ABIN DA KE SHAFIN FARKO | SHIN YA DACE KA YI NAZARIN LITTAFI MAI TSARKI?
Shin Ya Dace Ka Yi Nazarin Littafi Mai Tsarki?
-
Me ya sa aka halicce mu?
-
Me ya sa mutane suke shan wahala kuma suke mutuwa?
-
Mene ne zai faru a nan gaba?
-
Allah ya damu da ni kuwa?
Shin ka taɓa yi wa kanka irin waɗannan tambayoyin? Idan haka ne, to ka san cewa akwai ɗimbin mutane a faɗin duniya da suke yin tambayoyin nan. Mutane a duk faɗin duniya suna neman amsoshi ga muhimman tambayoyi a rayuwa. Shin za ka iya samun amsoshin?
Miliyoyin mutane za su ce, “Ƙwarai kuwa!” Me ya sa? Domin sun riga sun sami amsoshi masu gamsarwa a Littafi Mai Tsarki. Za ka so ka san abin da Littafi Mai Tsarki ya ce? Idan haka ne, za ka amfana da nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidun Jehobah suke yi da mutane. *
Idan ya zo ga binciken Littafi Mai Tsarki, wasu suna cewa: “Ba ni da lokaci.” “Ya yi wuya ainun.” “Ba na son abin da zai takura min.” Amma wasu suna farin cikin koyan abin da ke cikin Littafi Mai Tsarki. Ga wasu misalai:
-
“Na je cocin Katolika da na Furotestan da haikalin Sikh. Na zauna a gidan shugabannin addinin Buddha kuma na karanta ilimin addini a jami’a. Duk da haka, ban sami amsoshi ga tambayoyin da nake yi game da Allah ba. Wata rana, Shaidun Jehobah suka ziyarce ni. Amsoshin da suka ba ni sun burge ni sosai, sai na amince su yi nazarin Littafi Mai Tsarki da ni.”—Gill, Ƙasar Ingila.
-
“Na yi tambayoyi da yawa game da rayuwa, amma fastonmu ya kasa ba ni amsoshi masu gamsarwa. Sai wani Mashaidin Jehobah ya nuna mini amsoshin dukan tambayoyina a Littafi Mai Tsarki. Sa’ad da ya tambaye ni ko ina bukatar ƙarin bayani, na amince da hakan.”—Koffi, Ƙasar Bini.
-
“Na so in san yanayin matattu. Na yi imani cewa matattu za su iya yi wa rayayyu lahani, amma na so in san abin da Littafi Mai Tsarki ya ce. Hakan ya sa na soma nazarin Littafi Mai Tsarki da wani abokina wanda shi Mashadin Jehobah ne.”—José, Ƙasar Brazil.
-
“Na karanta Littafi Mai Tsarki, amma ban gane ba. Sai Shaidun Jehobah suka ziyarce ni kuma suka yi mini bayani a kan annabci da yawa a cikin Littafi Mai Tsarki. Na so in sami ƙarin ilimi daga wurinsu.”—Dennize, Ƙasar Meziko.
-
“Na yi ta tunani ko Allah ya damu da ni da gaske. Sai na yi addu’a ga Allahn da aka ambata a cikin Littafi Mai Tsarki. Washegari, sai Shaidun Jehobah suka zo gidana, kuma na amince su yi nazarin Littafi Mai Tsarki da ni.”—Anju, Ƙasar Nepal.
Waɗannan misalan sun tuna mana abin da Yesu ya faɗa cewa: “Masu farin ciki ne waɗanda suka san cewa suna bukatar ƙulla dangantaka da Allah.” (Matta 5:3, New World Translation) An halicci ’yan Adam da sha’awar ƙulla dangantaka da Allah. Allah ne kaɗai zai iya biya musu wannan bukatar kuma yana yin amfani da Littafi Mai Tsarki don yin hakan.
Mene ne nazarin Littafi Mai Tsarki ya ƙunsa? Ta yaya zai iya amfanar ka? Za a amsa waɗannan tambayoyin a talifi na gaba.
^ sakin layi na 8 Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Jehobah shi ne sunan Allah.