Takawa a kan Gadon Teku don Wa’azi
Mutane wajen 300 ne suke zama a kananan tsibirai da ake kira Halligen, a Tekun Arewa da ke kusa da yammacin gabar Schleswig-Holstein. Yaya mutanen nan suke jin wa’azin bishara da Shaidun Jehobah suke yi?—Matta 24:14.
Shaidun Jehobah sukan shiga kwalekwale zuwa wasu tsibiran. Amma wasu tsibiran kuma sai sun taka wajen nisan kilomita 5 a kan gadon teku kafin su isa. Ta yaya hakan yake yiwuwa?
Yin Amfani da Canjin Yanayin Teku
Kowane awa shida, zurfin ruwan Tekun Arewa da ke yankin tsibiran Halligen yakan ragu da wajen kafa 10! A duk lokacin da ruwan tekun ya ja da baya haka, ana ganin gadon tekun kuma hakan yana ba wa Shaidun Jehobah damar takawa da kafa zuwa tsibirai guda uku.
Yaya tafiyar take? Ulrich, wani shahararren mai ja-gora a tekun ya ce: “Yakan dauke mu awa biyu kafin mu kai dayan tsibirin kuma yawancin lokuta muna takawa babu takalma. Wannan ita ce hanya mai kyau na yin tafiya a gadon teku. Amma idan ana sanyi, sai mu saka takalman ruwa.”
Yanayin yana da ban tsoro. Ulrich ya ce: “Za ka ji kamar kana wata duniya ne dabam. Wasu wurare a gadon tekun suna da laka sosai, wasu sun cika da duwatsu sa’an nan wasu kuma da ciyayin teku. Za ka ga dimbin tsuntsayen teku da kaguwowi da dai sauran dabbobi.” A wasu lokuta, masu tafiyar sukan tsallake kananan ruwaye da ake kira Priele da Jamusanci.
Wadanda suke wannan tafiyar sukan fuskanci kalubale da dama. Ulrich ya ce: “Za ka iya batawa a tekun musamman idan ana hazo. Saboda haka, muna amfani da kamfas da na’urar GPS, kuma muna gwada daidai lokacin da ruwan tekun ya ja da baya domin kada ya dawo ya same mu bayan awa shida.”
Me ya sa ake wannan yunkurin? Ulrich ya ba da labarin wani mutum mai shekaru 90 da wani abu da yake yawan karanta mujallun Hasumiyar Tsaro da Awake! Ya ce: “Akwai ranar da lokaci ya kure mana kuma ba mu sami damar zuwa wurin mutumin ba. Amma kafin mu bar tsibirin sai mutumin ya bi mu a guje a kan keke kuma da ya same mu sai ya ce mana: ‘Wai yau ba za ku ba ni Hasumiyar Tsaro ba?’ Hakika da farin ciki muka ba shi Hasumiyar Tsaro.”