Me Zan Yi Don In Zama Mashaidin Jehobah?
Yesu ya ambata matakan da ya kamata mutum ya dauka don ya zama Mashaidin Jehobah a cikin Matta 28:19, 20. A wurin an nuna abin da mutum zai yi don ya zama almajirin Yesu, wato, a gaya wa mutane game da Jehobah.
Mataki na 1: Ka koya abin da ke cikin Littafi Mai Tsarki. Yesu ya gaya wa mabiyansa su ‘almajirtar . . . , suna koya musu.’ (Matta 28:19, 20) Kalmar nan da aka fassara ta zuwa “almajiri” tana nufin “dalibi.” Littafi Mai Tsarki yana dauke da koyarwar Yesu Kristi akan abubuwan da kake bukatar ka sani don ka sami farin ciki a rayuwa. (2 Timotawus 3:16, 17) Za mu yi farin cikin nuna maka abin da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa ta wurin nazarin Littafi Mai Tsarki da muke yi da mutane kyauta.—Matta 10:7, 8; 1 Tasalonikawa 2:13.
Mataki na 2: Ka yi amfani da abin da kake koyo. Yesu ya ce dole ne wadanda suke koyo su “kiyaye dukan iyakar abin da na umurce” su. (Matta 28:20) Hakan yana nufin cewa nazarin Littafi Mai Tsarki da kake yi ba don ka yi ilimi ne kawai ba, amma don ka kyautata tunaninka da kuma halayenka ne. (Ayyukan Manzanni 10:42; Afisawa 4:22-29; Ibraniyawa 10:24, 25) Wadanda suke bin umurnan Yesu, za su so su yanke shawarar ba da kansu ga Jehobah.—Matta 16:24.
Mataki na 3: Ka yi baftisma. (Matta 28:19) A cikin Littafi Mai Tsarki an kwatanta baftisma a matsayin binne mutum. (Gwada Romawa 6:2-4.) Yana kamar a ce mutum ya dena irin rayuwar da yake yi a dā kuma ya soma sabuwar salon rayuwa. Saboda haka, idan ka yi baftisma, ka nuna ke nan a fili cewa ka riga ka dauki matakai biyu na baya da muka tattauna wadanda Yesu ya fada kuma kana bidan lamiri mai kyau daga wurin Allah.—Ibraniyawa 9:14; 1 Bitrus 3:21.
Ta yaya zan san na kai a yi mini baftisma?
Ka gaya wa dattawa cikin ikilisiya. Su za su taimaka maka ka gane abin da hakan ya kunsa, wato, ko kana aiki da abin da ka koya, kuma, ko ka riga ka ba da kanka don ka yi nufin Allah.—Ayyukan Manzanni 20:28; 1 Bitrus 5:1-3.
Shin wadannan matakan sun shafi yaran Shaidu kuwa?
E. Kamar yadda Littafi Mai Tsarki ya fada, muna yi wa yaranmu “horon Ubangiji da gargaɗinsa.” (Afisawa 6:4) Amma sa’ad da suke girma, kafin a yi musu baftisma, sai sun koya kuma sun nuna a halayensu cewa sun amince da abin da suka koya daga Littafi Mai Tsarki. (Romawa 12:2) A takaice dai, kowanne mutum zai yi nasa zabi game da batun ibadarsa ga Allah.—Romawa 14:12; Galatiyawa 6:5.