KU ZAUNA A SHIRYE!
Za a Daina Wariyar Launin Fata Ne?—Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce?
Mutane da yawa suna ganin ba za a taba daina wariyar launin fata ba.
António Guterres wanda shi ne Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya ya ce: “A fadin duniya, nuna wariyar launin fata yana jawo matsaloli da yawa ga kungiyoyi da dama da kuma harkokin rayuwar mutane. Kuma hakan yana sa mutane su rika wulakanta juna.”
Shin za a daina wariyar launin fata ne? Mene ne Littafi Mai Tsarki ya ce?
Raꞌayin Allah game da wariyar launin fata
Littafi Mai Tsarki ya nuna mana yadda Allah yake ganin mutane daga wurare dabam-dabam.
“[Allah] ya halicci dukan alꞌumma daga mutum guda, domin su zauna a dukan fuskar duniya.”—Ayyukan Manzanni 17:26.
“Allah ba ya nuna bambanci, amma yana karbar duk mai tsoronsa da kuma mai aikata adalci a kowace alꞌumma.”—Ayyukan Manzanni 10:34, 35.
Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa dukan ꞌyan Adam sun fito daga wurin daya kuma Allah yana amince da mutane ko da mene ne launin fatarsu.
Yadda za a daina wariyar launin fata
A Mulkin Allah ne za a daina wariyar launin fata. A mulkin ne za a koya wa mutane yadda ya dace su rika shaꞌani da juna. Mutane za su koyi yadda za su daina nuna wariyar launin fata.
“Mazaunan duniya za su koyi yin adalci.”—Ishaya 26:9.
“Amfanin yin abin da yake daidai, shi ne salama. Abin da yin adalci zai haifar, shi ne natsuwa da hutawa har abada.”—Ishaya 32:17.
A yau, miliyoyin mutane suna koya daga Littafi Mai Tsarki yadda za su rika daraja da girmama mutane.
Don karin bayani, ka karanta mujallar Awake! mai jigo “Is There a Cure for Prejudice?”
Ka karanta talifin nan “Talking to Children About Racism” don ka ga yadda iyaye za su iya tattauna wannan batun a gida.