Koma ka ga abin da ke ciki

“Mu Riƙa Yaɗa Bishara!”

Taron Yanki na Shaidun Jehobah na 2024

Kyauta Ake Shiga Ba a yawo da tire don karɓan kuɗi

Wasu Abubuwan da Za A Gudanar

Jummaꞌa: Za ka ga abin da ya nuna cewa labarin rayuwar Yesu da ke Linjila abu ne da ya faru da gaske. Za ka kuma ga yadda labarin nan daga Littafi Mai Tsarki zai amfane mu a yau.

Asabar: Waɗanne annabce-annabce ne aka yi game da haihuwar Yesu da kuma rayuwarsa, kuma annabce-annabcen sun cika kuwa? Za ka ji amsar.

Lahadi: A jawabi daga Littafi Mai Tsarki mai jigo, “Me Ya Sa Ba Ma Tsoron Munanan Labarai?” Za ka ga dalilin da ya sa miliyoyin mutane suke kasancewa da kwanciyar hankali da kuma bangaskiya duk da cewa yanayoyin rayuwa na daɗa muni.

Wasan Kwaikwayo

Labarin Hidimar Yesu: Sashe na 1

Hasken Gaske a Duniya

A cikin abubuwan ban alꞌajibi da suka faru lokacin da Yesu yana ƙarami, haihuwarsa ne abu ne farko da ya ba wa mutane mamaki. Iyayensa sun kai shi Masar don su kāre shi daga hannun sarki da ke so ya kashe shi. Daga baya, ya ba ma wasu manyan malamai mamaki sosai. Ka kalli yadda waɗannan da wasu abubuwa suka faru a bidiyo mai sassa biyu da za a nuna ranar Jummaꞌa da Asabar.

Ka kalli waɗannan bidiyoyi game da taron yanki na wannan shekarar

Me Ake Yi a Taron Yankinmu?

Kalli wannan bidiyon don ka ga abin da ake yi a taron yanki na Shaidun Jehobah.

Taron Yanki na Shaidun Jehobah na 2024: Mu Riƙa Yaɗa Bishara!

Ka ga abin da za mu koya a taron yanki na shekarar nan.

Soma Taɓin Wasan Kwaikwayo: Labarin Hidimar Yesu

Mutane da yawa sun san game da labarin haihuwar Yesu. Amma mene ne ya faru kafin a haifi Yesu da kuma bayan da aka haife shi?