Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ka Sani?

Ka Sani?

Me ya nuna cewa yin waƙa yana da muhimmanci a ƙasar Israꞌila a dā?

YIN WAƘA yana cikin ayyukan alꞌadar Israꞌilawa a dā. Akwai wurare da dama da Littafi Mai Tsarki ya ambaci masu yin waƙa da masu kiɗa. Wajen kashi goma cikin ɗari na Littafi Mai Tsarki ma, waƙoƙi ne. Waɗanda aka fi sani su ne littafin Zabura, da Waƙar Waƙoƙi da kuma littafin Makoki. Shi ya sa wani littafi da ya yi bayani a kan Littafi Mai Tsarki ya ce, Israꞌilawa sukan yi waƙoƙi saꞌad da suke yin abubuwa da dama a rayuwarsu.

Saꞌad da suke ayyukansu na yau da kullum. Israꞌilawa sukan yi amfani da waƙa don su nuna farin cikinsu ko baƙin ciki. (Isha. 30:29) Mata sukan kaɗa tambura suna waƙa da rawa idan ana biki, ko ana naɗa sarki, ko kuma an ci nasara a yaƙi. (Alƙa. 11:34; 1 Sam. 18:​6, 7; 1 Sar. 1:​39, 40) Ƙari ga haka, Israꞌilawa sukan yi waƙar nuna baƙin ciki idan wani ya rasu. (2 Tar. 35:25) A bayyane yake cewa Israꞌilawa suna son waƙoƙi ba kaɗan ba.

A fadar sarki. Sarakunan Israꞌila suna son waƙoƙi. Alal misali, Sarki Shawulu ya sa a kawo Dauda fadarsa ya riƙa masa kiɗa da waƙa. (1 Sam. 16:​18, 23) Daga baya da Dauda ya zama sarki, ya ƙera kayan kiɗa, ya rubuta waƙoƙi masu daɗi, kuma ya tsara yadda za a riƙa yin kiɗa da waƙa a haikalin Jehobah. (2 Tar. 7:6; Amos 6:5) Sarki Sulemanu shi ma yana da maza da mata da suke masa waƙa a fadarsa.—M. Wa. 2:8.

A lokacin ibada. Abu mafi muhimmanci da Israꞌilawa sukan yi da waƙa shi ne ibada. Maza da suke yin kiɗa a haikalin da ke Urushalima sun kai 4,000, kuma dukansu kwararru ne. (1 Tar. 23:5) Sukan yi amfani da kuge, da molo, da giraya, da kuma kakaki. (2 Tar. 5:12) Amma ba su kaɗai ba ne suke amfani da waƙa wajen bauta wa Allah. Israꞌilawa da yawa sukan rera Waƙoƙin Haurawa Zuwa Sujada (wato, Hallel Psalms) idan za su je yin bukukuwa a Urushalima kowace shekara. (Zab. 120–134) Kuma tarihin Israꞌilawa ya nuna cewa, sukan rera wasu waƙoƙi da ke littafin Zabura a a lokacin bikin Idin Ƙetarewa.

A yau ma, waƙa tana da muhimmanci a gun bayin Allah. (Yak. 5:13) Muna yabon Jehobah da waƙoƙi. (Afis. 5:19) Kuma yin waƙa tare da ꞌyanꞌuwanmu yana ƙara mana dankon zumunci. (Kol. 3:16) Idan muna cikin hali mai wuya, yin waƙa yakan ƙarfafa mu. (A. M. 16:25) Ba shakka, yin waƙa hanya ce mai kyau ta nuna bangaskiyarmu da ƙaunarmu ga Jehobah.

a Israꞌilawa sukan rera waƙoƙi da ke Zabura ta 113 zuwa 118 don su yabi Jehobah.