Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 8

WAƘA TA 130 Mu Riƙa Gafartawa

Me Za Ka Yi don Ka Zama Mai Gafartawa Kamar Jehobah?

Me Za Ka Yi don Ka Zama Mai Gafartawa Kamar Jehobah?

“Ku gafarta masa kamar yadda Ubangiji ya gafarta muku zunubanku.”KOL. 3:13.

ABIN DA ZA MU KOYA

A wannan talifin za mu tattauna matakan da za su taimaka mana mu iya gafarta ma wanda ya yi mana laifi.

1-2. (a) Mene ne zai iya sa ya yi mana wuya mu gafarta wa mutum? (b) Ta yaya Denise ta nuna halin gafartawa?

 YANA maka wuya ka yafe wa mutum? Yafewa yana wa mutane da yawa wuya, musamman idan mutum ya yi abin da ya ɓata mana rai sosai. Amma, akwai wasu abubuwan da za mu iya yi don mu daina fushi kuma mu yafe wa mutane. Wata ꞌyarꞌuwa mai suna Denise a ta yafe wani babban laifi da aka yi mata. A 2017, Denise da maigidanta da yaransu sun ziyarci Hedkwatar Shaidun Jehobah. Da suke komawa gida, sai wani direba ya zo ya yi karo da su, kuma nan take Denise ta sume. Bayan da ta farfaɗo, sai ta ji cewa yaransu sun ji ciwo sosai, kuma maigidanta mai suna Brian ya rasa ransa a wannan hatsarin. Denise ta ce: “Na rikice, kuma na yi baƙin ciki sosai.” Daga baya ta ji cewa direban bai sha wani abin maye (wato, abin da ke sa buguwa) ba, kuma ba wai yana danna waya ko yana wani abin da zai raba hankalinsa ba ne. Sai ta roƙi Jehobah ya kwantar mata da hankali don kar ta yi fushi da mutumin.

2 An kama direban, kuma aka kai shi kotu don ya yi kisa. Idan kotu ya kama shi da wannan laifin, za a ƙulle shi a gidan yari. Kotun ya gaya wa Denise cewa za a yanke hukunci ne bisa ga abin da ta faɗa. Denise ta ce: “Da aka ta da wannan batun, na ji kamar an zuba min gishiri ne a ciwon da nake fama da shi, don wannan ne abu mafi muni da ya taɓa faruwa da ni kuma ana so in yi magana a kai.” ꞌYan makonni bayan haka, Denise ta je kotun don ta faɗi raꞌayinta game da abin da mutumin ya yi mata da ꞌyan iyalinta. Ka san abin da ta ce? Denise ta ce alƙalin ya yi wa mutumin jinƙai. b Da ta gama bayaninta, sai alƙalin ya fashe da kuka, kuma ya ce: “Na yi shekaru 25 ina aikin alƙali, amma ban taɓa ganin irin wannan abin ba. Ban taɓa jin wanda aka yi wa laifi yana roƙo a yi wa mai laifin jinƙai ba. Ban taɓa jin kalamai da suka nuna ƙauna da gafartawa irin wannan ba.”

3. Me ya taimaka wa Denise ta yafe wa mutumin?

3 Me ya taimaka wa Denise ta yafe wa mutumin? Ta yi tunani a kan yadda Jehobah yake gafartawa. (Mik. 7:18) Idan muna jin daɗin yadda Jehobah yake gafarta mana, hakan zai sa mu riƙa gafarta wa mutane.

4. Mene ne Jehobah yake so mu yi? (Afisawa 4:32)

4 Jehobah yana so mu riƙa gafarta wa mutane kamar yadda yake gafarta mana. (Karanta Afisawa 4:32.) Yana so mu kasance a shirye don mu gafarta ma waɗanda suka yi mana laifi. (Zab. 86:5; Luk. 17:4) A talifin nan, za mu tattauna abubuwa uku da za su taimaka mana mu daɗa zama masu gafartawa.

KADA KA YI KAMAR BA ABIN DA YA FARU

5. Bisa ga Karin Magana 12:18, yaya muke ji idan wani ya ɓata mana rai sosai?

5 Wani lokaci abin da aka yi mana zai dame mu sosai, musamman idan abokinmu ko wani a iyalinmu ne ya yi mana laifin. (Zab. 55:12-14) Wataƙila ranmu ya ɓace har mu ji kamar an soke mu da wuka. (Karanta Karin Magana 12:18.) Za mu iya yi kamar ba abin da ya faru. Amma hakan kuskure ne, don zai zama kamar an soke mu da wuka, kuma muka bar wukar a jikinmu. Hakika, idan ba mu ɗauki mataki ba, abin da aka yi mana zai ci-gaba da daminmu.

6. Mene ne za mu iya yi idan wani ya ɓata mana rai?

6 Idan wani ya ɓata mana rai, wataƙila mu yi fushi. Littafi Mai Tsarki ya ce hakan yana iya faruwa. Amma ya ce kada mu ci-gaba da yin fushi. (Zab. 4:4; Afis. 4:26) Me ya sa? Domin fushi yana sa mu yi saurin ɗaukan matakin da bai dace ba. (Yak. 1:20) Mu tuna cewa idan aka mana laifi, wani lokaci dole mu yi fushi, amma ba dole ne mu ci-gaba da yin fushi da mutumin ba.

Wani lokaci dole mu yi fushi, amma ba dole ba ne mu ci-gaba da yin fushi da mutumin

7. Idan aka ɓata mana rai, yaya hakan zai iya shafanmu?

7 Idan aka wulaƙanta mu, hakan zai iya shafanmu a hanyoyi dabam-dabam. Alal misali, wata ꞌyarꞌuwa mai suna Ann ta ce: “Da nake ƙarama, mahaifina ya rabu da mahaifiyata kuma ya auri ꞌyar aikin gidanmu. Hakan ya sa na ji kamar ba wanda ya damu da ni. Da suka haifi yara, na ji kamar ni ba ꞌyarsu ba ce. Na daɗe ina ji kamar ba wanda yake son ganina.” Wata ꞌyarꞌuwa mai suna Georgette ta bayana yadda ta ji da maigidanta ya yi zina kuma hakan ya sa sun rabu. Ta ce: “Mu abokai ne tun muna yara, kuma mun yi hidimar majagaba tare. Don haka, abin ya dame ni sosai!” Wata ꞌyarꞌuwa kuma mai suna Naomi ta ce: “Ban taɓa tsammani cewa maigidana zai yi abin da zai yi mini zafi sosai haka ba. Saboda haka, da ya gaya min cewa yana kallon batsa a ɓoye, na ji kamar ya ci amanata.”

8. (a) Waɗanne dalilai ne suka sa yake da kyau mu yafe wa mutane? (b) Ta yaya za mu amfana idan muka yafe? (Ka duba akwatin “ Me Za Mu Yi Idan Wani Ya Yi Abin da Ya Dame Mu Sosai?”)

8 Mutane za su ci-gaba da yi mana laifi, kuma ba za mu iya hana hakan faruwa ba, amma mu ne za mu zaɓi yadda za mu bi da yanayin. A yawancin lokuta, abin da ya fi alheri shi ne mu yafe. Me ya sa? Don muna ƙaunar Jehobah, kuma yana so mu riƙa yafewa. Ƙari ga haka, idan muka ci-gaba da yin fushi, ba wuya mu yi abin da bai kamata ba, kuma mu cutar da kanmu. (K. Mag. 14:17, 29, 30) Alal misali, wata ꞌyarꞌuwa mai suna Christine ta ce: “Idan ina fushi ko wani ya ɓata min rai, da wuya in yi murmushi. Sai in riƙa cin abincin da ba ya gina jiki da kyau. Wani lokaci barci ya gagare ni, ƙaramin abu yakan tayar min da hankali, kuma hakan yana shafan dangantakata da maigidana da kuma wasu mutane.”

9. Me ya sa yake da kyau mu daina fushi da wanda ya yi mana laifi?

9 Ko da wanda ya yi mana laifi ya ƙi ya ba mu haƙuri, akwai abin da za mu iya yi don mu ji sauƙi. Me ke nan? Georgette, da aka ambata ɗazu ta ce: “A-hankali-a-hankali, na yi ƙoƙari na daina fushi da maigidana da muka rabu. Hakan ya sa na sami kwanciyar hankali.” Idan muka daina fushi, hakan zai taimaka mana mu iya yi wa mutane kirki. Kuma hakan zai zama alheri a gare mu, domin za mu daina tunani a kan batun kuma mu ji daɗin rayuwarmu. (K. Mag. 11:17) Amma idan kana ganin ba za ka iya yafe wa mutumin yanzu ba, me zai taimaka maka?

YADDA ZA KA DAINA FUSHI

10. Me ya sa yake da kyau mu ba wa kanmu lokaci don mu daina yin fushi da wanda ya yi mana laifi? (Ka kuma duba hotunan.)

10 Me zai taimaka maka ka daina yin fushi? Wataƙila kana bukatar lokaci. Idan mutum ya ji rauni, kuma aka kula da shi a asibiti, yana bukatar lokaci don ya warke. Mu ma idan aka mana laifi, mai yiwuwa za mu bukaci lokaci kafin mu iya yafe wa mutumin daga zuciyarmu.—M. Wa. 3:3; 1 Bit. 1:22.

Idan mutum ya ji rauni, kuma aka kula da shi a asibiti, yana bukatar lokaci don ya warke. Mu ma za mu bukaci lokaci kafin mu iya yafe wa mutum (Ka duba sakin layi na 10)


11. Ta yaya adduꞌa zai taimaka maka ka zama mai gafartawa?

11 Ka roƙi Jehobah ya taimake ka ka zama mai yafewa. c Abin da ya taimaka wa Ann da aka ambata ɗazu ke nan. Ta ce: “Na roƙi Jehobah ya yafe wa dukanmu a iyalin don abubuwan da muka yi da ba daidai ba. Bayan haka, sai na rubuta wa babana da amaryarsa wasiƙa, na gaya musu cewa na yafe musu.” Ann ta ce hakan bai yi mata sauƙi ba ko kaɗan. Amma ta ce: “Ina ƙoƙari in zama mai gafartawa kamar Jehobah. Kuma ina fatan cewa hakan zai sa babana da matarsa su so koyan abubuwa game da Jehobah.”

12. Me ya sa ya kamata mu bi abin da Jehobah ya ce maimakon raꞌayinmu? (Karin Magana 3:5, 6)

12 Ka bi abin da Jehobah ya ce, kada ka bi raꞌayinka. (Karanta Karin Magana 3:5, 6.) A koyaushe, Jehobah ya san abin da zai fi amfanar mu. (Isha. 55:8, 9) Ba zai taɓa gaya mana mu yi abin da zai cutar da mu ba. Da yake Jehobah ya ce mu zama masu gafartawa, ba shakka yin hakan zai amfane mu. (Zab. 40:4; Isha. 48:17, 18) Amma idan mun bi raꞌayinmu, wataƙila ba za mu taɓa yafewa ba. (K. Mag. 14:12; Irm. 17:9) Naomi, da aka ambata ɗazu ta ce: “Da farko, na gaya wa kaina cewa bai kamata in yafe wa maigidana don yadda yake kallon batsa ba. Na ɗauka cewa idan na yafe masa, zai koma gidan jiya, ko ya manta cewa abin da ya yi ya ɓata min rai sosai. Kuma na yi ta ce wa kaina Jehobah ma ya fahimce ni. Amma na zo na gane cewa ko da yake Jehobah ya fahimci yadda nake ji, hakan ba ya nufin cewa abin da nake yi ya dace. Jehobah ya san cewa abin ya dame ni kuma zai ɗau lokaci kafin in huce. Duk da haka, yana so in yafe.” d

KA KASANCE DA RAꞌAYI MAI KYAU

13. Bisa ga Romawa 12:18-21, me ya kamata mu yi?

13 Bai kamata mu yafe don kawai a bar zancen ba. Idan wanda ya yi mana laifi ɗanꞌuwa ne ko ꞌyarꞌuwa a cikin ikilisiya, bayan mun yafe masa, ya kamata mu dawo da zumuncin da ke tsakaninmu. (Mat. 5:23, 24) Maimakon mu ci-gaba da fushi, mu tausaya wa mutumin kuma mu gafarta masa. (Karanta Romawa 12:18-21; 1 Bit. 3:9) Me zai taimaka mana mu yi haka?

14. Me ya kamata mu yi ƙoƙarin yi, kuma me ya sa?

14 Mu yi ƙoƙari mu kasance da raꞌayin Jehobah game da wanda ya yi mana laifi. Jehobah ya fi mai da hankali ga abubuwa masu kyau da mutane suke yi. (2 Tar. 16:9; Zab. 130:3) Idan muka mai da hankali ga abubuwa masu kyau da mutum yake yi, za mu ga ƙoƙarinsa. Amma idan kurakuransa muke nema, abin da za mu riƙa gani ke nan. Idan muna ƙoƙarin ganin halayen mutane masu kyau, zai yi mana sauƙi mu gafarta musu. Alal misali, wani ɗanꞌuwa mai suna Jarrod ya ce, “Yana min sauƙi in gafarta wa ɗanꞌuwa idan na yi tunani a kan abubuwa masu kyau da yake yi maimakon kurakurensa.”

15. Me ya sa wani lokaci yana da muhimmanci mu gaya wa mutum cewa mun yafe masa?

15 Wani abu mai muhimmanci kuma da zai taimaka maka shi ne, ka gaya wa mutumin cewa ka yafe masa. Naomi da muka ambata a baya ta ɗauka ta riga ta yafe wa maigidanta. Amma ga abin da ta ce: “Saꞌad da maigidana ya tambaye ni cewa, ‘Kin yafe mini?’ Na buɗe baki zan ce masa, ‘na yafe maka,’ amma sai na gagara. A lokacin ne na gane cewa ban riga na yafe masa daga zuciyata ba. Da shigewar lokaci, na iya na gaya wa maigidana cewa na yafe masa. Jin hakan ya sa maigidana ya zub da hawaye. Na yi mamakin irin sauƙin da ya ji a ransa, da irin kwanciyar hankalin da ni ma na samu. Tun daga wannan lokacin, na fara yarda da maigidana, kuma yanzu mun zama aminai.”

16. Mene ne ka koya game da gafartawa?

16 Jehobah yana so mu riƙa gafartawa. (Kol. 3:13) Amma zai iya mana wuya mu yafe wa mutane. Duk da haka, idan mun yi ƙoƙari mun daina yin fushi, kuma ba mu yi kamar ba abin da ya faru ba, za mu iya yafewa. Hakan zai taimaka mana mu kasance da raꞌayi mai kyau game da mutane.—Ka duba akwatin da ya ce, “ Abubuwa Uku da Za Su Taimaka Mana Mu Yafe.”

KA YI TUNANI A KAN AMFANIN GAFARTAWA

17. Ta yaya muke amfana idan muka gafarta wa mutane?

17 Muna da dalilai da dama da za su sa mu gafarta. Ga wasu daga cikinsu: Na ɗaya, hakan zai nuna cewa muna koyi da Jehobah Ubanmu mai tausayi, kuma zai faranta masa rai. (Luk. 6:36) Na biyu, zai nuna cewa muna godiya don yadda Jehobah yake gafarta mana. (Mat. 6:12) Na uku kuma shi ne, zai inganta lafiyarmu, kuma zai ƙara danƙon zumunci da ke tsakaninmu da mutane.

18-19. Mene ne zai iya faruwa idan muka yafe ma wanda ya yi mana laifi?

18 Yafewa zai iya kawo sakamakon da ba mu yi tsammani ba. Abin da ya faru da Denise da muka ambata ɗazu ke nan. Ashe direban da ya yi karo da su yana shirin kashe kansa bayan an yanke masa hukunci. Amma da Denise ta yafe masa, ya yi mamaki sosai har ya soma nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidun Jehobah.

19 Wani lokaci mukan ji kamar ba abin da yake da wuya kamar yafewa. Amma yafewa zai iya zama abu mafi alheri a gare mu. (Mat. 5:7) Don haka, bari kowannenmu ya yi iya ƙoƙarinsa ya zama mai gafartawa kamar Jehobah.

WAƘA TA 125 Masu Jinƙai Suna Farin Ciki!

a An canja wasu sunayen.

b A irin wannan yanayin, kowane Kirista ne zai zaɓi abin da zai yi.

c Ka kalli bidiyoyin waƙoƙin nan, “Ku Rika Gafartawa,” da “Mu Sasanta,” da kuma Forgive One Another,” a dandalin jw.org/ha.

d Ko da yake kallon batsa zunubi ne kuma yakan dami maꞌaurata sosai idan ɗayansu ya yi hakan, amma Littafi Mai Tsarki bai ce za su iya kashe aurensu idan ɗaya daga cikinsu yana kallon batsa ba.