Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shin ya kamata mu riƙa dogara ga raꞌayinmu?

Abin da Ke Sa Mutane Su Yanke Shawara

Abin da Ke Sa Mutane Su Yanke Shawara

Kusan dukan mutane sun yarda cewa wasu abubuwa sun dace ko kuma ba su dace ba. Alal misali, a faɗin duniya mutane suna ganin yin kisa da fyaɗe da cin zarafin yara ba su dace ba. Kuma mutane suna yaba wa mai adalci da alheri da kuma mai tausayi. Amma a wasu batutuwa kamar jimaꞌi da faɗin gaskiya da kuma renon yara, mutane da yawa suna ganin kowa zai iya yin abin da ya ga ya dace. Ƙari ga haka, suna ganin duk abin da mutum ya zaɓa ya yi daidai ne. Mutane sukan yanke shawarwari bisa ga yadda suke ji da kuma bisa raꞌayin mutane da ke kusa da su. Amma hakan ya dace ne?

RAꞌAYINMU

Mukan tsai da shawarwari a zuciyarmu bisa ga yadda muke ji game da abin da ya dace da abin da bai dace ba. (Romawa 2:​14, 15) Ko yara ƙanana ma, sun san abin da bai dace ba, kuma zuciyarsu takan dame su idan suka yi abu marar kyau. Yayin da muke girma, mukan koya abin da ya dace da abin da bai dace ba daga mutanen da muke cuɗanya da su. Mutane kamar iyalanmu da tsaranmu da malamanmu da yankinmu da kuma addininmu. Saꞌad da muka tsai da shawarwari, zuciyarmu takan gaya mana ko zaɓin da muka yi ya jitu da raꞌayinmu ko aꞌa.

Sanin abin da ya dace da abin da bai dace ba zai iya sa mu riƙa damuwa da mutane da nuna musu godiya da yin adalci da kuma tausaya musu. Hakan kuma zai hana mu yin abubuwan da za su sa waɗanda muke ƙauna baƙin ciki, ko kuma abubuwan da za su kunyantar da mu da kuma sa mu ji kamar muna da laifi.

Shin ya kamata mu riƙa dogara ga raꞌayinmu? Saꞌad da wani mai suna Garrick yake matashi, ya ce: “Zan iya yin duk abin da nake so.” Amma ya gano cewa yin abin da yake gani ya dace ya jawo masa mummunar sakamako. Bai yi farin ciki da irin rayuwa da ya yi ba, domin ya zama “mai lalata, ɗan ƙwaya da mashayi da kuma mai aikata mugunta.”

RAꞌAYIN MUTANE

Ban da yadda muke ji, mukan damu da yadda mutane za su ji game da shawarwarin da muke yankewa. Hakan zai taimaka mana mu amfana daga hikimarsu da kuma abin da ya faru da su a rayuwa. Idan muka yi abin da iyalanmu da abokanmu da mutane da ke yankinmu suke ganin ya dace, hakan zai sa su riƙa daraja mu.

Shin ya kamata mu riƙa dogara ga raꞌayin mutane? Saꞌad da wata mai suna Priscila take matashiya, ta yi abubuwan da matasa da yawa suke yi har da yin lalata. Ta gano cewa, ko da yake tana yin abubuwan da mutane suke ganin ba laifi, hakan bai sa ta farin ciki ba. Ta ce: “Yin abin da kowa yake yi bai sa na ji daɗin rayuwata ba. Ya sa na jefa rayuwata cikin matsala kamar wata wawiya.”

TA YAYA ZA MU TSAI DA SHAWARWARI MASU KYAU?

Saꞌad da muke tsai da shawara a rayuwa, raꞌayinmu da na mutane yana da muhimmanci. Amma dogara ga raꞌayinmu da na mutane ba kowane lokaci ba ne yake kawo sakamako mai kyau. A wasu lokuta, mukan jawo wa kanmu da kuma wasu baƙin ciki domin ba mu san abin da zaɓinmu zai jawo mana ba. (Karin Magana 14:12) Ko da mu da wasu muna ganin cewa wani zaɓin da muka yi ya dace, zaɓin zai iya jefa mu cikin matsala, kuma daga baya raꞌayoyin za su iya canjawa. A yanzu ma, ana amincewa da wasu abubuwa da ake ganin ba su da kyau a dā, kuma wasu halaye da ake ganin ba su da laifi a dā, yanzu ana ganin ba su dace ba kuma.

Shin bin raꞌayin mutane saꞌad da muke tsai da shawara zai taimaka mana?

Shin akwai abin da zai fi taimaka mana don yanke shawara game da abin da ya dace da abin da bai dace ba? Shin akwai ƙaꞌidodin da za mu iya bi a yau da ba za su sa mu yi da-na-sani ba a nan gaba?

Abin farin ciki shi ne, akwai wani da zai gaya wa kowa da ke koꞌina a koyaushe abin da ke daidai da abin da ba daidai ba. A talifi na gaba, za a tattauna wurin da za mu sami abin da zai taimaka mana mu san da kuma tsai da shawara game da abin da ya dace da abin da bai dace ba.