mu ga wasu abubuwa da iyaye za su iya yi da yaransu don su sami damar yin hira game da imaninmu.

KU TAIMAKI YARANKU SU TABBATAR DA ABIN DA SUKA YI IMANI DA SHI

4. Waɗanne tambayoyi ne wasu yara suke yi, kuma me ya sa?

4 Gaskiyar ita ce, ba lallai ne yaranku su gaskata da abu don kawai kun gaskata da shi ba. Kuma ba a haifan yaro da bangaskiya, kamar yadda ku ma ba a haife ku da bangaskiya ba. A-kwana-a-tashi, wataƙila yaro ya soma yin tambayoyi kamar: ‘Yaya aka yi aka san cewa akwai Allah? Abin da ke Littafi Mai Tsarki gaskiya ne kuwa?’ Littafi Mai Tsarki ya ce yana da kyau mu yi ‘amfani da hankalinmu’ kuma mu “gwada kome.” (Rom. 12:1, NWT; 1 Tas. 5:21) Ta yaya za ku taimaki yaron ya ƙara gaskata da Littafi Mai Tsarki?

5. Mene ne iyaye za su yi don su taimaki yaronsu ya gaskata da Littafi Mai Tsarki? (Romawa 12:2)

5 Ku ƙarfafa yaranku su nemi tabbacin. (Karanta Romawa 12:2.) Idan yaro ya yi muku tambaya, ku nuna masa yadda zai yi bincike don ya sami amsar ta wurin yin amfani da kayan bincikenmu, kamar Littafin Bincike Don Shaidun Jehobah. Alal misali, don ya ga tabbacin cewa Littafi Mai Tsarki “kalmar Allah” ce ba na ꞌyan Adam ba, zai iya zuwa inda aka ce “Littafi Mai Tsarki,” sai ya duba talifofin da ke ƙarƙashin jigon nan, “Allah Ne Ya Hure.” (1 Tas. 2:13) Ƙari ga haka, zai iya yin bincike a kan Birnin Nineba da ke ƙasar Assuriya ta dā. Wasu masu bincike sun ce ba wani birni da ake kira Nineba a dā. Amma a wajen shekara ta 1850, an gano wasu abubuwa game da birnin a can cikin ƙasa. Hakan ya nuna cewa abin da Littafi Mai Tsarki ya ce gaskiya ne. (Zaf. 2:13-15) Don yaronku ya sami ƙarin bayani a kan abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da hallakar birnin Nineba, da yadda hakan ya cika, ya karanta talifin nan, “Ka Sani?” da ke Hasumiyar Tsaro ta Nuwamba 2021. Ku gaya ma yaronku ya gwada abin da Littafi Mai Tsarki ya ce da abin da littattafan bincike ko bayanan masana da aka tabbatar da su suka ce. Hakan zai taimaka masa ya tabbatar da cewa abin da Littafi Mai Tsarki ya ce gaskiya ne.

6. Ta yaya iyaye za su taimaki yaransu su yi tunani? Ka ba da misali. (Ka kuma duba hoton.)

6 Ku taimaki yaranku su yi tunani. Iyaye, ku nemi zarafin yin hira da yaranku game da Littafi Mai Tsarki da kuma yin imani da Allah. Za ku iya koya ma yaranku irin abubuwan nan idan kuka je wurin shakatawa mai dabbobi da itatuwa da furanni, ko wurin adana kayan tarihi, ko rashen ofishinmu. Za ku kuma iya kallon wasu wuraren nan ta intane, ko ku yi amfani da hotunansu ko bidiyoyinsu. Idan kuna kallon kayan tarihi, za ku iya nuna ma yaranku abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da wani abu a wurin, ko wani abin da ya faru a dā. Hakan zai taimaka musu su ga cewa abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa gaskiya ne. Za ku iya gaya musu game da dutsen da ake kira Moabite Stone. Dutsen nan ya yi shekaru 3,000, kuma an ga sunan Jehobah a rubuce a kansa. Yanzu haka, ainihin dutsen yana a wani wurin adana kayan tarihi a ƙasar Faransa. Za ku iya kallon hotonsa a intane ko a littattafanmu. Kuma akwai irinsa da aka ƙera a Hedkwatar Shaidun Jehobah a Warwick, da ke New York. An ajiye shi a wurin adana kayakin tarihi da ake kira “The Bible and the Divine Name. Akwai rubutu a kan dutsen cewa sarkin Mowab mai suna Mesha ya yi wa Israꞌila tawaye, kuma hakan ya yi daidai da abin da Littafi Mai Tsarki ya ce. (2 Sar. 3:4, 5) Idan yaranku suka ga abubuwan da suka tabbatar da cewa abin da ke Littafi Mai Tsarki gaskiya ne da idanunsu, bangaskiyarsu za ta ƙaru.—Ka ga misalin da ke 2 Tarihi 9:6.

Ku yi amfani da kayan tarihi da suka shafi abin da Littafi Mai Tsarki ya ce don ku taimaki yaranku su yi tunani mai zurfi a kan Allah da Littafi Mai Tsarki (Ka duba sakin layi na 6)


7-8. (a) Mene ne kyan halittu da kuma tsarin da muke gani a jikinsu ya nuna mana? Ka ba da misali. (Ka kuma duba hoton.) (b) Wane irin tambaya ne zai taimaki yaranku su ƙara gaskata cewa akwai Mahalicci?

7 Ku taimaki yaranku su yi tunani a kan halittu. Idan kuna tafiya a lambu ko inda akwai itatuwa da furanni, ku nuna ma yaronku da ke shakka zane-zanen da ke kansu. Me ya sa hakan yake da kyau? Domin zane-zanen sun nuna cewa wani mai hikima ne ya yi abubuwan nan. Alal misali, akwai halittu da dama da suke da zane kamar dodon koɗi, kuma masanan kimiyya sun daɗe suna bincike a kan irin wannan zanen. Wani ɗan kimiyya mai suna Nicola Fameli ya ce idan ka ƙirga layi-layin da ke irin halittun nan kuma ka bincika su, za ka ga cewa yadda aka tsara dukansu ɗaya ne. Irin wannan tsarin ne ake kira Fibonacci sequence. Kuma za a iya ganin irin wannan tsarin a halittu da yawa kamar damin turari, da jikin dodon koɗi, da wasu ganyaye, da kuma furen sanfulawa. a

8 Wataƙila a makaranta, yaron zai koyi wasu abubuwa da suka nuna cewa halittu da dama su ma suna da yadda aka tsara su. Alal misali, akwai yadda aka tsara yawancin bishiyoyi. Akwai asalin jikin bishiyar, sai kuma manyan rassanta. Bayan haka akwai ƙananan rassa, kuma haka abin yake raguwa har a zo kan ganyen bishiyar. Ana kiran irin tsarin nan fractal pattern. Kuma za mu ga irin wannan tsarin a jikin halittu da dama. Wane ne ya yi tsarin nan da ke sa halittu su fita da kyau? Ba mamaki idan yaronku ya yi tunani mai zurfi a kan irin tambayar nan, zai ƙara gaskata cewa akwai Mahalicci. (Ibran. 3:4) Kuma idan kuna so ku taimaka masa ya ga amfanin bin dokokin Jehobah, za ku iya tambayarsa cewa: “Da yake Allah ne ya halicce mu, ba ka ganin shi ne zai iya gaya mana yadda za mu yi rayuwar da za ta sa mu farin ciki?” Sai ku gaya masa cewa abin da ya sa Allah ya ba mu Littafi Mai Tsarki ke nan.

NASA, ESA, and the Hubble Heritage (STScl/AURA)-ESA/Hubble Collaboration

Waye ne ya yi halittu da kyau da kuma tsari haka? (Ka duba sakin layi na 7-8)


KU TAIMAKI YARANKU SU GA AMFANIN BIN DOKOKIN JEHOBAH

9. Mene ne zai iya sa yaro ya tambayi iyayensa abin da ya sa Littafi Mai Tsarki ya ce kar a yi wani abu?

9 Idan ɗanku ko ꞌyarku ta tambaye ku abin da ya sa Littafi Mai Tsarki ya ce kar a yi wani abu, ku yi ƙoƙari ku san abin da ya sa. Wataƙila yana shakkar abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa ne. Wataƙila kuma bai san yadda zai bayyana wa mutane imaninsa a kan batun ba ne. Ko da mene ne dalilinsa, za ku iya taimaka masa ya ga amfanin bin dokokin Jehobah ta wurin yin nazarin littafin nan, Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada! da shi. b

10. Ta yaya za ku taimaki yaranku su yi marmarin zama abokan Jehobah?

10 Ku taimaki yaranku su yi marmarin zama abokan Jehobah. Idan kuna nazari da yaronku da littafin nan, Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada! ku yi amfani da tambayoyi da misalai da suke darasin don ku san raꞌayinsa. (K. Mag. 20:5) Alal misali, a darasi na 8 an ce Jehobah kamar abokin da yake ba mu shawarwari masu kyau ne don yana ƙaunarmu. Bayan kun tattauna abin da ke 1 Yohanna 5:3, za ku iya tambayarsa cewa, “Da yake Jehobah ba ya so wani abu ya same mu, idan ya ce kada mu yi wani abu, yaya ya kamata mu ɗauki umurninsa?” Tambaya mai sauƙi ce, amma za ta iya taimaka ma yaron ya ga cewa ƙaunar da Jehobah yake mana ne ya sa yake ba mu dokoki.—Isha. 48:17, 18.

11. Ta yaya za ku taimaki yaranku su ga amfanin bin abin da Littafi Mai Tsarki ya ce? (Karin Magana 2:10, 11)

11 Ku taimaki yaranku su ga amfanin bin abin da Littafi Mai Tsarki ya ce. Bayan kun karanta Littafi Mai Tsarki ko nassin yini, ku yi magana a kan yadda bin ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki ya amfane ku a iyalin. Alal misali, ku taimake su su ga amfanin yin aiki da ƙwazo da kuma faɗin gaskiya. (Ibran. 13:18) Za ku kuma iya bayyana musu yadda bin abin da Littafi Mai Tsarki ya ce yake inganta lafiyarmu kuma yake sa mu farin ciki. (K. Mag. 14:29, 30) Idan yaranku suka ga cewa bin abin da Littafi Mai Tsarki ya ce yana amfanar mutum, ƙila su ma za su so binsa.—Karanta Karin Magana 2:10, 11.

12. Mene Ɗanꞌuwa Steve da matarsa suke yi don su taimaki ɗansu ya ga amfanin bin abin da Littafi Mai Tsarki ya ce?

12 Wani ɗanꞌuwa mai suna Steve da matarsa suna da ɗa mai suna Ethan. Ɗanꞌuwan ya faɗi abin da suke yi don su taimaki ɗansu ya ga cewa ƙauna ce ta sa Jehobah ya ba mu dokoki. Ya ce: “Mukan tambayi ɗanmu cewa, ‘Me ya sa Jehobah yake so mu bi wannan dokar? Ba ka gani yana ƙaunar mu shi ya sa ya ba mu dokar nan? Idan muka ƙi bin abin da ya ce, me zai faru?’” Irin tattaunawar nan ya sa ɗanmu ya ga cewa abin da Jehobah ya ce shi ne ya fi dacewa. Steve ya ƙara da cewa: “Babban burinmu shi ne mu taimaki ɗanmu Ethan ya ga cewa babu abin da ya fi bin abin da Littafi Mai Tsarki ya ce.”

13. Ka ba da misalin yadda iyaye za su koya ma ɗansu yadda zai bi ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki.

13 Ku koya musu yadda za su bi ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki. Alal misali, ƙila a ce wa yaronku ya karanta wani littafi a makarantarsu. Kuma mai yiwuwa a littafin, an ba da labarin yadda wasu suka yi lalata ko mugunta, amma an ba da labarin kamar abu mai kyau ne suka yi. Idan hakan ya faru, zai yi kyau ku ce ma yaronku ya yi tunani a kan yadda Jehobah yake ɗaukan irin halayen nan. (K. Mag. 22:24, 25; 1 Kor. 15:33; Filib. 4:8) Hakan zai taimaka masa ya ga cewa bin maganar Jehobah ne ya fi. Kuma idan malaminsu ko ꞌyan ajinsu suka ce ya faɗi raꞌayinsa game da labarin, zai yi masa sauƙi ya gaya musu imaninsa.

KU KOYA MA YARANKU YADDA ZA SU BAYYANA IMANINSU

14. A wane batu ne yake yi wa ꞌyan makaranta wuya su bayyana imaninsu, kuma me ya sa?

14 Wani lokaci tsoro yakan hana yara gaya wa mutane abin da suka yi imani da shi. Musamman idan ana zancen juyin halitta a aji. Dalilin shi ne a yawancin lokuta, malaman sukan gaya wa ɗalibansu cewa koyarwar juyin halitta gaskiya ne kuma an tabbatar da shi. Ta yaya za ku taimaki yaranku su kasance da tabbaci cewa abin da suka yi imani da shi gaskiya ne?

15. Me zai taimaki yaranku ya kasance da tabbaci cewa abin da ya yi imani da shi gaskiya ne?

15 Ku taimaki yaranku su kasance da tabbaci cewa abin da suka yi imani da shi gaskiya ne. Ba abin kunya ba ne a ce mutum ya yi imani cewa Allah ne ya halicci abubuwa. (2 Tim. 1:8) Me ya sa? Domin akwai ꞌyan kimiyya da yawa da su ma suka yi imani cewa ba haka kawai abubuwa suka fito ba. Sun ga cewa halittu masu rai suna da tsari sosai kuma suna da wuyar ganewa. Don haka, sun ce lallai wani mai hikima sosai ne ya yi su. Kuma ba su yarda da koyarwar juyin halitta ba, duk da cewa ana yin ta a makarantu a faɗin duniya. Sanin hakan zai iya tabbatar wa yaranku cewa abin da suka yi imani da shi gaskiya ne. Wani abu kuma da zai taimaka musu shi ne, su tambayi wasu ꞌyanꞌuwa abin da ya tabbatar musu cewa akwai Mahalicci. c

16. Mene ne iyaye za su iya yi don su taimaki yaransu su iya bayyana imaninsa cewa akwai Mahalicci? (1 Bitrus 3:15) (Ka kuma duba hoton.)

16 Ku taimaki yaranku su iya bayyana ma wasu imaninsu cewa akwai Mahalicci. (Karanta 1 Bitrus 3:15.) Za ku iya taimaka wa yaronku ta wurin tattauna wasu talifofi a jerin talifofi mai jigo, “Tambayoyin Matasa—Halitta ko Raꞌayin Bayyanau?” da ke jw.org/ha. Sai ku bar yaron ya zaɓi bayanin da yake gani zai fi saurin sa mutane su ga cewa akwai Mahalicci. Bayan haka, ku sa shi ya gwada yadda zai bayyana batun. Ku gaya masa cewa kada ya yi gardama da ꞌyan ajinsu. Kuma idan ya sami wanda zai saurare shi, ku gaya masa ya yi bayani mai sauƙin fahimta. Alal misali, idan ɗan ajinsu ya ce: “Ba na yin imani da abin da ban gani ba, kuma ban taɓa ganin Allah ba.” Yaron zai iya gaya masa cewa: “A ce kana tafiya a cikin dajin Allah kuma ka ga rijiya da aka gina bakinsa da duwatsu. Me za ka ce? Ai za ka ce wani ne ya haƙa rijiyar, ko ba haka ba? Ballantana mu mutane da duk duniyar dan da muke ciki, ai dole akwai wanda ya yi mu!”

Idan kana magana da ꞌyan ajinku game da imaninka, ka yi bayani mai sauƙin fahimta (Ka duba sakin layi na 16-17) d


17. Mene ne iyaye za su iya yi don su taimaki yaransu su riƙa neman yadda za su yi waꞌazi? Ka ba da misali.

17 Ku taimaki yaranku su riƙa neman yadda za su yi waꞌazi. (Rom. 10:10) Za ku iya gaya musu cewa yin waꞌazi kamar koyan buga ganga ne, ko wani abin kiɗa. Mai koyon yakan fara da kiɗa mai sauƙi ne. Saꞌan nan a-kwana-a-tashi zai saɓa kuma ya ƙware. Haka ma, idan yaro yana so ya yi waꞌazi, zai soma ne da yin bayani mai sauƙi. Alal misali, yaronku zai iya tambayar ɗan ajinsu cewa: “Ka san cewa masu ƙera abubuwa sukan dubi wasu halittun Allah ne sai su yi nasu? Bari in nuna maka wani bidiyo mai burgewa.” Sai ya nuna masa wani bidiyo daga bidiyoyi masu jigon nan, Halittarsa Aka Yi? kuma ya ce: “Ana yabon ꞌyan kimiyya da suka kwaikwayi abin da Allah ya halitta. To wa ya kamata a yaba wa don halittun nan da muke gani?” Ƙila hakan zai sa ɗan ajinsu ya so koyan wasu abubuwa kuma game da Jehobah.

KU CI-GABA DA TAIMAKON YARANKU SU ƘARA BA DA GASKIYA

18. Ta yaya iyaye za su ci-gaba da taimakon yaransu su ƙara ba da gaskiya ga Allah?

18 Yawancin mutane a yau ba su gaskata da Jehobah ba. (2 Bit. 3:3) Don haka idan kuna nazari da yaranku, ku ƙarfafa su su riƙa bincika batutuwa da za su sa su ƙara son Kalmar Allah da dokokinsa. Ku taimaki yaranku su yi tunani ta wurin yin zancen halittun Jehobah masu ban mamaki da su. Ku taimaka musu su fahimci annabce-annabcen Littafi Mai Tsarki da suka cika. Mafi muhimmanci kuma, ku riƙa yin adduꞌa da su, kuma ku riƙa sa su cikin adduꞌa. Ba shakka idan kuka yi haka, Jehobah zai sa albarka a ƙoƙarin da kuke yi don ku taimaki yaranku su zama masu bangaskiya sosai.—2 Tar. 15:7.

WAƘA TA 133 Mu Bauta wa Jehobah da Kuruciyarmu

a Don samun ƙarin bayani, ka kalli bidiyon nan The Wonders of Creation Reveal God’s Glory, a jw.org.

b Idan yaron ya riga ya gama nazarin littafin nan, Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada! za ku iya sake duba wasu darussa a sashe na 3 da na 4, da suka bayyana ƙaꞌidodin Jehobah.

c Ka ga talifin nan Why We Believe in a Creator da ke Awake! na Satumba 2006, da ƙasidar nan, The Origin of Life—Five Questions Worth Asking. Don samun wasu misalai kuma, ka kalli bidiyoyin da ke jerin bidiyoyi mai jigo, Viewpoints on the Origin of Life a jw.org.

d BAYANI A KAN HOTO: Wani yaro yana nuna wa ɗan ajinsu wani bidiyo daga jerin bidiyoyi mai jigo, Halittarsa Aka Yi? don ya ga cewa ɗan ajin nasu yana son naꞌurar drone.