Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ka Ci-gaba da Jira!

Ka Ci-gaba da Jira!

“Ka jira shi, ko da ka ga kamar yana jinkiri.”—HAB. 2:3, Littafin Mai Tsarki.

WAƘOƘI: 128, 45

1, 2. Wane hali ne aka san bayin Jehobah da shi tun da daɗewa?

TUN da daɗewa, an san bayin Jehobah da jiran cikar annabcin Littafi Mai Tsarki. Alal misali, Irmiya ya annabta cewa Babiloniyawa za su halaka Yahuda kuma hakan ya faru a shekara ta 607 kafin haihuwar Yesu. (Irm. 25:8-11) Ta ja-gorar ruhu mai tsarki, Ishaya ya annabta cewa Jehobah zai sa Yahudawa da suke zaman bauta su koma ƙasarsu, kuma ya ce: “Masu-albarka ne dukan waɗanda ke sauraronsa.” (Isha. 30:18) Mikah da ya yi annabci game da mutanen Allah ya ce: “Zan jira Allah na cetona.” (Mi. 7:7) Ƙari ga haka, bayin Allah sun yi shekaru aru-aru suna jiran cikar annabcin da suka shafi Almasihu ko kuma Kristi.—Luk. 3:15; 1 Bit. 1:10-12. *

2 Bayin Jehobah na zamani suna jiran cikar annabci game da Mulkin Allah. Yesu ne Sarkin kuma zai kawo ƙarshen wahala ta wajen halaka mugayen mutane da kuma ceton mutanensa daga wannan mugun zamani da Shaiɗan yake mulki. (1 Yoh. 5:19) Saboda haka, bari mu kasance a faɗake da yake mun san cewa wannan zamanin yana gab da zuwa ƙarshensa.

3. Wane tunani ne za mu iya yi idan mun yi shekaru da yawa muna jiran zuwan ƙarshen zamani?

3 Muna son mu ga lokacin da za a yi nufin Allah a “duniya, kamar yadda ake yinsa cikin sama.” (Mat. 6:10) Amma, idan mun yi shekaru da yawa muna jiran ƙarshen wannan zamani, wasu za su iya soma tunani ko ya dace mu ci-gaba da jiran zuwan ƙarshen wannan zamani. Shin muna da dalilai masu kyau na yin haka? Bari mu gani.

ME YA SA YA DACE MU SA RAI CEWA ƘARSHEN ZAI ZO BA DA DAƊEWA BA?

4. Wane dalili mai kyau ne muke da shi na yin tsaro?

4 Littafi Mai Tsarki ya bayyana dalla-dalla abin da ya kamata mu yi a wannan lokacin da muke gab da ƙarshen zamani. Yesu ya gaya wa mabiyansa cewa su ci-gaba da ‘yin tsaro.’ (Mat. 24:42; Luk. 21:34-36) Hakan, dalili mai kyau ne na yin tsaro. Ƙari ga haka, ƙungiyar Jehobah ta ci-gaba da tanadar mana da littattafai da ke taimaka mana mu ci-gaba da “sauraron ranar Allah” da kuma sa rai ga sabuwar duniya da Allah ya yi mana alkawari.—Karanta 2 Bitrus 3:11-13.

5. Me ya sa yake da muhimmanci mu yi tsaro?

5 Kiristoci na ƙarni na farko sun yi zaman jiran ƙarshen zamani kuma hakan ya nuna cewa yana da muhimmanci sosai a yau mu yi zaman jiran ƙarshen zamani. Me ya sa? Domin alama ta nuna cewa tun shekara ta 1914, Yesu ya soma sarauta kuma muna kwanaki na ƙarshe. Wannan alamar ta haɗa da yanayin duniya da ke daɗa muni da kuma wa’azin bishara ta Mulki da ake yi a faɗin duniya kuma hakan ya nuna cewa muna rayuwa a “cikar zamani.” (Mat. 24:3, 7-14) Da yake Yesu bai faɗi lokacin da kwanaki na ƙarshe za su ƙare ba, ya kamata mu kasance a shirye kuma mu yi tsaro.

6. Ta yaya muka san cewa yanayin duniya zai ƙara taɓarɓarewa yayin da ƙarshen zamani yake gabatowa?

6 Za mu iya yin tunani cewa “cikar zamani” yana nufin wani lokaci a nan gaba da yanayin duniya zai ƙara taɓarɓarewa. Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa mugunta za ta daɗa ƙaruwa a “kwanaki na ƙarshe.” (2 Tim. 3:1, 13; Mat. 24:21; R. Yoh. 12:12) Saboda haka, mun san cewa yanayin duniya zai ci-gaba da daɗa muni.

7. Mene ne Matta 24:37-39 suka faɗa game da yanayin duniya a kwanaki na ƙarshe?

7 Amma, yaya kake ganin yanayin duniya zai kasance kafin ‘babban tsanani,’ wato ƙunci mai-girma? (R. Yoh. 7:14) Shin kana ganin za a yi yaƙi da rashin abinci da cuta a kowace ƙasa kuma waɗannan bala’o’i za su shafi kowace iyali? Idan hakan ya faru, kowa zai san cewa annabcin Littafi Mai Tsarki yana cika, har da masu shakka ma. Amma Yesu ya ce yawancin mutane za su mai da hankalin ga hidimominsu na yau da kullum kuma ba za su san cewa ya soma sarauta a sama ba. (Karanta Matta 24:37-39.) Saboda haka, Littafi Mai Tsarki ya ce yanayin duniya a kwanaki na ƙarshe ba zai yi muni sosai da zai sa mutane a ko’ina su amince cewa ƙarshen ya kusa ba.—Luk. 17:20; 2 Bit. 3:3, 4.

8. Mene ne waɗanda suke ‘yin tsaro’ kamar yadda Yesu ya faɗa za su sani?

8 Amma, waɗanda suka ci-gaba da ‘yin tsaro’ kamar yadda Yesu ya umurta za su san ma’anar alamar da ya bayar game da kwanaki na ƙarshe. (Mat. 24:27, 42) Hakan ya faru tun shekara ta 1914. Tun daga lokacin, fannonin alamar suna cika. A bayyane yake cewa yanzu muna rayuwa a “cikar zamani,” wato wani gajeren lokaci da zai kai ga halakar wannan mugun zamanin.

9. Waɗanne dalilai ne suka sa muke jiran ƙarshen wannan zamani?

9 Tun da haka ne, me ya sa ya kamata mu ci-gaba da jira? Domin muna bin umurnin Yesu. Ƙari ga haka, mun san cewa Yesu ya soma sarauta. Mun san cewa ƙarshen ya kusa ba don mun amince da duk abin da mutane suke faɗa ba, amma don Littafi Mai Tsarki ya nuna hakan kuma shi ya sa muke yin tsaro kuma muna zaman jira.

HAR YAUSHE?

10, 11. (a) Me ya sa Yesu ya gaya wa almajiransa su ci-gaba da ‘yin tsaro’? (b) Mene ne Yesu ya gaya wa almajiransa su yi idan ƙarshen bai zo a lokacin da suke zato ba? (Ka duba hoton da ke shafi na 14.)

10 ’Yan’uwa da yawa sun yi shekaru suna bauta wa Jehobah da aminci yayin da suke jiran ƙarshen ya zo. Amma kada mu yarda shigewar lokaci ta sa mu soma sanyin gwiwa kuma mu daina ganin cewa ƙarshen zai zo nan ba da daɗewa ba. Wajibi ne mu kasance a shirye don lokacin da Yesu zai zo ya halaka duniyar Shaiɗan. Ka tuna cewa Yesu ya ba wa mabiyansa shawara sa’ad da ya ce: “Ku yi lura, ku yi tsaro, ku yi addu’a: gama ba ku san lokacin da sa’a take ba. Kamar mutum da yake baƙunci a cikin wata ƙasa, ya rigaya ya rabu da gidansa, ya ba da iko ga bayinsa, ga kowanne kuma aikinsa, ya umurci sarkin ƙofa shi yi tsaro. Ku yi tsaro fa: gama ba ku san lokacin da ubangijin gida yana zuwa ba, ko da maraice, ko da tsakiyar dare, ko da carar zakara, ko da safe; kada ya iske ku kuna barci da zuwansa ba labari. Abin da ni ke ce maku, ina faɗa wa duka; Ku yi tsaro.”—Mar. 13:33-37.

11 Sa’ad da mabiyan Yesu suka san cewa ya soma sarauta a shekara ta 1914, sai suka kasance a shirye don sun san cewa ƙarshe zai iya zuwa ba zato ba tsammani. Sun yi hakan ta ƙara ƙwazo a yin wa’azin bishara ta Mulki. Yesu ya nuna cewa zai iya zuwa “ko da carar zakara, ko da safe.” Idan hakan ya faru, mene ne ya wajaba mabiyansa su yi? Ya ce su ci-gaba da ‘yin tsaro.’ Saboda haka, ko da mun daɗe muna jira, kada mu ɗauka cewa ƙarshen ba zai zo a zamaninmu ba.

12. Mene ne Habakkuk ya tambayi Jehobah, kuma wace amsa ce Allah ya ba shi?

12 Ka yi la’akari da annabi Habakkuk da aka ba shi umurni ya yi annabci cewa za a halaka Urushalima. Kafin a haife shi, wasu annabawa sun riga sun yi shela game da halakar. Yanayin ya kai wanda “miyagu sun kewaye masu-adalci” kuma “hukunci ya kan fita a karkace.” Saboda haka, ba abin mamaki ba ne cewa Habakkuk ya yi wannan tambayar: “Ya Ubangiji, har yaushe zan yi kira.” Jehobah bai ba wa amintaccen annabin amsa kai tsaye ba, a maimakon haka, ya tabbatar masa cewa halakar da aka annabta za ta faru, “ba za ta yi jinkiri ba.” Allah ya gaya wa Habakkuk ya “dakata mata,” wato ya ci-gaba da jira.—Karanta Habakkuk 1:1-4; 2:3.

13. Wane irin tunani ne Habakkuk zai iya yi, kuma me ya sa hakan yake da haɗari?

13 Da a ce Habakkuk ya yi sanyin gwiwa kuma ya yi tunani cewa: ‘Na yi shekaru da yawa ina jin labari cewa za a halaka Urushalima. Ai da sauran lokaci sosai. Bai kamata in riƙa annabci kamar za a halaka birnin nan ba da daɗewa ba. Zan bar wa wasu aikin su yi.’ Da a ce Habakkuk ya yi irin wannan tunanin da ya rasa dangantakarsa da Jehobah kuma wataƙila da ya rasa ransa sa’ad da Babiloniyawa suka halaka Urushalima!

14. Me ya sa ya kamata mu gode wa Jehobah saboda gargaɗin da ya ba mu game da jiran ƙarshen wannan zamani?

14 A sabuwar duniya, za mu tuna da yadda duk abubuwan da aka annabta game da ƙarshen wannan zamani suka faru. Za mu yi bimbini a kan annabcin da suka cika kuma hakan zai ƙara sa mu kasance da aminci ga Jehobah da kuma sauran abubuwan da ya yi alkawarinsu. (Karanta Joshua 23:14.) Babu shakka, za mu gode wa Allah don ya sa “lokatai da zamanai . . . cikin ikonsa,” kuma ya shawarce mu mu yi rayuwar da ke nuna cewa “matuƙar dukan abu ta kusa.”—A. M. 1:7, Littafi Mai Tsarki; 1 Bit. 4:7.

MU CI-GABA DA YIN WA’AZI YAYIN DA MUKE JIRA!

Kana yin wa’azin bishara da himma kuwa? (Ka duba sakin layi na 15)

15, 16. Me ya sa ya dace mu mai da hankali ga yin wa’azi a wannan kwanaki na ƙarshe?

15 Mun tabbata cewa ƙungiyar Jehobah za ta ci-gaba da faɗakar da mu mu ci-gaba da bauta wa Jehobah da sanin cewa ƙarshen ya kusa. Ana tanadar da wannan faɗakarwar don mu kasance da ƙwazo a hidimarmu ga Allah kuma mu san cewa annabcin da aka yi game da lokacin da Yesu ya soma sarauta suna cika. Wane mataki ne ya kamata mu ɗauka yanzu? Mu ci-gaba da biɗan Mulkin Allah da kuma adalcinsa ta wajen yin wa’azi da himma!—Mat. 6:33; Mar. 13:10.

16 Wata ’yar’uwa ta ce: “Idan muna wa’azin bisharar Mulkin Allah, za mu . . . iya taimaka wa mutane su tsira daga bala’in da ke nan tafe da zai shafi dukan duniya.” Ta san muhimmancin taimaka wa mutane su tsira don ita da mijinta sun tsira daga wani babban bala’i da ya faru da wani jirgin ruwa ta shaƙatawa mai suna Wilhelm Gustloff a shekara ta 1945. Ko a irin wannan yanayin, mutum zai iya yin ɓatan basira kuma ya ƙi saka abin da ya fi muhimmanci kan gaba. ’Yar’uwar ta tuna da wata mata da ke kuka tana cewa: “Akwatunana! Akwatunana! Gwalagwalaina! Duka gwalagwalaina suna cikin jirgin. Na yi asarar kome da kome!” Amma kuma wasu fasinjojin jirgin sun ba da kansu, suna aiki da ƙwazo don su ceci mutanen da suka faɗa a cikin ruwan tekun mai sanyin tsiya. Kamar waɗannan fasinjoji da suka ba da kai, ya kamata mu yi iya ƙoƙarinmu don mu taimaka wa mutane. Da yake mu san cewa lokaci yana ƙurewa, ya kamata mu mai da hankali ga yin wa’azi don mu taimaka wa mutane su tsira daga bala’in da ke tafe da zai shafi dukan duniya.

Shin kana ɗaukan matakan da suka dace don kada wani abu ya hana ka yin wa’azi da himma? (Ka duba sakin layi na 17)

17. Me ya sa ya kamata mu gaskata cewa ƙarshen duniya zai zo ba zato ba tsammani?

17 Abubuwan da suke faruwa a duniya sun nuna dalla-dalla cewa annabcin Littafi Mai Tsarki suna cika kuma ƙarshen zai zo ba da daɗewa ba. Saboda haka, kada mu ɗauka cewa za a jima kafin yanayin duniya ya kai lokacin da “ƙahonni goman” da kuma “dabban” da aka ambata a Ru’ya ta Yohanna 17:16, za su kai hari wa Babila Babba, wato dukan addinan ƙarya. Za su ɗauki wannan matakin ba tare da ɓata lokaci ba kuma ba zato ba tsammani don Allah ne zai sa tunanin ya shiga “cikin zuciyarsu”! (R. Yoh. 17:17) Ƙarshen wannan zamanin zai zo nan ba da daɗewa ba. Saboda haka, ya kamata mu bi umurnin Yesu da ya ce: ‘Amma ku yi hankali da kanku, kada ya zama zukatanku su yi nauyi da zarin ci da maye da shagulgula na wannan rai, har ranan nan ta hume ku, ba labari, kamar tarko.’ (Luk. 21:34, 35; R. Yoh. 16:15) Bari mu ƙuduri niyyar bauta wa Jehobah da sanin cewa ƙarshen zai zo nan ba da daɗewa ba kuma mu kasance da tabbaci cewa shi mai “aikawa sabili da mutum wanda yake sauraro gare shi” ne.—Isha. 64:4.

18. Wace tambaya ce za mu tattauna a talifi na gaba?

18 Yayin da muke jiran ƙarshen wannan zamanin ya zo, bari mu bi shawarar da almajiri Yahuda ya bayar ta ja-gorar ruhu mai tsarki sa’ad da ya ce: “Ya ku ƙaunatattuna, ku riƙa inganta kanku ga bangaskiyarku mafi tsarki, kuna addu’a da ikon Ruhu Mai Tsarki. Ku tsaya a kan ƙaunar da Allah ke yi mana, kuna sauraron jinƙan Ubangijinmu Yesu Almasihu mai kaiwa ga rai madawwami.” (Yahu. 20, 21, LMT) Amma, ta yaya za mu nuna cewa muna zaman jiran sabuwar duniyar da Allah ya yi alkawarinta kuma muna sa rai cewa zai zo? Abin da za mu tattauna a talifi na gaba ke nan.