Ka Sani?
Me ya sa ya yi kyau da Jehobah ya yarda Isra’ilawa su ba da hadaya da tsuntsaye iri biyu?
A ƘARƘASHIN Dokar da Aka Bayar ta Hannun Musa, Jehobah ya yarda Isra’ilawa su ba da hadaya da kurciyoyi da kuma tattabaru. Akan ambata tsuntsayen nan tare a dukan dokoki da aka bayar game da hadaya, kuma za a iya ba da ɗaya maimakon ɗayan. (L. Fir. 1:14; 12:8; 14:30) Me ya sa hakan yake da amfani? Dalili ɗaya shi ne domin ba a kowane lokaci ne ake samun kurciyoyi ba. Me ya sa?
Kurciyoyi tsuntsaye ne da suke ƙaura kuma lokacin zafi ne kawai ake samun su a ƙasar Isra’ila. A kowane watan Oktoba, suna ƙaura kudu zuwa ƙasashen da ake zafi kuma su dawo Isra’ila a lokacin damina. (W. Waƙ. 2:11, 12; Irm. 8:7) Hakan yana nufi cewa a zamanin dā a Isra’ila, yana da wuya mutum ya ba da hadayar kurciya a lokacin sanyi.
Amma tattabaru ba sa ƙaura. Domin haka, ana iya samun su a kowane lokaci a Isra’ila. Ban da haka, ana kiwon tattabaru. (Ka duba misalin da ke Yohanna 2:14, 16.) Littafin nan Bible Plants and Animals ya ce: “Ana kiwon tattabaru a kowane ƙauye da gari a yankin Falasdinu. Kowane mai gida yana da gidan tattabaru ko kuma rami a bango da tsuntsayen suke zama.”—Ka duba misalin da ke Ishaya 60:8.
Jehobah ya nuna cewa shi mai ƙauna ne da kuma sanin yakamata ta wajen amincewa Isra’ilawa su ba da hadayar tsuntsaye da za a iya samu a kowane lokaci a cikin shekara.