Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

KA YI KOYI DA BANGASKIYARSU | ANUHU

“Ya Faranta wa Allah Rai”

“Ya Faranta wa Allah Rai”

ANUHU ya kwan biyu sosai. Tsawon rayuwarsa ya kai shekara 365 kuma hakan yana da wuyan fahimta. A yau, mutane suna yawan rayuwa shekara 70 ko 80. Saboda haka, idan an haɗa shekarun mutane huɗu a zamaninmu, na Anuhu ya fi nasu! Amma a zamaninsa, shi ba tsoho ba ne sosai. A zamanin dā, fiye da ƙarnuka 50 da suka shige, mutane suna yin rayuwa na dogon lokaci fiye da mu a yau. Mutum na farko, wato Adamu ya yi shekara ɗari shida kafin a haifi Anuhu kuma ya ƙara yin shekara ɗari uku a duniya bayan hakan! Wasu ‘ya’yan Adamu ma sun yi rayuwa fiye da hakan. Don haka, wataƙila Anuhu yana da sauran ƙarfinsa sa’ad da ya kai shekara 365, kuma yana ɗokin zai ci gaba da rayuwa na dogon lokaci kafin ya mutu. Amma ba abin da ya faru ba ke nan.

Anuhu yana cikin haɗari sosai. Ka yi tunaninsa yana gudu kuma yana tunanin abin da mutanen da ya yi wa wa’azi za su yi masa. Fuskokinsu sun nuna cewa suna fushi sosai. Waɗannan mutanen sun tsane shi. Ba sa son saƙon da yake gaya musu kuma sun tsani Allahn da ya turo shi. Tun da ba za su iya kai wa Allahn Anuhu hari ba, sai suka kai wa Anuhu hari don su kashe shi! Wataƙila Anuhu ya yi tunanin ko zai sake ganin iyalinsa kuma. Shin ya tuna da matarsa da ‘ya’yansa mata ko ɗansa Methuselah ko kuma jikansa Lamek? (Farawa 5:21-23, 25) Shin ƙarshensa ke nan?

Labarin Anuhu a cikin Littafi Mai Tsarki yana da ɗan wuyan fahimta. Littattafai guda uku na Littafi Mai Tsarki ne kawai suka yi magana game da shi. (Farawa 5:21-24; Ibraniyawa 11:5; Yahuda 14, 15) Amma sun bayyana irin bangaskiyar da Anuhu ya kasance da shi. Shin kai mai iyali ne? Yin abin da ya dace yana maka wuya ne? Idan haka ne, za ka iya koyan darussa da dama daga bangaskiyar Anuhu.

ANUHU “YA RIƘA TAFIYA TARE DA ALLAH”

A lokacin da aka haifi Anuhu, ‘yan Adam suna yin abin da bai dace ba. Anuhu ya rayu a tsara ta bakwai daga zamanin Adamu. Kuma bai jima sosai ba da Adamu da Hauwa’u suka yi zunubi. Shi ya sa mutane ba sa saurin mutuwa a lokacin. Duk da haka, ɗabi’ar mutanen da kuma dangatakarsu da Allah sun taɓarɓare. Mugunta ta cika ko’ina. Wannan halin ya soma ne a tsara ta biyu, sa’ad da Kayinu ya kashe ƙanensa Habila. Akwai wani dangin Kayinu da yake alfahari sosai cewa ya fi Kayinu mugunta. A tsara ta uku kuma, sai mutane suka soma wani irin mugun abu. Suka soma kiran sunan Jehobah, ba don su bauta masa ba. Amma suna yin saɓo da suna mai tsarki na Allah.Farawa 4:8, 23-26.

Irin wannan muguntar ta zama ruwan dare gama gari a zamanin Anuhu. Yayin da Anuhu yake girma, sai ya tsinci kansa a cikin tsaka mai wuya. Shin zai bi halin mutanen da ke zamaninsa? Ko zai biɗi Allah na gaskiya Jehobah, mahaliccin sama da ƙasa? Babu shakka, labarin Habila wanda aka kashe shi saboda amincinsa ga Jehobah ya ratsa zuciyarsa. Anuhu ya yanke shawarar bauta wa Jehobah. Farawa 5:22 ta ce: Anuhu “ya riƙa tafiya tare da Allah.” Wannan furucin ya nuna cewa Anuhu ya kasance da aminci a duniyar da ke cike da munanan abubuwa. Shi ne mutum na farko da Littafi Mai Tsarki ya kwatanta haka.

Ayar ta kuma ce Anuhu ya riƙa tafiya tare da Jehobah bayan da ya haifi Methuselah. Hakan ya nuna cewa shi magidanci ne sa’ad da yake wajen shekara 65. Yana da aure amma Littafi Mai Tsarki bai ambata sunan matarsa ba. Ƙari ga haka, Nassi bai ambata adadin yaran da ya haifa ba, ya dai ce “ya haifi ‘ya’ya maza da mata.” Magidancin da ke tafiya da Allah yayin da yake kula da kuma yi wa iyalinsa tanadi yana bukatar ya koya musu ƙa’idodin Allah. Anuhu ya san cewa Jehobah ba ya so ya ci amanar matarsa. (Farawa 2:24) Ya yi ƙoƙari sosai don ya koya wa yaransa tafarkun Jehobah. Wane sakamako ne ya samu?

Littafi Mai Tsarki ya ba da ‘yan bayanai kawai game da wannan batun. Ya ce Methuselah, ɗan Anuhu ne ya fi kowa yawan shekaru a duniyar nan kuma ya mutu a shekarar da aka yi ambaliyar ruwa a zamanin Nuhu. Amma bai faɗi kome game da bangaskiyarsa ba. Bayan haka, Methuselah ya haifi ɗa mai suna Lamek. Lamek ya rayu fiye da shekara ɗari kafin kakansa Anuhu ya rasu. Lamek yana da bangaskiya sosai. Jehobah ya hure shi ya yi annabci game da ɗansa Nuhu, kuma annabcin ya cika bayan babbar ambaliyar ruwa na zamaninsa. Nuhu ya yi tafiya da Allah kamar kakan-kakanninsa Anuhu. Anuhu ya mutu kafin a haifi Nuhu. Amma Anuhu ya kafa masa misali mai kyau. Wataƙila, Nuhu ya koyi waɗannan abubuwan daga wurin mahaifinsa, Lamek ko daga wurin kakansa Methuselah ko daga wurin Jared, mahaifin Anuhu wanda ya mutu sa’ad da Nuhu yake ɗan shekara 366.Farawa 5:25-29; 6:9; 9:1.

Ka yi tunani a kan bambancin da ke tsakanin Anuhu da Adamu. Ko da yake Adamu kamili ne, ya karya dokar Jehobah kuma ya kafa wa ‘ya’yansa misali marar kyau. Amma ko da yake Anuhu ajizi ne, ya yi tafiya da Allah kuma ya kafa wa ‘ya’yansa misali mai kyau na bangaskiya. Adamu ya mutu sa’ad da Anuhu yake ɗan shekara 308. Shin iyalin Adamu sun yi makokin kakansu mai son kai? Ba mu da labari. Amma mun san cewa Anuhu ya ci gaba da “tafiya tare da Allah.”Farawa 5:24.

Idan kana yi wa iyalinka tanadi, to, ka yi la’akari da darasin da za ka iya koya daga bangaskiyar Anuhu. Ko da yake muna bukatar mu tanadar wa iyalinmu da abin biyan bukata, amma abu mafi muhimmanci shi ne mu taimaka musu su kasance da dangantaka mai kyau da Jehobah. (1 Timotawus 5:8) Za mu iya yin hakan ta ayyukanmu ba furucinmu kaɗai ba. Za ka kafa wa iyalinka misali mai kyau idan ka yanke shawarar yin tafiya da Allah yadda Anuhu ya yi, ta wajen barin Kalmar Allah ta yi maka ja-gora.

ANUHU YA “YI ANNABCI A KAN” SU

A wannan lokacin da mutane ba sa ƙaunar Allah, Anuhu ne kaɗai mutum mai bangaskiya. Amma shin Allahnsa Jehobah ya lura da bangaskiyarsa? Ƙwarai kuwa. Wata rana, Jehobah ya yi magana da bawansa. Ya ce ya idar da saƙo ga mutane. Ta hakan, Anuhu ya zama annabin da saƙonsa ya fara bayyana cikin Littafi Mai Tsarki. Mun san da hakan domin Yahuda, ɗan’uwan Yesu ya rubuta annabcin Anuhu bayan ƙarnuka da yawa. *

Wane annabci ne Anuhu ya yi? Annabcin ya ce: “Ku duba, ga Ubangiji ya zo da rundunan tsarkakansa, garin ya hukunta shari’a bisa dukan mutane, domin ya kāda dukan masu-fajirci kuma a kan dukan ayyukansu na fajirci da suka yi cikin fajircinsu, da dukan maganganu na ɓatanci waɗanda masu-zunubi masu-fajirci suka ambace shi da su.” (Yahuda 14, 15) Abu na farko da za ku lura a ayar shi ne cewa Anuhu ya yi annabcin kamar ya riga ya faru. Annabci da yawa da aka yi bayan zamanin Anuhu sun bi wannan salon rubutu. Dalilin shi ne: Annabin ya yi amfani da wannan salon rubutun domin ya kasance da tabbaci sosai cewa annabcin zai cika ko da yake bai faru ba tukun.Ishaya 46:10.

Anuhu ya gargaɗi miyagun mutane da gaba gaɗi

Shin ya kasance wa Anuhu da sauƙi ya idar da wannan saƙon, wataƙila ta wajen yi wa dukan mutanen wa’azi? Ka lura cewa saƙon ba albishiri ba ne. Anuhu ya yi amfani da furucin nan “fajirci” sau huɗu don ya tsawata wa mutanen da ayyukansu da kuma yadda suke tafiyar da rayuwarsu. Annabcin ya gargaɗi dukan ‘yan Adam cewa ayyukansu tun daga lokacin da aka fitar da Adamu da Hauwa’u daga lambun Adnin yana daɗa muni. Jehobah zai yi amfani da “rundunan tsarkakansa,” wato mala’ikunsa masu iko wajen kawo ƙarshen wannan mugun zamanin. Anuhu ya yaɗa wannan saƙon shi kaɗai kuma bai ji tsoron kowa ba. Wataƙila Lamek ya yi mamaki sosai don gaba gaɗin kakansa. Idan haka ne, to mun san dalilin haka.

Bangaskiyar Anuhu za ta iya sa mu tambayi kanmu ko muna ɗaukan wannan duniyar da muke ciki a yau yadda Allah yake ɗaukan ta. Saƙon hukuncin da Anuhu ya idar bai canja ba tukun. Ya shafe mu a yau yadda ya shafi mutane a zamanin Anuhu. Annabcin Anuhu ya cika sa’ad da Jehobah ya halaka miyagun mutane a zamanin Nuhu da babbar ambaliyar ruwa. Amma wannan halakar ta nuna cewa halakar da ta fi wannan tsanani tana nan tafe. (Matta 24:38, 39; 2 Bitrus 2:4-6) A yau ma, Jehobah yana a shirye da mala’ikunsa don ya halaka wannan duniya mai cike da fajirci. Dukanmu na bukatar mu yi la’akari da gargaɗin Anuhu kuma mu sanar da wasu. ‘Yan’uwanmu da abokanmu za su iya yin hamayya da mu. Kuma a wasu lokuta, za mu iya ji mun kaɗaita. Amma Jehobah bai yi watsi da Anuhu ba kuma ba zai taɓa manta da amintattun bayinsa a yau ba!

AN “ƊAUKI ANUHU DOMIN KADA YA GA MUTUWA”

Ta yaya Anuhu ya mutu? Yadda ya mutu ya fi salon rayuwarsa ban mamaki. Littafin Farawa ya ce: Anuhu “ya riƙa tafiya tare da Allah: ba a same shi ba; gama Allah ya ɗauke shi.” (Farawa 5:24) A wace hanya ce Allah ya ɗauki Anuhu? Manzo Bulus ya yi bayani: “Ta wurin bangaskiya aka ɗauki Anuhu (Enok) domin kada ya ga mutuwa; ba a kuwa same shi ba, gama Allah ya ɗauke shi: gama tun gaban ɗaukarsa aka shaida shi mai-game Allah ne sarai.” (Ibraniyawa 11:5) Mene ne Bulus yake nufi da furucin nan an ‘ɗauki Anuhu domin kada ya ga mutuwa’? Wasu juyin Littafi Mai Tsarki sun ce Allah ya ɗauki Anuhu zuwa sama. Amma hakan ba gaskiya ba ne. Me ya sa? Domin Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Yesu Kristi ne mutum na farko da ya tashi daga mutuwa zuwa sama.Yohanna 3:13.

A wace hanya ce aka “ɗauki” Anuhu domin kada ya “ga mutuwa”? Wataƙila Jehobah ya sa ya mutu domin kada maƙiyansa su kashe shi. Amma da farko, Anuhu ya “shaida shi” mai faranta ran Allah ne. A wace hanya ce ya shaida haka? Wataƙila Jehobah ya saukar masa da wahayi dab da mutuwarsa, don ya ga yadda duniya za ta kasance sa’ad da ta zama aljanna. Kafin Anuhu ya mutu, ya kasance da tabbaci cewa ya faranta wa Allah rai. Manzo Bulus ya yi wannan furucin game da Anuhu da wasu maza da mata masu aminci. Ya ce: “Dukan waɗannan suka mutu cikin bangaskiya.” (Ibraniyawa 11:13) Saboda haka, wataƙila maƙiyansa sun nemi gawarsa, amma ba su “same shi ba.” Mai yiwuwa, Jehobah ya binne shi da kansa don kada su wulaƙanta shi ko su yi amfani da shi wajen fifita bautar ƙarya. *

Bari mu yi amfani da waɗannan bayanan da Littafi Mai Tsarki ya yi wajen yin la’akari da yadda wataƙila Anuhu ya mutu. Ka yi tunani cewa abin da ya faru ke nan. Anuhu yana gudu kuma ya gaji sosai. Maƙiyansa suna nemansa don saƙon hukuncin da ya idar. Sai Anuhu ya nemi wani wuri ya ɗan ɓoye, amma ya san cewa wata rana, za su kama shi. Yana cikin tsaka mai wuya domin ana so a kashe shi. Ya yi addu’a ga Allah yayin da yake hutawa. Sai hankalinsa ya kwanta. Bayan haka, sai ya soma ganin wahayi kuma ya ji kamar abin na faruwa da gaske.

Wataƙila maƙiyan Anuhu suna dab da kashe shi sa’ad da Allah ya ɗauke shi

Ka yi tunanin cewa Anuhu ya ga duniyar da ta yi dabam da na zamaninsa. Ya ga cewa wurin yana da kyau kamar lambun Adnin, amma babu Kerub da ke tsaron lambun don kada mutane su shiga ciki. Mutane maza da mata masu ƙoshin lafiya da kuzari sun cika wurin kuma suna zaman lafiya. Babu ƙiyayya da kuma ‘yan hamayya da suke ko’ina a lokacin. Anuhu ya ga cewa Jehobah yana ƙaunarsa kuma ya amince da ayyukansa. Yana da tabbaci cewa zai zauna a irin wannan wurin. Yayin da Anuhu yake ganin wannan yanayi mai kyau, sai ya rufe idanunsa kuma ya daina numfashi.

Har yau, Anuhu yana cikin wannan yanayin amma Jehobah bai manta da shi ba. Bayan shekaru da yawa, Yesu ya yi alkawari cewa lokaci na zuwa sa’ad da dukan mutanen da ke kabari za su ji muryarsa kuma su tashi. Za su tashi daga mutuwa kuma su zauna cikin kyakkyawar duniya mai cike da salama.Yohanna 5:28, 29.

Za ka so ka kasance a aljanna? Ka yi tunanin yadda za ka ji sa’ad da ka haɗu da Anuhu. Ka kuma yi tunanin abubuwan da za ka koya daga wurinsa. Zai iya gaya mana cewa wannan bayanin da muka yi game da mutuwarsa gaskiya ne. Amma akwai wani abu da muke bukatar mu koya daga Anuhu da gaggawa. Bayan Bulus ya kammala batun Anuhu, sai ya ce: “In ba tare da bangaskiya ba, ba ya yiwuwa a faranta wa Allah rai.” (Ibraniyawa 11:6, Juyi Mai Fitar da Ma’ana) Babu shakka, muna da dalilai masu ɗimbin yawa na yin koyi da gaba gaɗi da kuma bangaskiyar Anuhu!

^ sakin layi na 14 Wasu marubuta sun ce Yahuda ya yi ƙaulin littafin afokirifa da ake kira Book of Enoch (Littafin Enok), amma wannan littafin ya faɗi abubuwa game da Anuhu da ba gaskiya ba ne. Ƙaulin annabcin Anuhu da aka yi a ciki gaskiya ce, amma da alama cewa an ɗauko shi ne daga wani littafi ko furuci na zamanin dā wanda ba a san inda yake a yau ba. Wataƙila Yahuda ya yi amfani da wannan littafin ko furucin, ko kuma ya sami labarin Anuhu daga wurin Yesu wanda ya shaida rayuwar Anuhu daga sama.

^ sakin layi na 20 Wataƙila dalilan da suka sa Allah ya ɓoye gawar Musa da na Yesu ke nan.Kubawar Shari’a 34:5, 6; Luka 24:3-6; Yahuda 9.